NESA KUSA
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, tsira da amincin Allah su tabbata a gare ka Annabin Rahama Annabi Muhammad (S A W)
بسم الله الر حمن الر حيم
GARGAƊI
Ban yarda wani/wata su juya min labari ba yin hakan kuskure ne a
kiyaye
____________________________________
Haidar Ali Mgnd
(Aliyu Dalhat Ismail )01
*******
2020PRISON
A yanayi irin wannan kaɗaici kawai take buƙata, hayaniyr da sauran mutanen dake ɗakin ke yi jin ta take har cikin zuciyar ta. Wata irin shewa ce ta kaure ɗakin da ta tilas ta mata kai duban ta ɓangaren da shewar ke tashi, murmushi ne kwance akan fuskokin su
"kamar babu wani abu dake damun su kamar jindaɗin gidan nan suke"
Ta faɗi a zuciyar ta, ita kam ta san ko maƙiyin ta bata taɓa mai fatan ya kasance ce a cikin wannan baƙin gidan ba
.
"To ke me kika yi ne?"Cewar wata ƴar siririyar mata
Jin tambayar da aka yima ɗaya daga cikin su ya sanya ta mai da hankalin ta garesu don jin amsar da za'a bayar
Wani murmushi tayi mai ciwo matar da aka tambaya tayi kafin ta ce
"Wallahi matsala ce ta bashi kin san...
" Mtswwww "
Wani dogon tsaki matar da tayi tambayar tayi kafin ta ɗora da
" Ai ke ki godewa Allah matsalar ki ba mai girma ba ce, cikin ƙanƙanin lokaci zaki fita to matsalar bashi a ko ina ana fama, ita kanta gwamnatin bashin da ke kanta sai dai ƴan baya su biya don baza ta iya ba. Yanzu abin da nake so dake, ki natsu ki kwantar da hankalin ki kinji, ki saki jikin ki, komai zai yi dai-dai".
Hirar su suke cikin kwanciyar hankali.
Daga inda take a zaune tsaf take jin duk Hirar da suke sai taji jikin ta yayi wani irin sanyi.
Wai bashi to me zai sa a kawo mai bashi gidan yari kamar wacce tayi sata ko ita da ta aikata babban laifi gani take kamar zaman ta a wajen bai dace ba kamar ba a yi mata adalci ba.
**COURT
Rubutu yayi sosai kafin ya ɗago da duban shi akan ta yana faɗn
"Bisa la'akari da hujjoji da shaidu da ita kanta mai laifin ta amsa laifin ta babu wata jayayya ko gardama kotu ta yanke mata hukuncin...
Bai kai ƙarshen maganar shi ba sakamakon wani irin kakari da take yi kamar zata zubar da ƴan cikin ta, amai ne yazo mata sosai bada wasa ba.
"Kotu ta bada damar a kai ta asibiti don a duba lafiyar taa karkashin kulawar jami'an tsaro zuwa ranar shida ga wannan watan".
ASIBITI
Zuwa yanzu taji ƙarfin jikin sakamakon ruwan da aka sanya mata da wasu allurori, sai dai ciwon jiki ne kawai ke damun ta sosai, tasan dole tai ciwon jiki musamman kwanciya a kasa abinda baza ta iya tuna yaushe ya faru ba a duk tsayin shekarun ta ga sauro ga wasu irin ƙwari da baza tace ga sunan su ba.
Tana daga kwance wata mata ta shigo da sallama ɗauke a bakin ta,
Amsawa tayi ciki-ciki don ba wani son Magana take ba a yanzu
Ruwan da aka sanya mata ta duba kafin ta ce
"Ki daina damun kanki don ba kya bukatar hakan, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce zai zama labari don...
Cikin razana da firgici ta juyo da duban ta kan matar, hannun ta na karkarwa bakin ta na rawa kamar na maroƙin dake shirin yin roƙo bai kai ga yiba yaga ana fallo nairori da kyar ta iya faɗin

YOU ARE READING
NESA KUSA
Mystery / Thriller"Haihuwar mu kaddarar ki ce son zama da mu zaɓin ki ne, ba sai kin yi hakan zamu fahimci me kika yi ba zamu karbi hakan a matsayin kaddarar da ta kanzo wa kowanne bawa ba tare da ta bashi zaɓi ba *** Ba tare da zato ko tsammani ba motar ƴan sanda ta...