page 2

212 12 3
                                    

*YANCI DA RAYUWA*

     ©®Hafsat Rano

   Page 2

*****Tun kafin ayi kiran farko ta tashi saboda tarin ayyukan da suke jiran ta a kitchen din gidan, a yanzu itace trusted cook da Hajiya ta amince da ita shiyasa abubuwan suka sake yi mata yawa gashi kusan kowa na gidan da abinda yake ci as breakfast, wanka ta fara yi dama tun kafin ta kwanta ta gyara dakin ta, ta fito da uniform dinta da school bag dinta ta ajiye su a gefen gado. Ana kiran farko ta fito zuwa kitchen din gidan domin ta fitar da komai ta gyara wanda zata gyara kafin a kira sallah, kasancewar aikin ya riga ya bi jikinta yasa take da mugun sauri, bata son abinda zai shiga lokacin karatun ta shiyasa ta tsara komai take yin sa da wurwuri ba tare da bata lokaci ba.
   Karfe bakwai da rabi ta fito cikin shigar uniform dinta, white hijab da light blue riga da wando, sai I'D card dinta da ta makale a wuyan ta. Ta gate din baya duk masu aikin gidan suke fita dan haka kanta tsaye ta nufi gate din bakin ta dauke da adduar fita daga gida. Ba kasafai ta fiya haduwa da mutane ba a lokacin sai masu fita training suma ta san hanyar da take bi ta guje ma haduwa dasu,  sannan da yanayi yadda unguwar take tsit ta manyan masu kudin kasar. Tafiya take a nutse kanta a kasa tana irga sauran subject din da suka rage mata. Bata ji tahowar sa ba, sai ji tayi mutum ya bangaje ta, a tsorace ta kalle shi, wani irin kallo yayi mata yayi saurin cewa

"I will call you back, naga wata fine babe." Be jira amsar sa ba ya danna airpod din ya katse wayar yana mata wani silent kallo. Ganin haka yasa tayi gaba zata wuce yayi saurin shan gabanta

"I'm so sorry please, ban ganki ba waya ta dauke min hankali."

"Ba komai."

Tace da sauri ganin haduwar shi bata taba zata zai tsaya bata hakuri, bata kuma so a samu wata matsala har labari ya koma. Gaba tayi da dan sauri tunawar da tayi 9:30 zasu shiga exams gashi tana yin tafiyar kusan awa daya kafin taje in da zata hau taxi dan taxi basa shigowa unguwar. Tsayawa yayi rataye da hannun sa a bayan sa yana kallon ta, ta cigaba da sauri kamar zata tashi sama. Zai iya rantsewa be taba ganin me kyawun ta ba, wani irin musulmin kyau me matukar daukar hankali da fusga, yana tsaye har ta bacewa ganin sa, ya sauke ajiyar zuciya, yasan idan har a area din take zasu sake haduwa, nan kusa kuwa dan a da yana dan yin wasa wajen fitowa gudu da safe amma daga ranar zai maida shi kullum. Sai ya sake murmushi ya juya yana sake kiran Rafeeq
   Yana zaune akan aikin da yake kiran Asim ya sake shigo masa, sai da ya ja siririn tsaki sannan ya daga

"Ina jinka?" Yace yana dan ture system din

"Sorry wallahi wata babe na gani, guy ka ganta kuwa?"

"Akan ta ka katse min waya?"

"Ba zaka gane ba, idan ban katse ba zata iya katse numfashi na."

"Mts! Baka da aikin yi, in dai yaran Abujan nan ne, zaka bata ma kanka lokaci ne kawai."

"Noo wannan daban ce."

"Kai ka sani."

"Allah kuwa."

"Naji, ina muka tsaya a maganar mu?"

"Yadda dai muka ce ne, idan ka dawo sai mu ga abinda za'a kara kai, but komai na office din ya kammala."

"Ok, karshen week din nan zan siya ticket in sha Allah, later bari na karasa wani aiki."

"Alright, sai munyi magana. " Suka ajiye wayar a tare. Sake matsawa yayi gaban system din ya dauki glasses dinsa ya saka ya cigaba da duba aikin.

   Direct toilet Asim ya wuce ya sakar ma kansa ruwa sannan ya fito da shirin fita office ya wuce dining area, a saman d-table ya tarar da Anisa tana shan tea da pancake tana danna wayar hannun ta. Kusa da ita ya zauna cook din dake tsaye daga gefe ya matso ya shiga serving dinsa shi kuma ya maida kallon sa kan Anisa da ta cigaaba da danna wayarta kamar bata ga sanda ya zauna ba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 12, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

YANCI DA RAYUWA Where stories live. Discover now