AMANNA
NA
JAMILA UMAR TANKO
(JUT)
HAQQIN MALLAKA(M): JUT
COPYRIGT©: JUT
SHEKARAR BUGAWA:
2014
ISBN:
NA'URA MAI QWAQWALWA:
ZUT
SADAUKARWA:
Masoyan da suke soyayya saboda Allah
TUKUICI:
Suwaiba Mohd Lawan
FATAN ALKHAIRI:
'Yan uwana marubuta (Mace mutum writers Asociation)
GORO:
Goron sallah ga makaranta masoyana
FAXAKARWA:
Wannan labari qirqirarran labari ne, ba'ayi dan wani ko dan wata ba duk wanda labarin ya yi kama da nasa ko nata katari aka yi.
GARGAXI:
Ba'a yarda wani ko wata ya juyi wannan labari ba ta kowacce siga ba tare da izinin marubuciya ba. Yin haka zai jawo mummunan hukuncin daga hukuma.
RANAR LAHADI 1st GA WATAN 6 2014
Yanayi ne na damuna, gari yayi garai-garai an yi ruwan sama an xauke tamkar an saka soso da sabulu an wanke shi. La'asar sakali iska mai sanyi ke kaxawa. Ko ina ka juya koren ganye ne ke ta kaxawa iska ce daga Rabbil samawati take ta barbazuwa tana fifita jikin bi'adama. Tabbas yanayin nan ya bawa jam'ar dake zaune a babban birnin tarayya Abuja nishaxi da annashuwa a wannan yammacin.
Izziddin ya murtike fuskar babu annuri, alamar babu walwala a zuciyarsa, ya yi kicin-kicin da fuska, ya haxe girar sama data qasa. Alamun gajiya ta nuna ajikinsa da tufafinsa shaidar ya wahala matuqa saboda tsaleliyar shadda fara sol day a saka jikinsa ta yamutse, haka haskenta ya disashe, daga ganinsa ba sai ka tambaya ba ka san tun fitowar safe ce bai koma gida ba, banda karin kumallo babu abincin daya sake saduwa da 'yayan hanjinsa. Kallo xaya zaka yiwa cikinsa ka ga kamar ya kusa haxewa da doron bayansa.
Bayan Izzidin ya tababtar Lado almajiri ya fahimci abinda ya ke nema sai ya umarce shi da ya shiga gaban motarsa ya raka shi gidan, shigar Lado cikin motar ke da wuya sai Izziddin ya suri mota da gudu, ba jimawa sai gasu a bakin get xin wani gida, Lado na nuna masa hanya sai kawai ya saka kai cikin get xin gidan kasancewar babu mai gadi kuma get xin a wangale yake, bai dire a ko ina ba sai a bakin barandar mashigar gidan.
Lado ya nuna masa gidan da xan yatsa
"yauwa ga gidan Zahidah."
Izziddin ya tsinci kansa tamkar an jefa shi cikin aljanna, Shekaru goma sha biyu kenan yana jiran wannan rana, yau ce ranar da ya ji farin cikin da bai tava jin irinsa ba tunda aka haife shi. Yau ce ranar da ya ji dunqulelen baqin cikin da ya danqare a zuciyarsa na shekaru da shekaru ya dire qasa. Yau ne ya ji jijiyoyin zuciyarsa su na ta gudanar da jini yadda ya kamata. Yau ne ranar da ya yi murmushi mai nuna tsantsar farin cikinsa, murmushin da ya kan qara masa kyau da kamala.
Iziddin ya juyo a hankali ya dubi Lado cikin fuskar annuri "ka tabbata wannan gidan shine gidan da Zahidah take zaune? Ka tabbata ita xin ce da na nuna maka a hoto?"
Lado ya gyaxa kai ya ce "tabbas na santa, farin sani kuwa. Tana aike na ma kuma duk ranar juma'a anan muke zuwa karvar abincin sadaka, dan tana yin abinci ta raba mana."
Izziddin ya yi murmushi ya lumshe ido ya faxa a bayyane "Allahu akbar! Zahidah baiwar Allah. Ashe har yanzu tana nan da aikin Allah bata canja ba. Yaro ka tabbata bata da aure kada in faxa gidan mijinta fa?"
Lado ya girgiza kai ya ce "bata da aure duk unguwar nan kowa ya santa."
Izziddin ya maimaita "kowa ya santa?"
Lado ya gyaxa kai ya ce "tana da kyauta da fara'a."
Izziddin ya yi dariyar jin daxi ya saka hannu a aljihu ya zaro kuxi naira na dukan naira har naira dubu biyar ya bawa Lado, sai Lado ya ji tamkar ya bashi duniya kasancewar naira hamsin ma wahalar samu take yi masa, ya duqa ya karva ya yi ta godiya sannan ya buxe qofar mota ya fice, ya tsaya a gefe yana kallon Izziddin.
Sai da Izzidin ya xaga hannayensa sama ya kwararo addu'ar godiya ga Rabbil samawati da Ya nuna masa wannan rana kuma ya sake nanawa alqawarin nan na azumi guda goma wanda zai yiwa Allah, na tawasali in har ya gano in da Zahidah take.
Ya fito daga motar sannan ya rufe, ya sake yiwa Lado godiya shima yana yi masa, ya nufi qofar shiga gidan kai tsaye yana mai matuqar muradin ganin wannan fuska daya ke kewarta, yana nemanta afujajan amma ya kasa samunta sai a yau. Ya tsaya akan baranda ya qwanqwasa, ya sake qwanqwasawa fiye da sau biyar, ba'a buxe qofar ba sai ya murxa, cikin sa'a ashe qofar a buxe take. Kafin ya saka kai ya shiga sai da ya runtuma sallama sau uku shiru ba amsa. Sai ya fara tunanin yaron nan Lado ya yi masa sakiyar da babu ruwa, ya turo shi gidan da babu kowa. Ya juya da sauri ya dubi wajen motarsa inda ya bar Lado a tsaye sai ya ga wayam yaron ya arce, nan da nan ya ji gaba xaya ransa ya vaci.
Duk da haka bai fitar da ran ganin Zahidah ba a yau kuma ya qudiri a niyyar sai ya ga qwaqwaf, sai ya tabbatar ba gidan ba ne sannan zai haqura dan haka sai ya danna kai ya shiga falon.
Kash! Abin da idanuwansa suka gane masa hankalinsa ya yi mummunan tashi, ya razana matuqa, haka saura kaxan ya haxiyi zuciya ya mutu Allah Ya kiyaye. A tsaye ya shixe ya qame, dan ma musulmin kwarai baya mantawa da kalmar 'Innalillah wa inna ilaihi rajuun.' a duk lokacin da bala'i ya tunkaro shi. Ita ya fara ambata, ya faxa ya sake nanantawa har sau uku.
Yadda ya haxu da wannnan gigita da ximuwa haka mai gidan da aka shigo mata ta samu har ma fiye da nasa. Ta zabura ta miqe tsaye gami da yin wurgi da abinda yake hannunta, aka rasa wanda zai fara magana a tsakaninsu, kawai a tsatstsaye su ke carko-carko, kallon -kallo kawai ake yi, har zuwa wani lokaci mai tsawo. Ya ji qafarsa babu qarfi sai ya sulale ya zauna akan kujerar da take kusa da shi ya ci gaba da kallon falon gabas da yamma kudu da arewa.
Babu abinda kwayar idanuwansa take cin karo da shi sai kwalaben Benalyn, pakalyn, kwaya irin su tramol, baliyan da sauransu a bisa teburin da yake gabanta kwalabe sun kai goma da qulli-qullin kwayoyi daban-daban a cikin ledoji, dukka a cikinta take xurawa har ta sha rabi.
Wasu danqara -danqaran garada ne su biyu qosassu sun sha giya sun yi mankwas a kwance a tsakiyar falon a qasa. Ya saka hannu a hankali ya xaga wata kwalba a qasa ya karanta an rubuta STAR, tabbas giya ce waxannan bayin Allah suka xixxika suka yi mankwas, ba su ma san waye akan su ba barci suke yi mai kama da mutuwa.
Ya xaga kai a hankali ya dubi Zahidah wacce yake zumuxin gani, nemanta yake sama da shekaru goma sha biyu sai yau ya nemo ta, yana murna zai ganta sai ga shi ya ganta a halin da bai tava zato ba ko a mafarki, halin daya ganta ya sa murnar da yake ta juye takaici. Yana haxa ido da ita sai ta sunkuyar da kai qasa, shigar da tayi kaxai ta nuna masa shaidar ko ita wacece, riga shimi ce marar hannu sai gajeren wando iya guiwa, kanta kuwa gashin jelar doki ne aka kitsa mata (attachment), farcen hannaye da qafafuwa kuwa jan farce ne ta shafa, faratanta zaqo-zaqo.
Ya shiga tunanin yadda ake yin Sallah a haka, ko ma ta bar musulunci oho bai sani ba. Haka tulin kwalaben shaye-shayen dake kan teburi a gabanta, ya nuna kuma ya tabbatar masa 'yar maye ce.
Wa su tanfatsa-tanfatsan mata ne suke ta firfitowa daga cikin xakuna daban-daban kowaccensu kyakykyawa ce ta kwatance son kowa qin wanda ya rasa amma kuma kyan xan muciji, waxannan sun e matan da ake kira furen kan juji sai kyau ba hali, suka fito getse-getse shiga marar tsari tamkar tsirara suke abin ba kyan gani. Kowacce ta fito sai ta yi hamma tayi miqa sannan ta qura masa ido tana xaga masa gira, da alama sabon kostoma suke nema. Wa'iyazu billah!
Kyakykyawar fuskarsa, shigarsa ta kamala, kyawun suffarsa, qirar jikinsa gami da alamar hutu a jikinsa suka dasa musu kwaxayinsa a cikin zuqatansu, sai kowace ta fara kwarkwasa tana maqale murya. Su ka gaishe shi, bai amsa musu ba, ya yamutse fuska yana kallon kowaccensu a wulaqance dan shi tsantsaninsu yake.
Ya miqe tsaye a hankali ya dubi Zahidah cikin jimami da baqin ciki ya na magana daqyar muryarsa na karkarwa ya ce "Zahidah, kada dai abinda nake gani da idanuwana gaskiya ne, kada dai ace gidan dana shigo gidan karuwai ne kuma gidan giya ?"
Zahidah ta sunkuyar da kai qasa da sauri ta kasa haxa ido dashi balle ta bashi amsa saboda nauyi da kunyarsa da take tsananin ji, shine mutum na farko da take jin nauyi a duniya.
Qawayenta suka tsaya cak suna kallonta da Izziddin tamkar sun sami talabijin, suna ganin wani baqon hali a wajen qawarsu Zahidah dan su a iya saninsu da ita ba su tava ganin alamar kunya a tare da ita ba sai yau.
Zahidah ta juyo a fusace ta harari qawayenta gami da yi musu tsawa "dalla ku koma xaki kada wata ta qara fitowa."
Su ka amsa mata da "to shugaba."
Kowacce ta juya da sauri ta nufi xaki amma basu daina kwarkwasa ba suna ta karairaya, har suka shige.
Zahidah ta kawar da kai gefe ba tare da ta bashi amsa ba. Ya dade a tsaye yana kallonta sama da qasa, sai huci yake tamkar Kasa ko wani kumurcin maciji, sai zufa yake kai kace a ramin da babu iska ya shiga, kan hancinsa da goshinsa suna ta tsatstsafo da ruwa. Ya fice da sauri a fusace, ita kuma Zahidah ta sulale ta zauna akan tiyils ta dafe kai, hawaye mai zafi ya fara kwaranya.
Ya na xaga labule ya fice sai ya ga giftawar wani mutum ya shiga gidan ta qofar kicin, Iziddin ya kalli mutumin shi kuma mutumin kansa na sunkuye a qasa yana danna waya bai kalle shi ba har ya shige, Izziddin ya kalle shi sosai kallo na qurilla nan da nan ya shaida shi, ga fuskarsa nan muraran da kayan jikinsa. Tabbas ganin mutumin nan da ya yi ya shiga qasurgumin tashin hankali har fiye da tashin hankalin day a shiga xazu na ganin Zahidah.
Toh fa! Rigiji gafji!! Ya ji lavvan bakinsa sun kasa haxuwa da junansu balle ya karanto salati, ya saki baki ya xurqushe a qasa yana karkarwa. Dole ya shiga tashin hankali mana da fuskar amininsa ya yi arangama wato Khamis, dan duk duniya Izziddin bashi da amini kamar Khamis, haka shima Khamis xin. Garinsu xaya, a garin ma unguwarsu xaya, a unguwar ma makwabta ne ga gida ga gida. Bayan haka iyayensu qawaye ne tare suka yi 'yanmatanci, rana xaya aka haife su xaya da safe xaya da yamma. Tare suka yi wasa, rana xaya aka yi masu shayi. A yanzu haka bacci kaxai ke raba su, xazu da safe ma sun haxu kafin ya fito neman Zahidah, har ma ya faxa masa in da zai je ya yi masa addu'a Allah Ya sa a dace.
Abin tambaya anan shine daman abokinsa Khamis ya san in da Zahidah take amma shekara da shekaru yake taya shi nemanta bai tava nuna masa ya san in da take ba har ma suke tunanin ko ta mutu ashe ya fi kowa sanin in da take? Shin daman Khamis yana tare da Zahidah? Toh a matsayin me xinta kenan ? Daga dukkan alamu Zahidah karuwa ce kuma 'yar maye shin Khamis ma kenan haka yake?
"Allah Ya sa abin da nake gani ba gaskiya ba ne, Allah Ya sa mafarki nake yi zan farka in ga ba haka ba ne." Iziddin ya faxa a bayyane yayin da hawaye ya fara surnano masa.
Khamis bai xaga idanuwansa ba har sai da ya isa cikin falo, yana shiga ya iske Zahidah a sanqare tayi zaman davaro a lungu, ta xaga ido da sauri ta kalli mai shigowa sai ta ga Khamis ne, ta qara shiga gagarumin tashin hankalin da ya fi na xazu, ta razana ta miqe da sauri ta tunkaro shi cikin murya mai makerketa tana faxin "ta ina ka shigo? Ba ka ci karo da wani mutum ba yanzu?"
Khamis ya dafe qirji ya zazzare ido, kan kace kwabo idanuwansa sun yi jajawur ya dube ta a zabura ya ce" kada ki ce min Izziddin ne ya gano gidan nan? Ban haxu da kowa ba, waye mutumin?"
Zahida ta yi ajiyar zuciyar farin ciki ta ce "Alhamdulillah. Ba Iziddin ba ne wani mutum ne da bana so ya ganka."
Khamis ya harare ta ya ce "daman har yanzu kina kula wani mutum daban kike munafunta ta?"
Ta jawo Khamis da sauri ta tura shi cikin quryar xaki, ta rufe dan kada Iziddin ya dawo cikin falo ya gan shi.
Iziddin ya shiga cikin mawuyacin hali ya sulale ya zauna akan xan dandamalin barandar qofar gidan, ya kasa qarasawa wajen motarsa balle ya iya tuqawa ya tafi gida. Fiye da mintina goma yana cikin wannan hali sannan ya miqe da qyar ya saka hannu a aljihu ya xauko hankici ya na goge hawaye ya juya ya kalli gidan ya sake kallo yana tunanin ya shiga gidan ya rutsa sun e ko ya tafi gida ya qyale su?
Yana cikin wannan hali ya ji qarar tsayawar wata mota a kusa da motarsa ya juya da sauri yana kallon mutanen da suke fitowa daga cikin motar, wani garjejen saurayi ne mai kama da qabila ya ke tuqa motar, xauke da buhun shikafa ya tunkaro gidan, da wata yar siririyar budurwa 'yar kimanin shekaru goma sha biyar zuwa goma sha bakwai tana riqe da ledoji a hannunta tana biye da shi. Shigarta babu laifi dai saboda atamfa ta saka riga da siket sai wani yalolon mayafin ta yafa.
Sun yi mamakin ganinsa kasancewar ba su tava ganinsa a gidan ba. Garjejen gardi ya bangaje Izziddin, gami da jefa masa harara haxe da ja masa tsaki, Izziddin ya matsa gefe ya bashi hanya ya wuce.
'Yar budurwar ce ta fara tafiya a hankali tana kallonsa yana kallonta sai ta duqa ta gaishe shi, takaici ya hana shi ya amsa ya ci gaba da kallonta, xan qugun nan kamar zai valle saboda siranta, bai daina harararta ba har ta shige, tana ta lave-lave kamar wata marar gaskiya.
Ya yi tsaki ya girgiza kai ya faxa a ransa "Wa'iyazu billah wannan 'yar yarinyar ma karuwa ce?"
Ya xan jima a tsaye ya na tunani ya yi kamar zai koma cikin gidan ya ritsa Khamis sai ya fasa yana so ya ga iya gudun ruwansa tukunna tunda ya tabbatar bai gan shi ba,sannan ya juya ya nufi wajen motarsa yana tafiya a hankali kansa a sunkuye a qasa, hawaye dai bai daina tsatstsafowa daga idanuwansa ba har ya isa bakin motarsa ya buxe kafin ya shiga sai da ya waiga kowacce kusurwa yana neman motar da Khamis ya zo da ita, ai kuwa ya yi arba da ita a wani loko. Abinda ya fahimta gidaje huxu ne a farfajiyar gidan iri xaya dan haka akwai mashiga da yawa, ta xaya get xin Khamis ya shigo shiyasa ma bai ga motarsa ba.
Iziddin ya shiga motarsa ya zauna, ya yi tagumi yayi shiru yana tunani, tashin hankali ya hana shi ya kunna motar ya tuqa, bugawa kawai zuciyarsa ke yi haka hannayensa karkarwa suke yi amma bai daina ambaton
'laa ilaaha illaa anta subhaanaka inni kuntu minaz zaalimiina" ba. Ya sai ta mudubin motarsa yana hangen bayansa, motar Khamis ce tabbas ya je ya voye a baya daga nan ya gasgata maganarsa ba gezau ba ce shi xin ne da gaske. Ya ci gaba da addu'a Allah Ya sa Khamis ya fito yanzu suyi arangama ya ga idanuwan marar gaskiya.
Kamar daga sama ya ji anyi masa sallama cikin kamilalliyar murya. Sai ya xago da sauri ya dubi in da sallamar ta fito. Abin mamaki sai ya ga wannan budurwar ce cikin fuskar tausayi da ladabi. Ta duqa ta sake gaishe shi.
Ya murtuke fuska yana yi mata kallo na rashin fahimta bai amsa mata ba. Kallon da yayi mata na tara saura kwata ya sa ta dabaibaye ta kasa faxar abinda ya kawo ta wajensa. Ya ci gaba da hararar ta, aka rasa wanda zai fara magana a cikinsu.
Ta daure cikin in'ina ta ce " wa kake nema na ga baka shiga ciki ba kuma zaka juya? Wa kake so in kira maka?"
Sai ya yi tsaki ya kawar da kai gefe ya ce "ke ma karuwar ce a hakan? Ko kuma kawaliya ce mai haxa zina?"
Ta yi sauri ta sunkuyar da kai qasa ta girgiza kai.
Ya sake tsuke fuska ya ce "kina qaramar ki, amma ki ka vata rayuwarki a karuwanci? Kamata yayi kina makarantar sakandire, yanzu haka sa'anninki suna makarantar kwana. Dan haka ki gaggauta barin jikin motata ni ba irinku ba ne." Ta ja da baya kaxan ta xago ta dube shi sai ta fashe da kuka ta ce "Sunana Aljannah, ni ba karuwa ba ce, ka taimake ni da kuxi zan ci abinci yunwa nake ji."
Ya sake fusata ya daka mata tsawa mai firgitarwa har sai da ta kusa faxuwa a qasa saboda razana.
"Ke matsa daga nan ko in vavvalla ki gida biyu, ni za ki rainawa hankali? Yanzu na ganki tare da qaton gardi kun fita a mota kun yi cefane za ki zo ki ce min in baki kuxi za ki ci abinci?" Izziddin ya faxa a fusace.
Aljannah ta sharce hawaye ta ce "ledojin da ka gani a hannuna kayan xinkin Anti Zahidah ne na karvo mata, buhun shinkafar nan kuwa bani da iko da shi sai sanda suka ga dama suke sa ni in dafa musu. Yawanci ma sau xaya ake yin girki a sati wato duk ranar juma'a ake dafa buhun shinkafa xaya a rabawa almajirai sadaka, ranar ne kaxai nake ci in qoshi amma sauran ranaku kowa shi yake ciyar da kansa. Samarinsu ke taho musu da abinci kala-kala ko su xauke su, su fita dasu wajen cin abinci su ci a can, wata ran da yunwa nake kwana ko in bi shara in ci guntun abincin da suka rage."
Ya daxe yana yi mata kallon jin haushi da tuhumarta akan rashin gaskiya, gaba xaya ya qaryata abinda take faxi da wanda zata faxa nan gaba. Haushi take bashi tamkar ya jawo ta ya xima.
Ya ce "ki koma gidan iyayenki mana dole ne zaman barikin?"
Ta sake rusa kuka ta xago da jajjayen idanuwanta ta dube shi ta girgiza kai.
Ta ce "bani da uwa, ba ni da uba, ba ni da dangi, ni shegiya ce."
Ya yi shiru yana kallonta kallo na takaici saboda rainin hankalin da 'yar qaramar yarinyar take so ta yi masa, ya tabbatar yaudararsa aka turo ta yi saboda an san shi da tausayi. Dan har ya fara jin yanayin tausayi zai kama shi, sai ya yi sauri ya kawar da shi gefe, ya kunna motarsa da sauri ya juyo ya harare ta.
Ya ce "ki je a sake shiryo miki wata sabuwar qaryar wannan bata daidaitu ba, saboda shegen da aka haifa ba aure ba'asan takamaiman ubansa ba dole yana da uwa, uwar kuma tana da iyaye da dangi dan itama ba daga sama ta faxo ba."
Ya ja motarsa ya fice daga cikin get xin da sauri ya bar ta anan a tsaye tana kuka.
Tafiya yake kawai ba tare da ya san in da zai je ba, ya tabbbatar idan ya je gida matansa ba zasu bar shi ya kulle kansa a xaki ba saboda ya shiga yanayin da basu tava ganinsa a ciki ba. A gefen hanya ya ja ya tsaya ya kulle kansa a cikin mota, babu abinda da yake tashi a cikin motar daga karatun kur'ani sai sanyin Ac zuciyarsa tana ta tafasa yana faxa yana maimaitawa a zuciyarsa
"xan adam abin tsoro ne, dawa kuma zan sake yarda a duniya mutanen dana yarda da su a rayuwa, Zahidah da Khamis sun ci amanata.".
Bai san dare ya yi ba, ashe har magaruba ta wuce bai yi Sallah ba sai da ya ji xan sanda ya kwankwasa masa gilas xin wundo, sai yayi firgigit ya dawo daga duniyar tunanin daya tsunduma, ya sauke gilashin motar da sauri cike da mamaki.
Xan sanda ya tambaye shi "lafiya ka bar mota a kunne ka zauna a ciki tunda yamma?"
Sai a lokacin Izziddin ya tabbatar ya daxe anan a tsaye ashe. Ya sosa qeya ba tare da ya san amsar da zai bashi ba, tun daga nan xan sanda ya fara tunanin ya sami nama, wannan bashi da gaskiya.
Xan sanda ya sake sava bindigarsa a kafaxa, ya daka masa tsawa ya ce "dalla Malam fito daga cikin motar nan baka da gaskiya. Daga ina kake kuma ina zaka je?"
Iziddin ya yi murmushin qarfin hali ya saka hannu a aljihu ya zaro ID card ya nunawa xan sanda, nan da nan xan sanda ya qame dan girmamawa, gami da yi masa kirari mai haxe da maula. Izziddin ya kunna mota ya ja ya tafi, ba tare da ya furta kalma ko xaya ba.
Ya ci sa'a ya sami masallaci a hanya ya tsaya yayi alwalla ya yi sallar magruba yana idarwa aka tayar da sallar isha'i, ya bi jam'i, da aka idar ya zauna ya ci gaba da jero addu'oi, yana roqar Allah Ya fitar dashi daga cikin matsannanciyar damuwar daya tsinci kansa a yau, Allah Ya shiryi aminansa da su ka vace daga kan hanya madaidaiciya. Bai fito daga masallaci ba har sai da qarfe goma na dare ta yi, yana shiga mota ya iske wayarsa na kururuwa, kafin ya amsa ta katse ya duba ya ga missed calls 31 gami da saqonni tara dukka daga matansa Amatullah da Nauwarah. Sai ya ja dogon numfashi ya lumshe ido ya jingina kansa kan kujera yana mai tsananin damuwa. Ya tabbatar yau idan ya shiga gida a cikin wannan yanayin za'a sami matsala, hankalin matansa zai tashi. Kuma al'adarsa ce idan ransa ya vaci baya son magana, haka baya cin abinci, ya san sun shirya masa abinciccika kala-kala shi kaxai suke jira shi kuma har ga Allah ba zai tava iya cin komai ba.
Wayarsa ce dai ta ci gaba da kururuwa ya na dubawa ya ga sunan Amatullah ne uwar gidansa, Ya danna gami da qirqiro murmushin qarfin hali.
Ta yi ajiyar zuciyar jin daxi "haba maigidana, haba dan Allah, ina ka shiga yau? Ka bar mu da fargaba mun kasa sukuni babu in da bamu buga waya muna cigiyarka ba daga kai har Khamis babu wanda ya xauki wayarmu, daga nan na tabbatar kuna tare. Shima Sahiba matarsa ta kira tana tambayata ko yana nan gidan? Dan bai koma gida ba tunda safe shima."
Sai ya ji ransa ya vaci data ambaci sunan Khamis ya cije baki ya ce "haka ne, bana kusa na yi nisa da gida ku yi haquri da qyar ma zan kwana a gida a yau saboda abinda nake yi zai kai ni dare, ku ci abinci ku kulle gida sai da safe kawai. Ki bawa Nauwara waya idan tana kusa da ke mu gaisa."
Amanatullah ta miqawa Nauwara waya a sanyaye, ta karva cike da fargaba kasancewar ta ga yadda abokiyar zamanta ta shiga damuwa. Ta yi masa sallama cikin sanyayyiyar murya tana mai fargabar jin abinda zai faxa mata.
Ya yi xan murmushi ya ce "Amarya ya gida? Kar ku damu fa yau ba zan kwana a gida ba ina cikin wani uzurin daya sha min kai."
Ta sulale ta zauna saboda fargaba ta ce "wanne irin uzuri ne darling, har da zai sa ka kwana a waje alhali baka tava yin haka ba?"
Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Nauwara, kin san ban tava yi miki qarya ba ko? To kada ki takura min da tambaya yadda zan kasa faxa miki gaskiya, ina cikin wani uzuri kada ki damu gobe zan dawo gida. Kin ji ko?"
Ta narairaice murya ta ce "haka ne, amma yaya za'ayi da 'birthday cake' xinka da zaka yanka, ka manta yau ne ranar birthday xinmu ni da kai?"
Ya dafe kai ya ce "kash! Na manta wallahi amma ai bai vaci ba Amatullah ta wakilce ni, ku yanka kek xin tare da yara, ayi hotuna idan na zo zan gani."
Ta miqawa Amanatullah wayarta dan ba zata iya isar da wannan mummunan saqon gare ta ba. Amatullah ta karva ta kara a kunnenta ya sake qirqiro murmushin dole.
Ya ce "uwar gida ran gida, haba tawan ke ce fa babba idan ba ki fahimce ni ba Nauwara ba zata fahimce ni ba, dan Allah ku kwantar da hankalinku ina nan lafiya qalau. Ki taya ta yanka kek xin ke da yara."
Ta yi dariyar farin ciki ta ce "toh shikenan yallavai zan kwantar mata da hankali. Allah Ya kiyaye ka Ya dawo mana da kai lafiya."
Ya ce "amin. Allah Ya yi muku albarka. Sai da safe."
Su ka kashe waya, tabbas matansa basu ji daxi ba amma hankalinsu ya kwanta da su ka ji yana nan lafiya kuma sun shaide shi sun tabbatar ba zai yi musu qarya ba. Suka sha shagalinsu a cikin gida su biyu da su da yaransu guda huxu.
Yana kashe waya, ya kunna mota ya nufi NICON Hotel, kai tsaye ya wuce wajen ajiye motoci ya sami lungu ya saka motarsa gami da rufe motar da tanfol gudun kada a gane motarsa, ya fito kai tsaye ya nufi reception. Yau ce rana ta farko daya tava kwana a wani Hotel a garin nan amma ya san wannan Hotel xin sosai saboda sun sha zuwa su sauke baqi abokan aikinsu.
Kasancewar asabar ce ana hutun qarshen mako (weekend) ya cika da fargaba kada a rasa xaki, yana shiga ya tambayi ma'aikatan da ya iske ko akwai xaki? Aka ci sa'a yau xakunan basu cika ba, su ka tabbatar masa akwai xin kuma a xakunan ma manyan ne suka rage, maqudan dubunnai su ka karanto masa na kwana xaya kacal, aka bashi mukulli a jikin mukullin akwai lambar xakin, kai tsaye ya wuce cikin na'urar da take kaiwa sama (lift) ta hau sama da shi hawa na uku.
Haxuwar xakin nan ta isa zaka rantse a ba'a qasarmu kake ba, tabbas anyi koyi da qasashen da suka dade da ci gaba, wannan shi ake kira aljannanr duniya. Bai damu da kayan da aka qawata xakin ba saboda tsantsar damuwar data ke addabarsa ga yunwa mai tsanani. Saboda tsabar yunwa har jiri ya fara xaukarsa ya yi kamar zai faxi nan da nan ya kama kujera ya riqe sannan ya lallava ya lalubi gado ya kwanta, ya tabbatar idan bai ci komai ba za'a iya zuwa a xauki gawarsa kafin safe, baya fatan ya mutu a hotel a zargi gawarsa.
Ya laluba ya jawo wayar da take gefen gadon ya buga lambar reception ya shaida musu yana buqatar abinci ne, su kuma suka sada shi da lambar restaurant. Nan fa suka dinga zano masa kala-kalar abinci da namomi da suke da shi, naman mutum ne kawai bai ji sun kira ba. Ya katse kafin su vata masa lokaci da yawa, ya ce a kawo masa soyayyen dankalin turawa da soyayyen kwai, da kuma rabin kaza, sai shayi ruwan zafi kaxai da lipton.
Bai iya tashi daga in da yake kwance ba har sai da yaji ana danna qararrawar xakin bayan mintina ashirin, babu tantama ya san mai kawo abinci ne ya iso. Ya miqe da qyar ya buxe qofa sai ga wani siririn mutum xauke da tafkeken faranti a danqare da kayan daxi har ma wanda bai ce a kawo ba aka haxo. Ya gaishe da maigida Iziddin sannan ya qarasa kan teburin cin abinci ya ba je masa gami da jeer masa komai a in day a kamata, ci ne kawai ya yi saura, day a gama sai ya fita ya jawo qofa ya rufe.
Izziddin ya daure ya laluba ya hau kan tebur ya zauna, ya kalli abincin ya yamutse fuska dan idan in ba dole ba, ba zai ci abincin nan ba dan bai bashi sha'awa ba ko kaxan, ya fara da shan ruwan zafi dan hanjin cikinsa ya warware sannan yayi ta turawa kaza da dankali ba dan daxi ba sai dan ya ceto rayuwarsa da halaka.
Daga ya tuna Zahidah, Khamis da Aljannah sai ya ji gabansa ya yanke ya faxi. Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un.
Haka ya dinga dafe qirjinsa dan kada zuciyarsa ta ragargazo ta faxo qasa. Ya ci abincin ba laifi amma dai ba wani mai yawa ba, ya tashi ya faxa kan gado ya runtse ido, bacci bai tunkaro idanuwansa ba kuka ne ya varke masa, sai a lokacin ya sami damar kwankwajewa da kuka yadda ya kamata dan xazu kasa yi yayi. Ya yi kuka har ya gaji, ya yi addu'a har kamar yawun bakinsa zai qafe. Ya jawo filo ya canja vangare ya kwanta wai ko barci zai zo amma abu ya faskara. Ya kwanta yayi lamo kamar sumamme amma bai sume ba, kuma ba bacci yake yi ba. Yana runtse ido sai yaga fuskar Zahidah da irin yananyin daya ganta, sai yayi farat ya buxe ido ya gyara kwanciya ya sake runtse ido sai ga fuskar amininsa Khamis a yadda ya hango shi.
"Ka taimake ni da kuxi zan ci abinci yunwa nake ji. Ba ni da uwa, bani da uba, ba ni da dangi ni shegiya ce" Kalaman siririyar yarinyar nan Aljannah suke sake dawo masa a cikin kunnuwansa tamkar zuwa take tana raxa masa, ya zabura ya miqe zaune yana huce.
Ya tabbatar idan ya yi wasa yau zai zama zautacce dan haka ya gaggauta barin kan gadon, ya buxe qofar baranda ya fita ya tsaya yana kallon qasa. Abin mamaki daya duba agogon hannunsa qarfe xaya na dare daidai amma tamkar gari ne ya waye yadda motoci tsala-tsala suke tsayawa mata da maza, matasa da dattijai, kuma attajirai, masu mulki da 'yayan masu mulki duk sune suke ta firfitowa suna tunkarar wani katafaren xaki mai girman gaske, da alama mashaya ne kuma gidan rawa (club).
Yana daga sama yana hange bai dai tabbatar ba amma ya hango kamar Zahidah da Khamis, abinda ya sa ma yake zargin su ne xin tabbas saboda ya hangi wannan siririyar yarinya Aljannah tana biye da su a baya, suka nufi cikin xakin. Yana dai tunanin ko gezau idanuwansa ke yi masa, ya fara tunanin kwakwalwarsa ta sami tavuwa a yau xin nan. Amma duk da haka sai ya bisu ya tabbatar da abinda yake zargi gaskiya ne ko ba gaskiya ba ne. Ya zabura ya fito daga baranda ya buxe qofar xakin ya fice da sauri bai damu da kulle xakin da mukulli ba, ya fice abinsa.
Har ya nufi wajen qofar shiga Xakin masha'ar sai ya lura ya fita daban saboda shigarsa ta manyan kaya kuma duk a cukurkuxe, jama'a na ta kallonsa. Ya waiga gefe sai ya hango katafaren shago na sayar da kaya (butik) nan da nan ya nufi ciki duk da bashi da kuxi tsaba amma yana da katin cirar kuxi a cikin wallet xinsa da shi ya biya. Mai jiran kantin ya taya shi zaven kayan daya dace da shi na shiga club. Wando (jeans) baqi da riga mai dogon hannu fara mai zanen baqi-baqi, hula (Face cap) baqa haxe da wani kwafcecen gilashi fari aka haxa masa da hular gashi da qasumba daya buqaci yana son ya canja kama. Akwai qaramin xaki mai xauke da qaton mudubi ya shiga ciki ya canja kaya, sannan mai jiran shago ya shigo ya taya shi saka hular gashi da gemu, ya fito tsaf a kamannin 'yan caburos sosai da ya dubi kansa a mudubi shima kansa bai shaida kansa ba balle wani, ya yi imanin babu mahalukin da zai shaida shi a haka hatta mahaifiyar data haife shi kuwa.
Ya nufi wajen da ake wannan baxala dan ma ya qi yarda yayi irin tafiyar da mai jiran shago ya koya masa wato tafiyar nigogi a zazzage wando kamar zai savule qasa (Ass down).
Bai san dokokin da ake bi ba kafin a shiga ciki amma ya tsaya a baya yana kallon yadda masana ke yi, biyan kuxi ake kafin a shiga kuxi mai yawa kuwa dan haka sai ya juya ya tafi bakin get in da ya hango injin fitar da kuxi ATM ya ciro kuxi da yawa ya zuba a aljihu, ya dawo ya biya ya shiga. Ya tsinci kansa a cikin wata irin quntatacciyar rayuwa, idanuwansa suka dinga hasko masa abinda bai shirya gani ba, kunnuwansa suka dinga jiyo masa abinda bai halatta ba. Babu abinda ya ke tashi a wajen sai kixa ana ta casu, kan kace kwabo 'yan mata sun baibaye shi haka yake warvar da su yana tunkuxe su har suka gaji da binsa suka qyale shi, ya ci gaba da zagaye yana neman abinda ya ke tunani ya gani. Yana ta ci gaba da zagayawa har ya gama zagaye 'yan rawar nan tsaf bai ga idon sani ba, ya dawo ya zagaye waxanda ke zazzauna suna kora ruwan hajijiya nan ma bai ga kowa ba, har ya juya zai fita sai ya jiyo wata murya wacce ta yi masa kama da muryar da ya sani kuma cikin yarensa ake yin magana wato Hausa. Ya juya da sauri ya dubi in da maganar ke fitowa sai yayi arangama da yayan Nauwara matarsa, Na'if uwarsu xaya ubansu xaya Nauwara amaryarsa shi da Laurat. Laurat qawar Nauwara ce sosai kuma makwabciyarsu ga gida ga gida kamar yadda ya ke da Khamis, sun yi rawa sun gaji sun sha abar sun yi tatul suna tangaxi.
"Subhanallah" Iziddin ya faxa a bayyane, yayin da ja baya ya tsaya a gefe yana kallonsu kallo na takaici. Bai yi mamakin Na'if ba saboda ya san halinsa daman iyayen suna ta fama dashi bayan sata da shaye-shaye har da neman mata, yana xaya daga cikin masu saka Na'if a gaba ayi masa faxa ya daina wannan halin. Amma yayi mamakin Laurat sosai, bai tava zaton itama haka take ba dan haka ya zama dole ya raba matarsa da wannan muguwar qawa. Su ka haxa ido da shi amma basu gane shi ba saboda ya canja kama, ya ji daxi da yin hakan.
Ya ci gaba da waiwaye-waiwaye sai ya yi kicivus da Aljannah ta tunkaro shi gadan-gadan sai ya shixe a tsaye ya zaci ta gane shi, da ta zo daf da shi sai ta kauce ta shige ashe ba wajensa ta zo ba, ta nufi wajen sayar da lemo da giya ta sayo lemon da aka aiko ta, ta dawo ta wuce ta gabansa tana tafiya kamar silan kara wai nan riga da wando ta saka (jeans da t-shirt) kanta babu xankwali ta saka ribbon ta tufke gashin kanta, da yake tana da gashi sosai. Iziddin na biye da ita a baya lungu-lungu saqo-saqo har ta isa wani katafaren falo mai xauke da jajajen kujeru da jan kafet na alfarma, sun fi seti goma an zagaye, mata da maza suna zazzaune ana ta masha'a nan ne fadar manyan 'yan iskan. Qirjinsa ya ci gaba da dukan uku-uku, lallai yau ya ga tashin hankalin da bai tava ganin irinsa ba, Zahida da Khamis ya hango tare suna zazzaune suna ciye-ciye da shaye-shaye suna dariya suna shewa yayin da idanuwan Iziddin suka cika da hawaye ya laluba wata kujera da ke gefe ya zauna. Ya xaga kai ya sake kallon Zahidah shigar da ta yi bai tava ganin irinta a ido biyu ba sai dai a fim xin turawa, matsatstsiyar riga ce ja iya cinya, babu hannu a rigar sai dogon takalmi mai tsinin gaske launin ja. Kanta babu xankwali ta zubo kitson da aka yi mata na qarin (attachment) har gadon bayanta, kasancewarta fara ce sosai sai ka rantse nasara ce, jikin nan sanval jajawur, gefenta kuwa Khamis ne abokinsa shima shigar ta tantiran 'yan duniya riga ce ya saka bata da hannu da wando iya guiwa, yana kora wani abu a kofi bai tantance ba lemo ne ko giya.
Aljannah kuwa da ta kai lemon sai ta rave a gefe ta tsaya, yayin da wani tantirin xan iska ya zagayo ta bayanta ya yi mata cakulkuli ya xaga ta sama cimak yana shilla ta kamar wata mage. Ta calla qara gaba xaya aka waiwayo ana kallonta, sannan aka dinga sheqa dariya ana qyaqyatawa irin ta zamanin jahiliya.
Zahidah ta yi dariya ta ce "Liyo ka ajiye min 'yata bata saba ba, ka barta ta girma tukunna."
Liyo ya yi dariya ya ajiye ta, Aljannah ta zura da gudu bayan Zahida ta tsugunna jikinta yana rawa tana hawaye.
Liyo ya ce ni dai ina kamu nan da shekara ni zan fara da ita."
Suka kwashe da dariya gaba xayansu.
Samir ya ce "na riga ka dalla, yarinyar nan na daxe ina jira ni zan fi kula da ita."
Khamis ya ce "to ku bari in raba muku gardama, duk wanda yake son Aljannah ya yarda zai dinga ajiye mana naira dubu hamsim duk qarshen wata har na tsawon shekaru biyu sannan ta girma sai a damqa masa ita shi kaxai."
Samir ya zabura ya ce "na yarda wallahi."
Liyo ya ce "a a ayi mana ragi, ina laifin ma ace naira dubu ashirin a wata kuma nan da shekara xaya ma ai ta qara girma ba sai an shekara biyu ba."
Aljannah ta fusata ta fashe da kuka ta girgiza kai, ta ce "ni wallahi bana son kowannensu." Ta miqe ta fice da gudu ta bar falon.
Liyo ya zabura ya ce "kamo ta nan! Kamo ta nan!! Ku tare min ita." Aljannah ta sake takawa a guje. Gaba xaya 'yan wajen su ka sake kwashe da dariya har da qyaqyatawa da buga qafa.
Iziddin ya sunkuyar da kai qasa ya riqe kai yana ta jujjuyawa ko Allah zai sa ya farka daga bacci idan ma mafarki ya ke yi. Sai bai farka ba, ya tabbatar ba zai farka ba, ba bacci ba ne a zahiri ne. Ya xaga ido ya kalli Zahida, ya kalli Khamis tabbas ya yi amanna su xin ne a zahiri a cikin Hotel, a Hotel xin ma a gidan rawa, a gidan rawar ma a xakin shan giya. Ya sake tunano Zahidah a cikin hijabi, ya tuno Khamis a masallaci a gaba yana jan jama'a sallah, ya sake juyowa ya dube shi a a tsakiyar mata har yana kora barasa.
Haka Iziddin ya dinga sheshsheqa kamar numfashinsa zai xauke, abinda ya fahimta kuma a cikin 'yan iskan ma Zahidah ita ce shugabarsu dan wani girma ake bata na musaman, tamkar ma idan mazan suka ga wata suna so sai an biyo ta kanta taba da izini tukunna. Iziddin ya cije levensa har kamar zai fitar da jini, ya ji kamar zai tashi ya shaqi wuyan Khamis ya dai sake daurewa, bai san sanda ya tashi a fusace ya fice daga cikin xaki ba ya fita waje ya tsaya yana shaqar iskar Allah.
Daga gefensa yake jiyo sheshsheqar kuka, ya juya da sauri ya dubi wajen sai ya hango Aljannah ta kifa kai akan gwiwarta tana kuka. Ya juya yana kallonta ba tare da ya san abinda zai iya yi mata ba, sai da ta yi kukan ya ishe ta sannan ta lura da cewar ga wani a gefenta ya zuba mata ido yana kallo tabbas ya yi mata kama da macuci kuma xan ta'adda sai ta miqe tsaye da sauri ta sake runtumawa da gudu cikin duhu tana rusa kuka. Yanzu ya fara gasgata abinda yarinyar nan ta faxa masa xazu, cewar ita ba karuwa ba ce.
Qarar ihunta ya juyo a cikin duhu, ya sa shi zabura ya bi bayanta da gudu, ya iske wani qaton qabila ne ya damqe ta. Iziddin ya fusace ya kai masa bangaza gami da yi masa tsawa mai firgitarwa. Cikin harshen turanci ya ce ya sake ta qanwarsa ce, nan da nan ya ajiye ta ya yi gaba daman a buge yake.
Iziddin ya dube ta cikin fushi ya yi mata tsawa mai rikitarwa "ke wacece? Me ya kawo nan kina qaramarki?"
Ta sake rikicewa jikinta na rawa ta ce "sunana Aljannaah, ba ni da gida, bani da uwa, ba ni da uba, ni shegiya ce."
Iziddin ya gigita sosai da ya ji ta sake maimaita abinda ta faxa masa xazu duk da ya tabbatar bata gane shi ba amma tana nan akan bakarta ita shegiya ce. Ya daxe a tsaye yana kallonta sannan ya ce "menene ma'anar shegiya?"
Ta sharce hawaye da gefen gyalenta ta ce "tsinta ta aka yi."
Sai ya ji gabansa ya yanke ya faxi, ya dafe kai saboda tsanani sarawar da kansa ya yi. Ta katse tunanin da yake yi.
Ta ci gaba da cewa "ka taimake ni kawu, ka bani kuxi in ci abinci."
Ya kalle ta ya ce "har yanzu baki abincin ba?"
Sai ta xago kai da sauri ta dube shi cike da mamakin tambayar da ya yi mata, ta gyaxa kai ta ce "tun da safe ban ci komai ba, kuma ina so in bar gidan karuwai ka samo min aiki ko na wanke-wanke ne."
Tashin hankali ya kai tashin hankali sai ya yi ajiyar zuciya ya ce "Za ki bini mu je gidana in ajiye ki mu zauna tare ina baki abinci? Ko in kama miki xaki a cikin hotel xin nan in voye ki kina cin kayan daxi."
Aljannah ta zabura ta ja da baya ta gigiza kai ta ce "ba na so."
Ya yi murmushi ya ce "Ki kwantar da hankalinki, ki xauke ni da zuciya xaya ni ba xan iska ba ne ba zan cutar da ke ba haka ba zan bari a cuce ki ba, zan kare miki mutuncinki haka zan taimaki rayuwarki, ki biyo ni in har zuciyarki ta kwanta da ni." Ya fara tafiya tana biye da shi, kallonsa ta ke yi amma a tsorace daga yayi magana sai ta ja da baya, har suka fito haske ya nufi cikin Hotel, sai ta ja da baya ta tsaya ta daina tafiya ya juyo ya dube ta sai ya ga ta arce da gudu ta nufi cikin xakin rawa. Ya yi kasaqe yana tunain yadda zai yi da ita haqiqa ya gasgata yarinyar nan ba karuwa ba ce, haka maganar da take faxa akwai qamshin gaskiya bata da in da zata je amma bata son zamanta da su Zahidah.
Ya juya ya shiga cikin Hotel da sauri ya wuce kai tsaye xakin abinci (restaurant) ya umarce da su zuba masa shinkafa da miya da kaza danqwaleliya guda xaya. Aka naxe a robobi ya buqaci da a saka masa kuxin a cikin list xin sa, ya fito ya nufi xakin kixa, a bayanwundo ya tsinkayo ta daga waje tana leqen jama'ar da suke cashewa. Ya na isa yayi mata sallama sai ta zabura zata gudu, data ga shine sai ta tsaya, ya miqa mata abincin, tana rawar hannu ta karva. Sannan ya saka hannu a aljihu ya damqo kuxi ya miqa mata, ya sake zaro wata qaramar takarda ya miqa mata.
Ya ce "Zauna ki ci ki qoshi, ga kuxi naira dubu goma ki dinga sayen abinci kina ci, idan ya qare ga lambar wayata nan a jikin takarda ki kira ni zan zo in qara miki. Ki yi min alqawari ba za kiyi zina ba haka ba za ki sha giya ba, ki daina biyo Zahidah club saboda da qarfi da yaji zasu vata miki rayuwarki."
Aljannah ta ce "Ka san Zahidah ne?"
Ya girgiza kai ya ce "na ji ana faxar ta dai a gari. Karuwa ce ko? Yar maye?"
Aljannah ta gyaxa kai ta ce "eh, ogarsu ce ma."
Ya yi shiru ya sunkuyar da kai qasa can ya xago ya ce "waye dadironta kuma?"
Aljannah ta ce " Khamis ne, yanzu ma suna cikin nan suna tare."
Ya runtse ido sai hawaye ya fara kwaranya, ya sa hankici ya goge.
Ya ce "yaushe ya ke samu ya zo wajenta alhali daga safe zuwa yamma yana wajen aiki, da daddare kuma yana wajen matarsa?"
Ta ce bai cika zuwa da rana ba sai da tsakar dare daga qarfe xaya na dare zuwa asuba muke zuwa club kullum. Ka sansu ashe?"
Ya girgiza kai "ban san su ba ina jin labarinsu dai."
Aljannah ta ce "yaya sunanka?"
Ya yi shiru can ya ce "sunana Aljannah nima."
Sai ta fashe da dariya.
Ya juya ya fara tafiya a sanyaye ya nufi cikin Hotel. Aljannah tana tsaye tana kallonsa sai data bari ya yi nisa.
Ta kwalla masa kira "Aljannah!"
Iziddin ya juyo da sauri ya dube ta.
Ta ce "Allah Ya baka Aljannah maxaukakiya."
Ya xauki lokaci mai xan tsawo ya na dubanta, hawaye ya cika masa ido.
Ya gyaxa kai.
Ya ce "Amin Aljannah! Allah Ya haxa mu ni da ke a cikin Aljannah maxaukakiya."
Ya juya ya ci gaba da tafiya, kuka ya ke yi tukuru, haka itama, ta sulale ta zauna akan wani tudu ta kalli kuxin daya bata ta, sai ta sumbaci kuxin sannan ta soke a cikin aljihun wandonta. Ta buxe abincin, kamshi mai daxi ya daki hancinta, ta yi murmushin farin ciki ta lumshe ido ta shaqa.
Ta faxa a bayyane "Allah Ka shiryi wannan bawan na Ka daya kyautata min, Ka sa ya fita daga irin wannan rayuwa ta iskanci."
Ta fara cin abincin tana figar naman kaza hannu baka hannu kwarya saboda tsananin yunwar da take addabar ta.
Iziddin ya shiga xakinsa ya kwashe gemuna da gashin daya tula a kai ya watsar a qasa, babu kalmar da ya ke Ambato sai "Astagfirullah. Lah haula wala quwwata illah billah."
Abubawa goma da ashirin suka taru suka haxe masa, yau ce ranar da Allah Ya amsa addua'arsa Ya nuna masa Zahidah, sai dai ya ganta a ciki mugun hali murnarsa gaba xaya ta koma ciki har ya gwammace dama bai ganta ba, babban abinda ya fi tayar masa da hankali da ya ganta tare da amininsa wanda ko a mafarki bai zaci zai ci amanarsa ba, ko a mafarki bai zaci xan bariki ba ne, koda zai yi barikancin bai zaci zai yi da Zahidah ba. Alhali ya san kowacece Zahidah a wajensa, ya fi kowa sanin muhimmancinta a rayuwarsa. Bai tava zaton Khamis ya san in da Zahidah take ba, ya bar shi yana ta wahalar nemanta gari-gari, qasa-qasa kuma hard a shi ake shan wahalar nemanta xin amma ya qi nuna masa ya san in da take.
"Ga wannan yariyar Aljannah itama ta faxo cikin matsalolina, matsalarta ta tsaye min a rai. Wayyo sarkin sarakuna Allah Ka yi min agaji. Xan adam kenan mai wuyar gane hali. Duniya! Duniya gidan kashe Ahu. Rayuwar duniya da wuya. Duk sanda Allah Ya binciko fiyil xin bawansa idan Ya damqe shi sai ya ji dama ba'a halicce ka ba." Iziddin ya faxa yayin daya sulale ya kwanta akan katafaren gadon nan.
Irin wannan yanayi Iziddin yake ji a yau tamkar duk bala'an duniyar nan gaba xaya aka jifga masa. Ya duba agogon da yake xaure a hannunsa ya ga wayam ya jefar dashi a shagon day a sayi kaya a garin canja kaya, ya lalubi wayarsa a aljihu ya ji ba komai, sannan ya tuna a mota ya bar ta, ya dubi agogon bango qarfe uku saura kwata, ya yunqura zai tashi ya je yayi sallar nafila, ya ji ba zai iya tashi ba. Ya koma 'javar' ya kwanta sai ya shiga karanto addu'ar da idan abubuwa suka tsananta a gare ka.
"Allahumma laa sahala illaa maa ja'altahu sahlan wa anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahlan."
Sai barci marar daxi ya sace shi. Asubah ta gari Izzy!!!
RANAR LITININ 2 GA WATAN 6 2014
Bai tashi farkawa ba sai qarfe goma sha xaya na safe, gari ya waye tangararan har rana ta dallaro.
Kalmar daya tashi da ita a bakinsa ita ce
"laa ilaaha illaa anta subhaanaka inni kuntu minaz zaalimiin"
Saboda ya yi mummunan mafarkai hakan ya sa ya tashi a gigice, haka ya manta yawan shekarun rabon da rasa sallar assalatu sai yau. Haqiqa rashin nutsuwa a rayuwa yana jawo rashin cika ibada.
Ya tashi ya zauna ya yi shiru ji yake gaba xaya bashi da lafiya daga jikinsa har cikin zuciyarsa, ya yunqura ya miqe tsaye sai ya koma ya zauna kansa ke ta ragargazar ciwo yana kyautata zaton alamar hawan jini zai kama shi. Ya jima a zaune sannan ya miqe da kyar ya shiga banxaki ya xauro alwalla ya zo ya yi sallah, yana ganin rana, rana na ganinsa.
Kunyar Ubangijinsa ta kama shi sai ya sunkuyar da kai qasa yana hawaye yana faxin
"Astagfirullah wa atubu ilaihi."
Ya daxe yana karanto zikirin safe kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya koyar da mu.
"Asbahanaa wa asbahal mulku lil-laahi wal hamdu lil-laahi laa ilaaha illallaahu wahdahu laa shariika lahu, lahul mulku walahul hamdu wahuwa alaa kulli shai'in qadiirun, Rabbi as'aluka khaira maa fii haazal yaumi wa khairi maa ba'adahu,wa'azu bika min sharri maa fii haazal yaumi wa sharri maa ba'adahu,Rabbi a'uzu bika minal kasali wa su'il kibari, Rabbi a'uzu bika min azabin fin naari wa azabin fil qabri."
Ya xaga hannu sama ya yiwa Allah kirari, ya yi kuka, ya roqi Allah da Ya fitar da shi daga ciki uqubar nan daya shiga, da wacce yake shirin ruftawa.
Ya fita baranda ya kalli xakin rawa bai ga kowa ba, an rufe ma, wajen bidirin na dare ne kawai, tsakiyar dare a lokacin da Ubangiji Ya ke saukowa duniya da kanSa Ya na neman wanda zai roqe Shi ya amsa masa, su kuma a lokacin suke kokawar sava maSa.
Ya girgiza kai ya shigo xaki kai tsaye ya wuce banxaki ya shiga ya yi wanka. ya fito zai saka kaya sai ya tuna ya bar shaddarsa a shagon sayar da kaya jiya da ya canja. Hankalinsa ya yi matuqar tashi saboda iyalansa zasu yi mamakin yadda aka yi ya canja kaya, zargi zai shiga tsakaninsu alhali bai saba yi musu qarya ba, sannan gaba xaya ba al'adarsa ba ce ba ma saka tsukakkun kaya sai jifa-jifa in da dalili. Ba yadda ya iya haka ya saka kayan, ya fito sannan ya zare mukullin yana qoqarin kullo qofa. Kusa da xakin da yake wasu mutane biyu ne suka fito mace da namiji suma da alama sun fito zasu tafi, suna xaga kai suka haxa ido da juna sai gaba xaya su ukun zuciyoyinsu suka harba 'VAM'. Kallon-kallo suke yiwa junansu.
Kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un." Iziddin ya faxa cikin raxa.
Irin wannan kalma ce ta ke ta fita daga bakunan saurayi da budurwar nan. Na'if ne da Laurat suka yi kicivis da Iziddin, kowa na tunanin me ya kawo xan uwansa nan? Cikin sanyin jiki kowannensu ya ke rufe qofa. Tabbas Iziddin girma ya faxi saboda yaqin da yake ta tafkawa akan mugayen halayen Na'if, kullum suka haxu sai ya ratattaka masa wa'azi yana karanto masa azabar da Allah Ya tanada akan 'yan maye,mazinata da varayi, kai ka ce limami ne ya hau mambari yana huxuba, Sai gasu yau a sahu xaya. Duk da dai Na'if bai gama zarginsa da iskanci gaba xaya ba amma
'idan babu rami meya kawo zancen rami?' In ji masu iya magana.
Na'if ya saki murmushin jin daxi ya yafici Laurat ya yi mata qifce da zunxe ya nuna mata Iziddin, sai ran Iziddin ya sake vaci hankalinsa ya yi matuqar tashi ya zare mukulli ya gaggauta barin wajen da sauri. Yana fita reception ya basu mukulli aka karanto masa maqudan dubbunnan da ake binsa kuxin xakin kwana xaya da kuxin abinciccika. Ya cire musu kuxi ta jikin injin cire kuxi a take ya biya ya fice, bai tsaya a ko ina ba sai a wajen daya ajiye motarsa. Ya shiga da sauri ya ja ya fita daga harabar Hotel kafin ya sake cin karo da idon sani kuma.
Kai tsaye ya wuce ofis babu abinda ya yi sai saka hannu (signing), haqiqa abokan aikinsa sun ga canjin yanayi a tattare da shi a yau. Ya yi wuf ya fito ya na shirin shiga mota sai sakatariyarsa mai suna Na'ila ta runtumo da gudu ta tsayar da shi. A fusace ya juyo ya dube ta yana sauraron ta faxi abinda yake tafe da ita ta bar wajen.
Cikin huci da sheshsheqa ta gaishe shi saboda gudun data yi. Ya amsa a gaggauce ya matsu ta faxi abinda zata faxa ta kauce masa da gani.
Ta ce "Ranka ya daxe MD ya na kiranka."
Ya ji qirjinsa ya harba sai ya zare ido yana kallonta har na wani lokaci mai tsayi.
Cikin sanyin murya ya tambaya "MD ya dawo ne?"
Na'ila ta gyaxa kai "jiya da daddare aka ce ya dawo yau kafin takwas na safe yana ofis, sau biyu ya aiko a yi kiranka ina cewa kana hanya baka qaraso ba."
Ya mayar da qofar mota ya rufe ya ce "na ji ki koma ofis shikenan."
Na'ila ta gyaxa kai ta juya zata tafi sai ta sake juyowa, ta ce "Oga! Abokinka Alh.Khamis yau zuwansa sau uku ofis yana nemanka."
Ya ji gabansa ya yanke ya faxi da aka ambaci sunan Khamis, ya yi shiru sannan ya gyaxa kai, ya ce "na ji."
Na'ila ta juya zata tafi sai ta sake juyowa, ta ce "Oga! Matar nan da kayiwa alqawari zaka biya mata gidan haya tana nan a qarqashin bishiyar can tana jiranka.
Ya gyaxa kai ya ce "na ji. Ki bata dubu hamsin a cikin kuxin nan."
Ta sake zabura ta ce "yauwa na manta Mr. John ya zo akan maganar nan ta . . . ."
Iziddin ya daka tsawa gami da xaga mata hannu ya dakatar da ita "Ke! Ke Na'ila! Ya isa haka. Ba kya la'akari da yanayin da mutum yake ciki ne? Yau baki lura ba ni da nutsuwa ba ne? Duk ki ce musu suyi haquri ba zan iya ganin kowa ba yau, a saurara min."
Ta duqa tana rawar jiki "Afuwan ranka ya dade. Allah Ya baka haquri." Ta juya da sauri ta nufi ofis. Ya daxe a tsaye yana kallon kayan jikinsa yana tunanin yadda zai je kiran Ogansa kuma surikinsa da yake matuqar jin nauyi da kunya da waxannan kaya, gaba xaya ma kayan nan bai yi kama da shigar aiki ba. Ba zai iya komawa gida ya canja ba ya dawo dan kafin ya dawo MD zai fita daga ofis dan baya wuce qarfe goma sha biyu na rana yake ficewa. In har ya bari ya fice basu haxu ba tabbas akwai matsala, zai yi zaton idan baya qasar wasa da aiki yake yi masa alhali ya yarda da riqon amanarsa.
Iziddin ya fara tafiya cikin nutsuwa kansa a sunkuye a qasa ya nufi ofishin Ogansa kuma sirikinsa tamkar uba yake a wajensa. Yana isa sakatariyar MD mai suna Rabeka ta miqe tsaye dan girmama Manaja Iziddin, ta gaishe shi gami da cewa "Eh Alhaji yana ciki."
Iziddin ya sake nutsuwa yana jan riga har ya shiga ciki a nutse, gami da yin sallama cikin kamilalliyar. Alh. Jibrin ya amsa gami da qurawa iziddin idanuwa har ya qaraso gabansa sannan ya tsugunna ya gaishe shi. Alhaji ya amsa cike da mamaki, ya nunawa Izziddin kujera ya umarce shi day a zauna, sannan ya zauna har yanzu kansa a sunkuye a qasa yake.
Iziddin ya gyara zama ya sosa qeya ya ce "Alhaji an dawo lafiya? Yau ban fito da wuri ba ne . . . ."
Alh. Jibrin ya katse shi " Izziddin lafiyarka qalau kuwa yau? Yaya Nauwara, abokiyar zamanta da yaransu, lafiyarsu qalau?"
Izziddin ya xago da sauri ya dubi Alhaji cikin firgici ya tabbatar tambayar Alhaji tana da alaqa da shiga da yanayin da ya ganshi wanda bai saba ganinsa a ciki ba, sai ya gyaxa kai ya ce "lafiya qalau ranka ya daxe."
Alh. Jibrin ya girgiza kai ya ce "na san halinka da kara da kunya da kawaici ba zaka tava faxa min ba amma bana jin kana jin daxin jikin ka yau, ka koma gida ka kwanta ka huta zuwa kwana biyu, ba damuwa ni da Khamis za mu kula da ma'aikatar. Ina ganin da bana nan kayi aiki da yawa har ka yiwa kanka illa, kasan a koda yaushe ina shawartarka da ka dinga ragewa kanka aikin wahala ko dan sabo da lafiyar ka rashin bacci matsala ne a jikin xan adam."
Izziddin ya ji daxi da hutun da aka bashi sai ya yi murmushi ya duqa ya yi godiya, ya tashi ya fice. A ransa yana mai godiya ga Allah da ya haxa shi da Oga mai ganewa da tausayi. Bai yarda ya bi ta hanyar da jama'a za su ganshi ba sai ya bi ta baya ya sulale ya isa wajen motarsa ya yi wuf ya shige ya fita. Masu gadin a bakin get suna ta jansa da wasa, suka ga alamar yau fa ba dama ne, ya qi biye su daga nan suka yi AMANNA oga babu kanta. Yana tafiya a hanya rabi da rabi hankalinsa ya karkasu kashi-kashi, xinbun damuwar nan ce a danqare a zuciyarsa, farin cikinsa da Ogansa ya fahimce shi, matan sa yake fata yana ta addu'a Allah Ya sa su fahimce shi kada su tayar da hankalinsu a duk yanayin da suka ganshi a ciki.
Wayarsa ce take ta qara (ringing) bai san in da take ba amma daga qarqashin kujera yake jiyo qarar, koma dai waye mai kira sai ya yi haquri sai ya tsaya zai duba, ya san dai kiran nan bai wuce daga gidansa ba ne ba matsala tunda a hanyar gidan yake. Addua'a yake ta yi fal bakinsa bai daina ba har ya dira a farfajiyar gidansa ya ja ya tsaya a kusa da motar Khamis, ya tabbatar Khamis ya biyo shi gida ya ji ko lafiya, kuma babu tantama matansa ne suka shiga damuwa suka dami Khamis da waya shine ya zo. Ya daxe yana hararar motar Khamis sannan ya yunqura ya fito daga tasa motar, ya xaga kujerun motar ya bankaxo wayarsa, daqyar ya ganta. Wayar ta cika, ta bunqasa da missed calls da saqonni abin har ya bashi tsoro. Da yawa daga matansa ne, wasu daga Ogansa sirikinsa Alh. Jibrin, wasu daga Khamis, sai sauran daga lambobin da bai sansu ba ma. Saqonnin kuwa bai wuce na cigiyarsa ba.
'Ina ka shiga? Ina kake yanzu? Mun kasa bacci.'
Dai-dai lokacin wayar tayi haniniya ta kashe kanta saboda caji ya qare, ya mayar da ita cikin aljihu ya rufe motar ya tunkari qofar shiga katafaren falon gidan, sai ya ci karo da Babban xansa Faruk, ya na ganin Abbansa ya daka tsalle ya xane shi yana murna, sannan ya quga da qarfi
"Lah! Ga Abba oyoyo! Ga Abba bai vata ba."
Sai ragowar yaran guda uku Mami, Asim da Baba qarami, su ka falfalo da gudu suka xane shi.
Iziddin ya rungume su sai ya ji hawaye ya cika masa ido, ya qirqiro murmushin qarfin hali, ya ce "lafiya, yau litinin baku je makaranta ba?"
Faruk ya narairaice ido ya ce "Mama ce ta ce mu zauna yau kada mu je makaranta saboda an rasa ka."
Mami ta ce "Su mama tun xazu suke kuka muma muna yi aka ce Abbanmu ya vata.."
Ya girgiza dan takaici ya sa hannu ya shafa kawunansu, ya ce "babu in da na je ni ban vata ba, ku kwantar da hankalinku dan haka kada ku sake yin fashin zuwa makaranta. Idan na mutu fa? Sai ku daina zuwa makaranta?"
Momi ta zabura ta ce "Allah Ya sawaqe ma Abbanmu ba zai mutu ba."
Ya yi dariya ya shigo falon, a jikin wundo ya iske Amatullah da Nauwara suna leqensa, Khamis kuma a zaune a kan kujera ya riqe kai. Tabbas ba qaramin qarfin hali Izziddin ya yi ba da ya iya duban fuskar khamis, har ya miqa masa hannu suka gaisa gami da qirqiro murmushi. Duk wacce ya tunkara a cikin matan sai ta goce tana kuka saboda sun yi fushi das hi. Haqiqa ya haddasa musu vacin rai da fargaba daga jiya zuwa yau. Iziddin ya yi murmushi ya sami kujera ya zauna daga nesa da khamis dan baya so su sake nanuquwa da juna har abada.
Khamis ya harare shi ya ce "haba! Haba Iziddin wanne irin abu ne haka? Abinda baka tava yi ba za ka aikata a yau. Babu in da ka tava shiga baka faxa min ni da matanka ba, ban sanka da haka ba."
Amatullah ta harari mijinta "tun jiya ya qi ya faxa mana ma abinda ya tsare shi da har ya kama shi ya kwana a waje, tunda nake da kai shekaru goma sha biyu baka tava kwana a wani waje ba alhali kana garin baka yi tafiya ba."
Iziddin ya sunkuyar da kai qasa bai yi magana ba.
Nauwara ta sharce hawaye cikin sheshsheqar kuka ta ce "yanzu haka kaina ke ta ciwo ina kyautata zaton jinina ne ya hau."
Iziddin ya yi dariya ya ce " zo in auna in gani ko jinin ne ya hau da gaske."
Haushi ya kama su kowaccensu ta tashi ta shige vangarenta a fusace.
Khamis ya gyara zama ya dubi Iziddin wanda ke kishingixe ya rufe idanuwansa da hannunsa kamar mai gyangyaxi ya ce " ina ka je ka kwana ne?" Iziddin ya yi shiru bai ba shi amsa ba.
Khamis ya sake gyara zama ya duba gabas da yamma kudu da arewa ya tabbatar babu kowa a falon sannnan ya yi Magana cikin raxa "ko neman Zahidah ne ya kai ka da nisa har ka vace hanya?"
Iziddin ya xago da sauri ya dubi Khamis duba na takaici.
Khamis ya yi murmushi ya ce "ka kwantar da hankalinka dan Allah abokina, an riga an tabbatar mana Zahidah tana raye, kuma na faxa na maimaita zaka sha mamaki."
Iziddin ya yi ajiyar zuciya ya maimaita "Mamaki? Wannan wanne mamaki ne da har yanzu ban sha shi ba Khamis? Tun ba yau ba kake faxar haka duk sanda zan xauko maganar Zahidah sai ka faxi wannan Kalmar, har yanzu banga abin mamakin ba kuma. Sai yaushe ne?"
Khamis ya yi murmushi ya ce "ka ci gaba da haquri dai. Amma dan Allah ka daina haka kada ka sake yiwa matanka haka, ka san suna sonka da yawa duk motsin da ka yi suna begenka ba kamar ni ba wanda matata bata damu da ni ba. Akwai Maganata da kai akan gimbiyata sai mun haxu a ofis zamu yi."
Iziddin ya hasala ya dube shi duba na rashin fahimta "wacce gimbiyar?" Khamis ma ya harare shi ya tuntsire da dariya "au baka ma san gimbiyata ba ma zaka ce? Wai kai babban yaya ko? To Izzatunka nake nufi kasan saura kwanaki goma sha biyar ta gama iddah bana son in wuce qarshen wata ba'ayi magana mai qarfi ba."
Iziddin ya mayar da kai ya kwanta bai bashi amsa ba.
Khamis ya miqe tsaye yana murmushi ya ce bari in koma ofis kasan MD ya dawo ko? Kai ma naga alama kwana kayi baka yi barci, ba baka da niyyar fita ma yanzu bari in tafi idan ka kimtsa ka fito. Ka canje ni yau kai ka zama mai gyangyaxi dan har suna ka saka min mai gyangyaxi a ofis."
Takaici ya hana Iziddin ya bashi amsa ya faxa a ransa "tabbas yanzu na gano bakin zaren na gane a club kake kwana shiyasa aiki yake gagararraka da safe."
Iziddin ya miqe tsaye ya miqawa Khamis hannu ya ce "toh na gode sai anjima."
Khamis ya fice da sauri ya yin da Iziddin ya nufi vangarensa yana tafe yana tangaxi kamar zai faxi. Muryar Amatullah ya ji ta ambaci sunansa
"Abban Faruk."
Ya juyo da sauri ya dube ta, ta qaraso in da ya ke, sai ta nuna masa teburin cin abinci ta ce "ba xaki za ka shiga ba abinci za ka ci saboda girkin Nauwara ne jiya ta sha wuyar yi maka girki baka dawo ba, yau da sassafe ta shiga kicin ta haxa maka ba zata ji daxi ba idan baka ci ba."
Ya miqe kai tsaye ya nufi kan tebur ya zauna, Amanatullah ta shiga vangaren Nauwara ta kira ta suka fito tare. Bayan Nauwara ta zuzzuba musu sai suka zauna suka yi bismillah suka fara ci babu abinda suke yi sai kallonsa ci yake kamar baya so, dakyar yake haxiya. Daga ya ajiye cokali sai ya ci karo da guru- gurun idanuwansu sai ya yi sauri ya tura lauma bakinsa, kamar wani yaro qarami. Nauwara ta yi ajiyar zuciya ta ce "me yake damunka ne wai?"
Ya sunkuyar da kai qasa bai amsa mata ba.
Ta sake cewa "a ina ka kwana ka canja kayan jikinka? Ina shaddar da ka fita da ita jiya?"
Ya sake kawar da kai gefe bai amsa mata ba.
Amatullah ta yi ajiyar zuciya ta dubi Nauwara ta ce "Nauwara ki yi shiru mana bakya ganinsa a gajiye aiki ne yayi masa yawa."
Nauwara ta girgiza kai ta zubo da hawaye ta ce " a'a kada ki kare shi, al'adarsa ce faxar gaskiya babu abinda yake voyewa duk sanda kika ga an tambaye shi abu ya qi magana to tabbas abin nan ba mai daxi faxa ba ne, ba zai faxa ba kuma ba zai shirya qarya ba sai ya yi shiru."
Amatullah ta ce "Alhamdu lillah tunda kika fahimci halin mijinki bai tava yi miki qarya ba idan kika tutsiye shi da yawa sai ya fara yi miki qaryar." Nauwara ta fusata ta miqe tsaye ta kama qugu ta harari Amatullah, ta ce"Kina ta kare shi bakya son a faxi laifinsa dan dai ba'a ranar girkinki ba ne ya yi miki haka. Ni ce daman baya so ya tarki qin kwana a gida ranar girkina."
Ta shige xakinta a fusace. Su ka bita da kallo su dukka, Amatullah ta juyo ta dube shi sai ya sunkuyar da kai qasa. Sun xauki lokaci mai tsawo a cikin wannan yanayi.
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "ka je ka kwanta na ga kamar kana jin bacci."
Ya yi zunbur ya miqe tsaye daman a takure yake ya nufi vangarensa yana jan qafa daqyar. Ta bishi da kallo zuciyarta cike da mamaki da damuwa ta rasa abinda zata zarga game da halin da mijinta ya shiga. Sai ta xaga hannayenta sama ta yi addua'a tana fatan Allah Ya sa ba matsala ya samu a wajen aiki ba ko daga danginsa ba.
Iziddin na shiga xaki ya ciro wayarsa ya saka a caji ya cire kayan jikinsa ya jefa a cikin kayan wanki, ya saka rigar bacci, ya kulle qofar xakin, ya kashe fitila sannan ya kunna Ac, ya shiga bargo sai ya runtse ido. Haqiqa daga ya rufe ido Zahidah da Kahamis yak e hange daga ya juya sai ya yi arba da Aljannah.
Ya faxa a bayyane "Khamis! Khamis!! Ni Khamis zai yiwa haka? Tabbas na sani alamomin munafuki shine idan kayi alqawari ka sava, na yi masa alqawarin zan bashi qanwata kwaya xaya kacal a duniya da nake ji da ita Izzatu ya aura ada, amma a yanzu ba zan iya bawa Khamis Izzatu ba, a matsayinsa na mashayi, mazinaci xan barikin da yake kwana a club, maci amana, mayaudari , macuci. Allah Ka sani ada ban san haka yake ba, na yi zaton tsantsar son nan da yake nuna mata a zahiri gaskiya ne, gara da Allah Ka nuna min gaskiya tun ba'ayi nisa ba. Ta ina zan vullowa wannan matsalar? Yanzu haka zan ci gaba da yi masa yaqe ina kallonsa da abin, ya ci gaba da raina min hankali? Kalli yadda ya fara haddasa min matsala a wajen aikina da wajen iyalina. Tabbas ba zan dauwama a cikin wannan hali ba, alhali damuwar dana shiga ba ni kaxai ta shafa ba sai ta shafi matana da 'yayana da wajen aikina."
A haka yake ta surutai shi kaxai tamkar tavavve har bacci ya sure shi. Iyalansa basu gan shi ba har washegari da safe shima sai da Amatullah ta yi da gaske tana bugun qofa sannan ya tashi ya buxe ya fito.
RANAR TALATA 3 GA WATAN 6 2014
Iziddin yana zaune a falo bayan ruwan shayi daya sha cikin qaramin kofi bai iya cin komai ba, Nauwara ta fito ta gaishe shi ba tare das akin fuska ba ta koma xakinta ta rufe. Amatullah ce a zaune a gefensa ta kalle shi ya kalle ta.
Can ya nisa ya ce "ina yaran nan suke? Ina fatan yau sun tafi makaranta ko?"
Ta gyaxa kai ta ce "sun tafi makaranta sun so ku gaisa da safe abu ya fassakara baka buxe qofa ba."
Ya gyaxa kai ya ce "Allah Ya basu sa'ar karatu."
Ta ce "amin. Yau ma ba zaka je ofis ba ne?"
Ya gyaxa kai y ace "sai dai gobe."
Ta yi shiru tana kallonsa ba tare da ta san abinda zata tambaye shi ba kuma ko ta tambaya ma ta san vata bakinta kawai zata yi ba amsa zata samu ba. Ta langwave kai ta ce "Allah ya kai mu goben."
Ya ce "Amin."
Ya ci gaba da kallon talabijin ba tare da yana fahimtar komai ba. A ka jima sai Amatullah ta yunqura zata tashi, gami da cewa "bari in xauko maka wayarka in kawo maka na san yanzu ana ta nemanka a waya kada shirun yayi yawa."
Ya xaga hannu ya dakatar da ita ya ce "ki bar wayar nan kada ki kunna." Ta koma ta zauna jikinta a sanyaye.
Da aka jima ya miqe tsaye ya nufi xaki ya ce "zan kwanta zan fito bayan la'asar kafin yara su tafi islamiyya mu gaisa."
Ta amsa a sanyaye "Allah Ya fito da kai lafiya."
Yana shiga xaki ya kulle kansa, ita kuma ta xora hannu aka ta fashe da kuka.
Bata sake ganin maigidanta ba sai washe gari da sassafe.
RANAR LARABA 4 GA WATAN 6 2014
Iziddin ne ya fito a gaggauce sanye da baqar riga da wando baqi (suit) da alama ya yi shirin tafiya ofis da wayarsa a hannu sai yanzu ya kunna babu abin da wayar take yi sai rugugin shigowar saqonni daban daban. Bai ma tsaya karanta dukka ba, ya dai karanta wasu daga cikinsu masu mahimmancin, da yawan saqonnin daga matansa ne. Amatullah tana yi masa addu'a akan Allah Ya yaye masa matsalar da yake ciki. Yayin da Nauwara take yi masa qorafi akan buris da al'amuransu da yayi, tana harsashen baya sonta yanzu.
Yara ya iske a zazzaune suna karya kumallo suna ganinsa suka zabura da gudu suka rungume shi, bayan sun gaisa ya umarce su da su je su qarasa cin abincinsu su tafi makaranta kada su makara. Ya shiga kicin ya iske Amatullah tana soya kwai, tana ganinsa sai ta yi murmushi, shima yayi mata, ta gaishe shi ya amsa cike da fara'a.
Ya qara da cewa " Ya ke mace ta gari, ga mijinki ya fito zan tafi aiki kamar yadda na yi miki al'qawari jiya."
Su ka qyalqyale da dariya gaba xayansu, ta lumshe ido ta ce "na ji daxi da ganin mai gidana ya warware. Amma sai ka ci abinci zaka fita saboda na manta rabonka da cin abinci. Ga kwanka nan ina soyawa ka jira ni a teburin cin abinci (dining table) zan kawo maka yanzu."
Ya lumshe ido ya yi murmushi ya ce "xan gata ne ni. Bari in ga Nauwara kafin ki fito na san fushi take yi da ni."
Ya fito daga kicin ya haxu da yara sun xauki jakunkunansu zasu tafi mota direba zai kai su makaranta.
Suka haxa baki "Abba, mun tafi makaranta kayi mana addu'a."
Ya yi dariya ya shafa kawunansu ya tofa musu addu'a, suma suka shafa, suna murna suka fice da gudu. Ya wuce kai tsaye xakin Nauwara, a zaune a falonta ya iske ta tana kallon talabijin, wani fim xin Hausa mai kyawun gaske take kallo mai suna 'ADON DAWA'. Da alama tana jin daxin kallon fim xin nan saboda Soyayyar gwarzaye ciki 'Kaltum da Mambela' tana burge ta matuqa, haka ta so ita da Iziddin su kasance da ace babu kishiya. Tana ganinsa sai ta cukuikuye fuska ta takure, ya kalle ta ya yi dariya ya zauna a kusa da ita,sannan ya gaishe ta, bata amsa ba ta kawar da kai gefe.
Ya ce "bari in durqusa qasa in gaishe ki tunda kin qi gaishe ni kuma na gaishe ki kin qi amsawa. Na lura kina fushi da ni alhali ba akan haqqina ba, ban yi miki laifi ba baki yi min laifi ba. Dan Allah ki dinga lura da yanayi, a rayuwa ba kullum ake dauwama a cikin farin ciki ba, ni xan adam ne zan iya samun canjin yanayi. Kiyi koyi da yayarki Amatullah, ta damu ita ma amma ta yi min uziri. Jiya girkinta ne ban ci abincinta ba haka tun da safe bata ganni ba sai yau." Ta turo baki ta ce "na ji."
Ya kalle ta ya yi dariya ya ce "amsar da za ki ba ni kenan, ba zaki yi min xan murmushin nan naki ba?"
Sai suka qyalqyale da dariya gaba xayansu.
Ya ce "ko ke fa? Zo mu je mu ci abinci zan wuce ofis kada in makara."
Ta miqe tsaye sai ta langwave kai ta ce " My dear, ina so in faxa maka daman da yamma zan je bikin ranar zagayowar haihuwar (birthday party) aminyata Laurat, wanda za'ayi a wajen wasa na Wanderland da yamma, na san zaka ce kada in tafi da yara saboda islamiyya ni da Yaya Amatullah za mu je mu dawo kafin magriba . . ."
Kafin ta rufe baki ya xaga hannu ya dakatar da ita, nan da nan alamar damuwa ta bayyana a fuskarsa.
Ya girgiza kai ya ce "kiyi haquri ba za ki je ba, bayan haka ina mai baki umarni ki rabu da Laurat bana son qawancenku da Allah, na tabbatar za kiyi mamaki da jin haka saboda Laurat qawarki ce kuma makwabciyarki ce tun yarinta hark u ka girma tare, kamar yadda na ke da Khamis amma ki tuna ke matar aure ce Laurat kuma bata da aure, rayuwarki daban tat a daban."
Ta na tsaye a sanqare tana yi masa duba irin na rashin fahimta ba tare da ta san amsa da zata bashi ba. Ya gama maganarsa ya fice ko waiwayenta bai yi ba. Ya isa kan tebur ya iske Amatullah a zaune tana jiransu. Ta ganshi shi kaxai kuma kamar ransa a vace yake, ba kamar yadda ya shiga xakin Nauwara ba.
Ta tambaye shi "ina Nauwara ka fito kai kaxai?"
Ya amsa mata "tana ciki, ina jin tana zuwa, ko ki shiga ki fito da ita." Ya fara shan shayin da ya iske ta haxa masa. Amatullah dai ta lura akwai wata matsala a tsakaninsu sai ta yi wuf ta miqe ta nufi xakin Nauwara, ta iske ta a zaune ta yi tagumi a falo. Amatullah ta zauna a kusa da ita bayan sun gaisa ta tambaye ta ko lafiya taga kamar ita da Maigida ransu a vace? Nauwara ta fara hawaye tana bawa abokiyar zamanta labarin yadda suka yi da maigida, sai gaba xayansu suka zuba tagumi suna tunanin abinda yake damun maigidansu kwana biyu ya canja halayyarsa.
Amatullah ta jawo hannunta ta ce "yi haquri zo mu je mu ci abincin tare da shi kada ya zaci mun ware shi yana cikin damuwa za mu qara masa damuwa."
Suna fitowa suka ga wayam baya nan, da Amatullah ta leqa wajen motarsa ta iske bata nan ya shiga mota ya tafi abinsa.
Bai bar ofis ba sai da yamma sai a lokacin suka haxu da Khamis a bakin motocinsu, bayan sun gaisa Khamis ya nemi da su yi hira Iziddin ya nuna zai koma gida sauri yake yi kada matansa su yi fushi.
Su ka yi sallama Khamis ya shiga mota shima Izidin ya shiga tasa motar amma fa ba gida su dukka suka nufa ba Wuse zone 6 suka nufa gidan Zahidah. Iziddin yana biye da khamis a baya ba tare day a sani ba, har bakin get xin gidan Iziddin ya tabbatar ciki khamis ya shiga sannan ya juya da baya. Zuciyarsa tana tafasa tana rugugin zafi ya nufi gidansa, daman babu zancen walwala a fuskar sa balle yayi hira da iyalansa haka babu maganar cin abinci balle ya yi kallo tare da iyalai. Yana shiga ya iske sun cava ado Amatullah mai girki ta yi dafe-dafe kala-kala ya basu haquri ya shige xaki ya kulle kansa. Ji yake tamkar ya haxiyi zuciya ya mutu.
Yana zaune a gefen gadonsa Khamis ya kira shi, ya yi kamar ba zai xauka ba dai ya daure ya xauka yana sauraron rainin hankalin da zai yi masa. Khamis ya gaishe shi yana ta fara'a kai kace an yi masa albishir da aljanna. Shi kuwa takaici ne yake nuqurqusarsa yana sauraren ya ji abinda zai faxa masa.
Khamis ya ce "kana gida ne?"
Iziddin ya tabbatar a hand's free ya saka shi, su Zahidah na wajen.
Iziddin ya nisa ya ce "kwarai ina gida. Ya aka yin e?"
Khamis ya ce "no, ba wani abu nima na iso gida ne."
Iziddin ya tave baki ya ce "a miqa gaisuwata zuwa ga madam da yara."
Khamis ya ce "suna jin ka ma"
Iziddin ya ce "ok bawa Sahiba waya mu gaisa."
Khamis ya zabura ya ce "Hallo bana jin ka, me kace?"
Iziddin ya maimaita cikin Gadara "Ina so in yi magana da Sahiba matarka ka bata waya."
Khamis ya ce "yauwa yanzu ina jin ka, gata nan."
Abin mamaki sai ga muryar Sahiba ta karvi waya, suka gaisa har ta bawa takwaransa Iziddin junior suka gaisa sannan suka kashe waya. Abin ya yi ta bawa Iziddin mamaki yadda Khamis har ya fito daga Wuse ya wuce unguwarsu Gwarumfa yanzu-yanzun, duk da go slow yamman nan. Bai fito daga xaki ba sai washe gari da sassafe ya yi shirin fita ofis.
RANAR ALHAMIS 5 GA WATAN 6 2014
Iziddin ya fito ya iske yaransa sun gama karin kumallo zasu tafi makaranta ya yi musu addu'a suka fice, ya iske matansa gaba xaya suna xakunansu basu fito falo ba sai masu aikinsa guda biyu Anna da Hauwa'u. Bayan sun gaishe shi ya tambaye su ko ina matansa? Su ka shaida masa kowacce na xakinta. Ya nufi xakin uwar gidansa Amatullah, ya iske ta a falo a kwance akan kujera tana ganinsa ta tashi zaune kallo xaya ya yi mata ya san bata cikin walwala, ya tsaya akanta yana kallonta cike da murmushi itama ta daure ta qirkiro murmushin qarfin hali ta sakar masa, sannan ta duqa ta gaishe shi. Ya amsa gami da yi mata sallama zai fita aiki. Ta yi masa addu'a Allah ya dawo da shi lafiya, ya ga alamar bata da niyyar yi masa rakiya shima kuma daman baya buqata. Ya fice ya nufi xakin Nauwara, akan gado ya iske ta a kwance ya daxe a tsaye akanta, ta rufe ido ta qi buxewa kamar mai bacci alhali ya fahimci idanuwanta biyu sai ya fice ba tare daya ce komai ba, ya nufi qofar fita. Zai shiga mota kenan ya hangi Nauwara tana leqensa ta jikin wundon xakinta, da ta tabbatar ya ganta sai ta saki labule da sauri, ya yi murmushi ya shiga mota ya wuce.
Yana tafiya akan hanya ne ya ji wayarsa ta yi qara, ya duba lambar bai san lambar ba abinda ya qara bashi mamaki shine day a ga a xaya layin (sim) aka kira shi layin dab a kowa ya san shi das hi ba, dan haka bai xauka ba. Amma da aka ci gaba da kira ba qaqqautawa sai ya sa hannu ya xauka, ya yi shiru yana saurarar abinda ake cewa. Muryar mace ce bai gane mai muryar ba amma ya fahimta daga baya da ya ji in da maganar ta nufa, bayan ta gaishe shine ta gabatar da kanta
Ta ce "sunanta Aljannah."
Sai ya ji gabansa ya yanke ya faxi, ya yi ajiyar zuciya yana magana a daqile kamar baya so.
Ya ce "kina nan lafiya?"
Ta yi murmushi ta ce "Lafiyata qalau. Ina ta kiran wayarka a kashe wataran kuma tana shiga amma baka xauka, sai yau na samu Anti Zahidah ta fita ta bar wayarta na sata na kira ka."
Ya yi sauri ya cire wayar daga jikin kunnensa ya duba lambar duba na tsanaki nan da nan ya haddace lambobin, sannan ya mayar da wayar kunnensa ya ci gaba da sauraron Aljannah.
Ta ce "na kira in yi maka godiya akan kyautar kuxin da ka yi min, da kuxin nake cin abinci, na sayi makilin, toilet paper, auduga sannan na sayi . . . ." Sai ya katse ta ya ce "kuxin ya qare ne?"
Ta girgiza kai ta ce "da saura da yawa ma."
Ya ce "toh ba matsala. Kin ji faxan da na yi miki ko? Ki tsare kanki."
Ta gyaxa kai ta ce "ina tsare kaina."
Ya ce "kin faxawa Zahidah za ki kira wani da lambarta net a baki izini?" Ta girgiza kai ta ce "bata sani ba, bata gida da sassafe ta shiga mota ta fita ina jin ta je gidan motsa jiki ne."
Ya ce "ki goge lambata, amma ki faxa mata kin yi amfani da wayarta ta yafe miki, rashin gaskiya bashi da daxi."
Ta ce "zan faxa mata insha Allah. Yaushe za ka zo club?"
Ya yi shiru can ya ce "kullum sai kun je ne?"
Ta gyaxa kai ta ce "eh, jiya ma mun je."
Ya nisa ya ce ke da wa da wa?"
Ta ce da "Anti Zahidah da Uncle Khamis."
Ya cije leve dan takaici ya ce "na ji, amma bana so ki bawa kowa labarina ko lambata. Sai anjima."
Ya kashe waya zuciyarsa tana tafasa, har sai da ya ja burki ya tsaya a gefen hanya ya huta saboda hankalinsa yana qoqarin gushewa. Daya da taimakon Allah ya yi ta addu'a har ya samu ya xan nutsu sannan ya ci gaba da tafiya. Ya isa ofis a makare gashi za'ayi taro (meeting) shine jagoran taron. Yana shiga da Khamis ya fara yin arba sai ya ji ransa ya qara vaci. A daddafe ya gudanar da taron, manyan abubuwan daya kamata ya tatttauna ba iya yi ba, sai kame-kame yana ta xauki burutsu, aka rasa kansa. Tabbas kowa ya lura Iziddin na da matsala musamman surikinsa Alh. Jibrin wanda ya yi amanna da nutsuwarsa da qwazon aikinsa amma yanzu duk ya susuce.
Bayan kowa ya koma ofis aka ci gaba da aiki sai daf da magaruba suka tashi, a bakin baranda suka haxu da Khamis, ya shaidawa Iziddin yau motarsa na wajen gyara yana so su tafi tare.
"Babu matsala mu tafi." Iziddin ya faxa a lokacin da yake qirqiro murmushin dole gami da miqawa Khamis mukullin motar suka xinguma suka tafi. Khamis ke tuqawa, suna tafe suna hira rai-rai-rai-rai kamar da, amma fa ba qaramin qarfin hali Iziddin yake yi ba da har yake kula shi haka saboda haushinsa kawai yake ji, musamman idan yayi masa maganar Izzatu qanwarsa. Wayar Khamis ce ta xauki ruri tana ajiye a gaban mota, gashi sun iso daf da 'yansanda ba damar ya amsa waya yana tuqi, hankalin Khamis ya tashi da yaga Iziddin ya saka hannu ya xauko wayar ya karanta sunan mai kira.
'Sahibata 2 . . .' Iziddin ya karanta sunan a bayyane.
Kafin ya qarasa Khamis ya zabura ya zare ido ya ce "Sahiba 1 ko 2 aka rubuta?"
Iziddin ya ce "Sahiban naka har guda nawa ne? Ai na zaci dukka lambobin madam ne? Ko ka haxawa Izzatu waya ne ban sani ba?"
Daidai lokacin wayar ta gama ruri ta katse, sai Khamis ya yi ajiyar zuciyar jin daxi ya lumshe ido ya yi dariya, ya ce "ai ka hana ni yin magana da Izzatu ka ce babu kyau sai ta gama idda. Lambobin madam ne dukka biyun."
Iziddin ya yi dariya ya ce "ka ce mata nace waxanne irin jama'a ce da ita haka suka yi mata yawa har ta sayi layika biyu na waya....."
Bai rufe bakinsa ba wayar ta sake ruri Khamis ya shixe a zabure ya juyo ya kalli Iziddin ya ce "Sahiba ce?"
Iziddin ya ce "Sahiba 1 ce yanzu ta kira da xaya layin, bari in amsa." Khamis ya ja dogon numfashi ya ce "amsa ka ce mata ina hanyar gida."
Iziddin ya danna sai bai yi magana ba, yana sauraronta.
Sahiba kuka take yi haiqam ta ce "Khamis, na lura gaba xaya ka canja halinka, ka daina kwana a gida, ka daina kula da ni, balle yaranka. Idan ka gaji da ni ka sallame ni in koma gidanmu."
Hankalin Iziddin ya tashi da alama annurin fuskarsa ya kauce sai Khamis ya ruxe ya fara magana cikin gigita "me ta ce? Me take cewa ne? Ba ni wayar in ji."
Iziddin ya yi murmushi ya ce da shi "bar ni da ita. Sahiba ya yara? Na ce Khamis ya faxa miki kin zama gwamnan banki ne wanda yake da layukan waya daban daban . . .?"
Bai rufe bakinsa ba Khamis ya warci wayar ya ce "Sahibata gani nan zuwa gida yanzu. Me kika dafa mana ne?"
Iziddin yana jiyo kukanta shi kuma Khamis yana ta dariya wai shi a dole hirar nishaxi suke yi. Ta kashe waya Khamis ya mayar da wayar gaban mota ya ajiye, kafin wani daga cikinsu ya sake yin magana wayar ta sake xaukar qara. Gaba xayansu suka kai hannu zasu xauka sai Iziddin ya riga shi xauka Sahiba 2 ce ta kira haqiqa yau Sahiba ta za'ala faxa ta ke nema.
Sai Iziddin yayi murmushi ya miqawa Khamis waya gami da cewa "Sahiba ce kuma ta kira da xaya layin, bata gaji da jin muryarka ba."
Khamis ya karvi wayar hannunsa yana rawa ya danna sai ya shiga magana cikin raxa da gigita. "Ga ni nan akan hanya minti biyar zan kawo miki."
Khamis ya kashe waya ya juyo ya kalli Iziddin yayi murmushi ya ce "ka yi haquri da Allah zan miqawa Sahiba kuxi a wani saloon a maitama."
Sai Iziddin ya sake tambayar abinda yake nufi cikin rashin fahimta, Khamis ya shaida masa matarsa Sahiba tana wajen gyaran gashi (Saloon) a unguwar Maitama zai kai mata kuxin man shamfo.
Iziddin ya yi shiru yana tunani sai can ya gyaxa kai ya ce "ba damuwa mu kai mata."
Babu abin da Iziddin yake sai wasi-wasi a zuciyarsa abin tamabaya anan shine "Shin ba yanzu suka yi waya da Sahibar ba tana kuka tana gida ta ce zata haxa kayanta ta tafi ba? Ko ba ita ba ce yanzu yake ce mata gashi nan zuwa gidan yana fatan ta yi masa abinci mai daxi? Wanne irin saloon Sahiba zata fito daga Gwarumfa ta tafi Maitama ita da bata san gari ba kuma bata da mota? Tabbas Khamis qarya yake wannan ba Sahibarsa ba ce, ya saka Sahiba 2. Amma yau sai gano gaskiyar, a yanzun kuwa."
Suka isa wani katafaren Saloon na 'yayan attajirai da matansu sai kin kai kin kawo ma zaki iya biyan kuxin da ake caji.
Jikin Khamis yana rawa ya tsaya daga nesa da Saloon xin ya juyo ya dubi Iziddin ya ce "bari in shiga in kai mata kuxin da zata biya, ka san Saloon xin mata ne ba zasu so mu shiga ba mu maza shiyasa ma na tsaya daga nesa."
Iziddin ya ce "toh, mu jira a gama mata mana sai mu xauke ta tunda ga dare zai yi, ita ba motar dawowa gare ta ba, ga motarka ta vaci."
Khamis ya zabura yana rawar jiki ya ce " a a kada in vata maka lokaci rayukan matanka ya vaci ai ni yanzu tsoron Nauwara nake ji gani take ni nake janka yawo gara in kai ka gida in damqa ka a hannunsu in ya so in fito da motar in dawo in xauke ta bayan magriba."
Iziddin ya yi murmushin qarfin hali, ya ce "ba damuwa shiga ka fito." Khamis ya fice da sauri yana laluba aljihu, bandir xin kuxi ne a aljihunsa naira dubu hamsin haka ya shiga ciki har a garin sauri wayarsa ta faxo daga kan cinyarsa bai lura ba Iziddin na kallonsa, sai da ya shige Iziddin ya fito ya xauki wayar. Abin da ya fara buxewa a jikin wayar sunan Sahiba 2 ya buxo lambar yana ganin lambar ya shaida lambar Zahidah ce wacce Aljannah ta tava kiransa da ita daman ya haddace. Saboda sanyin da qafarsa ta yi sai da ya kusa faxuwa qasa, ya yi sauri ya riqe jikin mota. Ya zagaya ya koma ya zauna a mazauninsa ya ajiyewa Khamis wayar a gaban mota sannan ya qurawa wata dalleliyar mota ido a bakin saloon xin, ko tantama babu motar Zahidah ce dan lambar motar ma sunanta ne 'HIDAH 3' aka rubuta.
Karewa ma sai ga Aljannah ta fito daga Saloon xin an aiko ta ta xauko wani abu a cikin motar, ta matsa mukulli ta buxe, ta xauko wata leda sannan ta mayar da qofar ta rufe. Iziddin ya fito daga mota da sauri ya tunkaro Aljanna yana yi mata xan kira. "Ke yarinya zo in tambaye ki."
Ta xaga ido a tsorace ta dube shi bata shaida shi ba sai ta xauke kai ta gaggauta runtumawa cikin shagon da sauri, sai abin ya bashi mamaki amma sai ya tuna ashe ba da wannan suffar ta san shi ba da suffar 'yan caburos ta san shi, dan haka sai ya daina mamaki. Yana zaune a mota har yanzu dai khamis shiru sai da ya jima sosai ya fito da sauri xauke da wannan ledar da Aljanna ta xauko a mota.
Ya shigo a gigice yana laluba aljihu yana neman wayarsa sai gata a ajiye a gaban mota, ya yi ajiyar zuciya ya kalli Iziddin ya yi dariya ya ce "kaina fa ya xauki zafi ina ciki in ta neman waya ashe ma na barta a nan a ajiye."
Iziddin ya yi murmushin qarfin hali ya ce "sai a hankali abubuwan ne da yawa."
Khamis ya wurga leda a kujerun baya ya ce "kayanta ta bani in kai mata gida wai gara ta dawo a motar haya."
Iziddin ya tave baki ya kalle shi da gefen ido ya yi shiru yana mamakin yadda Khamis ya zama mashahurin maqaryaci kuma mayaudari, dan ada bai tava sanin ashe haka yake ba.
Su ka ci gaba da tafiya Khamis yana ta zuba masa qarya shi kuma yana sauraronsa dan shi a yanzu babu abinda Khamis zai faxa a duniya da zai yarda da shi.
Su ka isa cikin farfajiyar gidan Iziddin, ya juya ya kalli Khamis ya ce " ba damuwa ka tafi da motar ina ganin babu abinda zan xauka a cikin motar sai wayata da gilashina, ka yi ta hawa ni zan dinga hawar xayar har a gyara maka taka."
Khamis ya ji daxi ya ce "kai mai Motoci da yawa ga ta yara, ga ta Nauwara, ga ta Amatullah."
Iziddin ya ce "ka san ni bana hawan motar mata sai dole, zan yi amfani da Babbar ba damuwa dan dai ban cika hawanta ba ne a yawan gari sai idan za'ayi wani babbabn taro."
Su ka yi sallama ya shiga gida Khamis ya fice da sauri, Ya iske matansa da 'ya'yansa a zaune a falo, bayan sun yi sallar magaruba da isha'i jam'i ya yi qarfin hali ya zauna a cikinsu ya ci abinci ya tava yar hira zuwa qarfe tara na dare. Girkin Nauwara ne, ya sake neman alfarma a barshi yau ma baya son kowa a kusa da shi. Ya tabbata ta qufula amma babu yadda ya iya akwai abubuwan da yake so ya bincika a cikin dare. Ya shiga xaki ya kulle kansa, yana yin wanka sai ya xauko lambar Khamis ya danna, tana ta ruri bai xauka ba, sai ya kira matarsa Sahiba yana kira ta xauka cikin kuka take magana.
"Ina Khamis xin ?" Iziddin ya tambaya a gigice
Ta sharce hawaye ta ce "rabonsa da gidan nan tun jiya da safe. Ba xazu kuna tare ba ya ce min gashi nan zuwa, toh bai zo ba. Motarsa ma tana wajen 'yan sanda sun kama ta a garin yawon dare. Ya zama xan bariki 'yanmata kala-kala yake bi. Na so in faxa maka tuntuni na fasa kai ma kuma na san ba zaka bi baya na ba saboda na ji an ce qanwarka Izzatu tsohuwar budurwarsa zai aura dan haka ba zaka bi bayana ba."
Izziddin ya yi shiru ya kasa magana har zuwa wani lokaci saboda wasan kurar da takaici yake yi masa da zuciya.
Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Sahiba! Ki yi min alqawari zaki kwantar da hankalinki, ki daina vata hawayenki kina kuka kwata-kwata akan Khamis, kada ki sake ki faxawa kowa irin wannan maganar daga ni da kika faxawa yau. Ko Khamis xin kada ki nuna masa kin damu. Kada ki faxawa iyayensa balle iyayenki, kada ki faxawa qawayenki su Amatullah. Ki bar komai a hannuna zan yi maganin abin in sha Allah. Ki xauke ni kamar yadda kika xauke ni ada xan uwa kuma yayanki, ki kawar da maganar Izzatu qanwata a gefe ke ma qanwata ce. Duk abinda kike buqata a duniya na kuxi ke da yaranki ki tambaye shi idan bai yi miki ba ki tambaye ni zan baki dai-dai gwargwado yadda ba zai gane ba. Zan nemo bakin zaren, matsalar nan ba zata daxe ba in sha Allah. Kin ji ko?"
Hankalinta sai ya xan kwanta, ta gyaxa kai ta yi godiya suka kashe waya.
Huci kawai yake yi kamar wani kasa haka ya kwana a zaune bacci ya gagari kwayar idanuwansa daga gani babu tambaya yana can a club shi da Zahida suna barikanci. Ya ci sa'a daren juma'a ne sai ya tashi ya yi alwalla ya dinga jero Salloli yana kai kukansa wajen mai dukka Sarkin sarakuna Allah.
RANAR JUMA'A 6 GA WATAN 6 2014
Iziddin bai samu ya yi bacci ba sai da asubah bayan ya idar da sallah ya miqe akan sallaya ya dinga bacci, bai tashi farkawa ba sai da rana, xansa Faruk ya dage yana ta buga masa qofa yana faxin "Abba ka tashi mu je masallaci yau juma'a an kusa tayar da sallah."
Ya yi furgit ya tashi ya buxe qofa ya dubi Faruk a gigice ya ce " qarfe nawa yanzu?"
Faruk ya ce "qarfe xaya da rabi tun xazu ake tafiya masallaci."
Iziddin ya sake murtsike ido ya zabura ya ce "ku je ku fara yin gaba ku da da direba, zan yi wanka in biyo ku."
Faruk ya ce " Abba ban ga motarka ba sai da mama da Umma kaxai, Umma ta ce kana ciki da mun xauka kana ofis."
Iziddin ya yi murmushi ya ce "yau ban fita ba ina hutawa."
Iziddin ya na shiga xaki ya wuce banxaki ya yi wanka, fitowarsa ke da wuya sai ya firgita ganin mace a zaune a gefen gadonsa tana riqe da wayarsa tana bincikawa, suna haxa ido ya ga Nauwara ce sai ya yi ajiyar zucya.
Ya ce "har kin ba ni tsoro ban yi tunanin zan fito in iske mutum a xakin ba, kinga na makara ku kuma ba ku tashe ni ba har na kusa na rasa sallah."
Ta tsuke fuska ta kawar da kai gefe bata bashi amsa ba.
Ya kalle ta yayi dariya ya ce "wayata ake tuhuma kuma, me ake zargi?" Ta tave baki ta ce "ada ba na vata lokacin bincikarka saboda komai na tambaye ka kana faxa min gaskiya amma yanzu ka fara bani tsoro, ka canja hali kai kaxai ka san qungiyar da ka shiga, gashi yau ma motarka bata kwana a gida ba. Ban san abinda yake faruwa ba."
Sai ta fashe da kuka.
Ya yi shiru yana kallonta ba tare da ya san amsar da zai bata ba, can ya nisa ya ce "bari in dawo daga masallaci zan zo mu zauna mu yi magana da ku sosai. Kiyi haquri dan Allah, duk yadda kike zargi bah aka ban e wallahi."
Ta gyaxa kai ta tashi ta fita a fusace ta koma xakinta, ya fito tsaf a cikin fararen kayansa waxanda suka yi matuqar yi masa kyau, ya xora baqar hula da baqin takalmi. Kai tsaye ya nufi qofar fita, sai ya ci karo da Amatullah tana tsaye cikin damuwa. Ta gaishe shi ya amsa gami da yi mata bayani zai je masallaci idan ya dawo yana da magana da su ita da Nauwara. Ta ji daxi da bayanansa sai ta yi masa addu'a Allah ya dawo dashi lafiya, ya fita a cikin dalleliyar motarsa. Ya ci sa'a ya sami sallah da aka idar da Sallah sai ya zarce gidan Zahidah. Yau ya qudiri aniyar yiwa Khamis kamun kazar kuku, yau sai ya kasa, ya tsare, ya raka, sai ya ga abinda ya turewa buzu naxi. Saboda Khamis ya gama cika masa ciki, matsalar da ya haddasa masa zata iya rugurguza rayuwarsa da ta iyalinsa gaba xaya, haka shima kansa Khamis xin ta tava nasa iyalinsa. Gara ayi ta qare kawai, 'ayi wacce za'ayi' wai vera ya zubar da garin mage.
Daga bayan gidan ya sami lungu ya ajiye motarsa dan kada ma Khamis ya hango motar ya gudu, ya tukaro farfajiyar gidan kai tsaye yana tafe yana waiwaye ko zai hango Khamis ya ritsa shi. Ya qaraso bakin barandar gidan anan ya iske dandazon almajirai da robobinsu sun jera a layi, Aljanna da wata mata tsohuwa da alama mai aiki ce sun yi kaca-kaca da manja suna rabon abinci. Ta qura masa ido tana yi masa kallon sani, ya wuce su kai tsaye ya afka cikin falon. Ya ci sa'a ya iske Zahidah ta baje a falo ta miqe qafa akan kafet, ta baza benelyn kwalba-kwalba, ta xaga xaya tana korawa sai ta ga Iziddin a tsaye akanta ko sallama bai yi bay a faxa, saboda firgici bata san sanda ta yi wurgi da kwalbar ba ta faxo qasa ta fashe, yayin da wanda ta zuqa a bakinta ya kwaranyo jikin rigarta, ta daka tsalle ta yi juyi sai gata a lave a bayan kujera.
Ya sami kujera ya zauna ya zubawa kujerar data vuya a bayanta ido ba tare da ya ce uffan ba. Su ka daxe a cikin wannan hali sannan Aljaannah ta shigo xauke da flask xin abinci. Ta duqa ta gaida Iziddin, bai amsa mata ba ya kawar da kai gefe ta razana da ganin Ogarta a lave a lungu.
Ta tambaye ta a gigice "Anti lafiya?"
Ta yi mata tsawa "ban sani ba, li je ki xauko min mayafina a xaki, ki taho min da wayata."
Aljannah ta shiga xaki da gudu a gigice ta xauko mata mayafi da waya ta miqa mata, Zahidah ta yafa mayafin akan 'yar shimi da gajeren wandon da yake jikinta sannan ta iya miqewa tsaye, tana daddanna waya da alama saqo take turawa Khamis ta ce kada ya shigo gidan nan yau.
Iziddin ya fahimci haka kuma haka xinne ma a zahiri ta rubutawa Khamis saqon ta tura sannan ta ja gefe ta kama qugu ta tsaya, aka shiga wurgawa juna harara ita da Iziddin yayin da Aljannah ta yi ta kanta bayan data fahimci faxan nan na manya ne. Iziddin ya miqe tsaye ya jawo wata leda ya kwashe kwalaben benalyn da ledojin kwayar ya zuba ya fice da su. Ta ji tamkar ta kurma ihu saboda zunzurutun asarar da ya yi mata bayan wahalar data sha kafin ta mallake su.
Ya iske Aljanna akan baranda ta miqe qafa tana lomar wake da shikafa da manja da yaji. Tana ganinsa sai ta langwashe qafa ta takure ta sunkuyar da kai qasa bata yarda sun haxa ido ba. Bata gane shi ba kwata-kwata ta ga dai kamar ta tava ganinsa, ta shaida waxannan idanuwansa nasa na harara, sai can ta tuna wannan mutumin ne marar mutunci da ya hana ta sadakar kuxi sanda ta ke jin yunwa zata ci abinci, har ya faxa mata baqar magana ya ce shege yana da uwa da dangin uwa ai. Amma Allah ya haxa ta da wani club xan bariki wanda ya fi shi imani. Ta bi shi da harara ita ma dan ta fuskanci bashi da mutunci balle tausayi, abinda kaga Zahidah na tsoronsa to ka guje shi bala'in ya yi bala'i tabbas. Ya sake waiwayowa ya dubi Aljannah ya ga kallonsa take yi har yanzu sai ya juyo gaba xayansa, ta zaci dawowa zai yi wajenta sai ta xauki kwanon abincin ta miqe tsaye da sauri tana shirin ta arta da gudu cikin gida, sai ya yi murmushi ya juya ya tafi.
Ya daxe a zaune a cikin motarsa yana hangen gidan ko zai ga giftawar Khamis bai ga Khamis ba. Ya lura la'asar ta jima da yi bai yi sallah ba, sai ya ja mota ya nufi central mosque a hanya ya sami bola ya watsar da kayan mayen nan, sannan ya qarasa masallacin a inda ya yi sallar La'asar, ya zauna a cikin masallaci ya jira magrib da isha'ai. Yana ta addu'a Allah Ya shiryi aminansa sannan Ya yaye masa damuwa.
Kafin ya isa gida sha xayan dare ta dade da gotawa sai a lokacin ya tuna alqawarin day a yiwa matansa na zai zo ya zauna da su ya yi musu bayani dan haka sai ya qara gaggauta isa gida da wuri, sai dai kash bai iske kowacce mata a falo ba duk sun kwanta dan haka sai ya wuce cikin xakinsa kawai. Ruwan shayi da biskit ya ci dan ya ga alamar yunwa ta fara yi masa illa har jiri yake yi kamar zai faxi. A kan doguwar kujerar falonsa ya kishingixe ya yi barci mai kama da ido biyu dan bai san in da hayyacinsa ya tafi ba gashi kuma ba barcin yake yi ba.
RANAR ASABAR 7 GA WATAN 6 2014
Da yake ya san asabar ce babu aiki sai da gari ya waye sannan ya koma kan gado ya sami barci mai qarfi, bai tashi farkawa ba sai da azahar. Ya na tashi ya faxa wanka ya xauro alwalla ya fito ya saka wata farar jallabiyya ya yi sallah yana ta fargabar fitowa ya haxa ido da iyalansa, ya san ya yi musu alqawari jiya bai cika ba, duk da dai ba laifinsa ba ne ya dawo ya iske sun yi barci.
Ya fito ya iske su dukka a zaune a babban falo daga dukkan alamu maganarsa suke yi dan ya jiyo suna ambatar sunansa suna ganinsa suka yi shiru kowacce babu walwala a fuskarta. Ya yi sallama, suka amsa ya sami kujera ya zauna bayan sun gaishe shi sai ya shiga bayanai.
Ya ce "ku yi haquri jiya na yi muku alqawarin zan dawo daga masallaci mu zauna a tattauna Allah cikin ikonSa na sha'afa na faxa wata hidimar sanda na dawo gida kuma kun yi bacci."
Sai ya ga gaba xayansu sun yi tagumi sun zuba masa ido suna kallon bakinsa, babu wacce ta tanka masa. Ya gyara zama ya yi ajiyar zuciya y ace "tabbas na san ba za ku ji daxin canje-canjen yanayi da na samu ba, gaba xaya ma ba wata matsala ba ce ta a zo a gani amma ina roqonku da ku ci gaba da yi min uzuri, kwanan nan in sha Allah, komai ya kusa zuwa qarshe."
Su ka amsa masa da "Allah Ya sa."
Ya ce " amin. Ina yaran nan suke?"
Amatullah ta ce "sun tafi islamiyya tun safe yau suna yin tahafiz."
Ya gyaxa kai ya ce "haka ne fa. Na manta a can suke yi ni har yamma. Allah Ya basu sa'ar karatun mai albarka."
Su ka haxa baki "amin."
Ya umarci Nauwara mai girki ta zubo masa abinci kaxan zai ci. Fried rice ta dafa da 'pepper chicken' ta kawo masa ta haxo da ruwa da lemo, ya ce ba zai sha lemo ba ruwan kawai za ta bashi. Yana ci kamar baya so da alama baya jin daxin komai a duniya. Nauwara da Amatullah su ka dinga haxa ido a jonansu suna qifce tabbas sun qara gasgatawa Iziddin bashi da nutsuwa yana cikin wata masifa ba qarama ba. Wayarsa ce ta xauki ruri, sai ya zabura ya jawo wayar ya duba, lambar Zahidah ce ya tabbata Aljanna ce dan haka sai da suka lura da alamar rashin sakin jiki a lokacin da zai xauki wayar. Nan fa ka ga Nauwara ta zazzare ido tana kallo jira take ta ji abinda ba daidai ba ta tubure daman qiris ta ke jira. Babu yadda ya iya dole ya xauka ya san in bai xauka ba, Aljanna zata ci gaba da kira matansa kuwa suna da hujjar su zarge shi da rashin gaskiya.
Cikin muryar kuka Aljanna ta ke magana ta ce "kawu dan Allah yau mu haxu a club ina da magana da kai, ka taimake ni rayuwata tana cikin haxari."
Sai ya ji gabansa ya yanke ya faxi, ya zabura ya ajiye plate xin abincin da yake ci ya kalli hararar da suke wurgo masa tabbas sun jiyo zaqin muryar mai magana mace ce. Sai ya koma ya zauna sosai ya ci fara voye damuwarsa amma fa cikin zuciyarsa dukan uku-uku take yi.
Ya faxa a fusace "wai mai yake faruwa ne?"
Kuka ya ci qarfinta har baya gane abinda take faxa. Ya kashe wayar ya xaga ido ya dube su haqiqa baya tunanin zasu yarda da duk abinda zai faxa musu, ya yi kamar zai yi magana sai ya fasa magana.
Nauwara ta tambaya a fusace "da wa na ji kana waya?"
Ya yi ajiyar zuciya yace "wata marainiya ce take neman taimako." Nauwara ta tave baki ta ce "marainiyar jaririya ce?"
Ya girgiza kai ya ce "za ta kai shekaru goma sha biyar dai."
Ta zabura ta miqe tsaye a fusace "yanzu na ji Magana, budurwa ka yi ciwon so yana nuqurqusarka ka fake da canjin yanayi. Amatullah kin yi shiru kin bari ni kaxai ina ta masifa, abin nan fa ba ni kaxai yake damu ba hard a ke gara ki tashi mu yaqi matsalar nan. Ga gaskiya ta bayyana Allah Ya nuna mana muna zaman mu."
Amatullah ta yi ajiyar zuciya ta ce "me zance? Abin dai yana bani mamaki, haba Abban Faruk ban san ka da voye-voye ba. Me yasa ka canja yanzu?"
Ya sunkuyar da kai qasa bai ce da su komai ba.
Amatullah ta jawo hannun Nauwara ta zaunar ta ce "ki bar ni da shi yanzu za ki ji gaskiyar magana. Iziddin yarinyar nan marainiya sonta kake ne?"
Ya girgiza kai ya ce "yadda na faxa muku ban santa ba ta zo wajena neman taimako kuma na taimaka mata, na bata lamba ta idan tana da matsala ta kira ni shine kawai."
Amatullah ta juya ta kalli Nauwara ta ce "kin ji amsar da ya bayar, ki yarda da hakan."
Nauwara ta ce "ai in duk jikina kunne ne ba zan yarda da haka ba, bakya ganin yadda ya susuce kwana biyu tunda ya haxu da ita aka rasa kansa. Har kwana fa ya yi a waje, ya shigo da wasu kayan daban a jikinsa ya bar nasa na da a can har yau bai xauko su ba."
"Subhanallah Nauwara har da zargi a tsakaninmu?" Iziddin ya faxa a lokacin day a zazzare ido dan tashin hankali.
Nauwara ta yi shiru bata amsa masa ba tana faman huci kamar zata haxiyi zuciya ta mutu. Ya ga dai abin bana qareawa ba ne ya tashi ya nufi xakinsa, yana shiga kafin ya rufo Nauwara ta tura qofar ta shiga ciki gami da kwashe mukullan qofar.
Ta ce "Iziddin! Ba zaka qara rufe kanka a cikin xaki ba ka yini kana hirar soyayya da wata 'yar iska ba, mu ka bar mu a gefe. Sai dai ayi duk abinda za'a yi yau."
Bai xaga kai ya kalleta ba balle ma ya tanka mata ya wuce banxaki kai tsaye ya yi alwallar la'asar ya zo ya yi sallah, Nauwara tana zaune ta gefen gadonsa ta kasa, ta tsare . Wayarsa ce a hannunta ta bincike, ba ta ga lambar da ya amsa yanzu ba, ya goge dan haka babu tantama bashi da gaskiya shiyasa ya goge. Ya xaga hannu sama yana ta kwararo addu'oi akan Allah Ya yaye masa bala'an nan da suke ta qaruwa. Ita kuwa Nauwara tana ta kwararo masifa tana faxa tana maimaitawa zaman lafiya a gidan nan ya gama samuwa.
Aka kira sallar magaruba ya miqe ya nufi qofar fita sai ta tare gabansa ta tambaya cikin tsiwa "ina zaka je ka xauki mukullin mota?"
Ya faxa cikin sanyin jiki "masallaci zan je in yi sallar magriba da isha'i." Ta girgiza kai ta ce "akwai masallaci a qofar gidan nan ba sai ka je babban masallaci ba."
Ya miqa mata mukullin mota ya fice duk da haka bata yarda ba sai ta biyo shi falo gami da raxawa Faruk ya bi Abbansa masallaci su yi sallah tare. Faruk ya zabura ya bi Abbansa da gudu yana ta murna dan ya kwana biyu bai ga Abbansa a gida ba balle su fita tare.
Ana idar da sallar isha'i suka dawo gida, yana shigowa falo Nauwara ya iske a bakin qofa ta tsare qofa tana jira ya shigo ta rufe qofa, yana shiga ta kulle qofar falon ta nuna masa teburin cin abinci ta ce ga abincinsa can ta gama. Yana tafe yana sanxa ya je ya zauna, gaba xayansu suka haxu da yara suka ci abincin dare kamar yadda suka saba ada. Amma fa Iziddin tamkar mutum-mutumi ne hankalinsa kusan gaba xaya baya tare dasu, yana ta jujjuya maganar Aljannah ya cika da fargabar abinda ya sa take kiransa tana kuka. Yana gama cin abinci ya shiga xaki ya duba wayarsa bai ganta ba tana wajen Nauwara sai ya ji hankalinsa gaba xaya ya qara tashi. Yau ba su yi waya da Khamis ba ma gaba xaya, gashi babu wayar balle ya kira Sahiba ya ji halinda Khamis ya ke ciki ko shine ma ya haddasa matsalar."
Nauwara ta shigo da shirinta tsaf a xakinsa take da niyyar kwanaa yau, babu in da zata matsa balle ya sami sukunin aiwatar da wani abu. Haka ya kwanta ba tare da ya iya bacci ba, ya gaji da kwanciya yana ta juyi, da tsakar dare ya tashi ya yi ta sallah ita dai tana voye da mukullai a qarqashin filo tana qyallara ido tana tallonsa duk motsin da ya yi.
Da asubah ta yi ya yi sallah sannan ya kwanta akan abin sallah, barci mai nauyi ya kwashe shi sai a lokacin Nauwara ta gama gadinsa tunda ta tabbatar ya yi bacci sai dai kash! Yau ne zata fita daga girki bata so hakan ba dan ta san Amatullah ba wani katavus da zata yi.
RANAR LAHADI 8 GA WATAN 6 2014
Bai tashi daga barci ba sai qarfe xaya na rana ya iske Nauwara bata nan amma ta ajiye masa waya da mukullan xaki a gefen filonsa. Ya zabura ya xauko wayar ya ga a kashe ta ke sai ya ji sanyi a ransa kada Aljanna ta kira Nauwara ta xauka, ba wai gudun kada Nauwara ta xauka ba ne kaxai ya san da lambar Zahidah take kira baya so Zahidah ta san lambarsa. Ya kunna wayar sannan ya dudduba saqonnin da suka shishshigo, ya iske babu saqon Aljanna ko xaya. Ya so ya ji abinda yake faruwa amma ba zai iya kiran lambar ba dan haka sai ya gaggauta faxawa wanka ya fito ya shiryar tsaf kamar wani xan saurayi sanye da qanana kaya a jikinsa tabbas ya yi shigar zuwa club idan ta kama yau. Ya fito ya nufi xakunan matansa kowacce sun gaisa amma babu fara'a a fuskokinsu dukka ukun.
Har ya juya zai fita Amatullah ta tsayar da shi ta ce "baka ci abinci ba."
Ya girgiza kai ya ce "ba zan komai ba, sai dai da daddare insha Allah. Zan je masallaci kuma zan je gidan Khamis daga can zan shiga cikin gari, sai dare zan dawo"
Ta amsa cikin sanyin jiki "Allah Ya dawo da kai lafiya."
Ta fara zubar da hawayen takaici saboda mijinta ya canja halayyarsa gaba xaya, wai mutumin da baya fita ko ina a qarshen sati (week end) kwata-kwata ma shine yanzu yake maganar zai yi dare a waje, wato yawon rana ma bai ishe shi ba.
A masallacin qofar gidansa ya yi sallah sannan ya wuce gidan Zahidah kai tsaye, bai tarar da kowa a gidan ba sai wata tantiriya mata ita kaxai ta gama yi masa kwarkwasa sannan ta faxa masa Zahidah da Aljannah ba su kwana a gida ba, ba su dawo ba tun fitar jiya. Sai hankalinsa ya tashi matuqar tashi, yana fita ya zarce gidan Khamis, nan ma ya iske gidan a kulle da kwaxo tun daga get. Ya tambayi mutanen da suke zaune a qofar gidan suka tabbatar masa tun jiya basu giftawar kowa ba a gidan nan ba. Dan haka sai Iziddin ya gasgata Zahida, Aljannah da Khamis suna tare kuma wataqila suna cikin matsala. Amma ina Sahiba ta tafi? Ko ta gaji da halayyar mijinta ta haxa kayanta ta tafi garinsu kamar yadda ta daxe tana ambata.
Iziddin ya faxa a bayyane "haqiqa Khamis ya zalunce ni, ya zalunci iyalina, kuma ya zalunci kansa da kansa, ya zalunci iyalinsa, gaba xaya ya rugurguza mana rayuwarmu mu dukka."
Ya daxe a zaune a cikin mota a qofar gidan khamis ba tare da ya san abinda zai yi ba, da kuma in da zai nufa ba. Wayar Khamis ya yi ta kira a kashe, sai ya kira wayar Sahiba ta shiga tana qara(ringing) amma bata xauka ba. Da ya ga dai ba shi da sauran mafita dole kawai ya kira lambar Zahidah ko ta xauka ko Aljanna ta xauka bai dame shi ba komai ta fanjama-fanjam. Ya danna lambar sai wani gagarumin tashin hankali ya tabbata a cikin zuciyarsa, yana ta fargabar jin wacce zata xauka da kuma fargaba jin amsar tambayar da zai yi. Kash! Ya kira itama wayar a kasha, ya gwada fiye da sau goma bata shiga ba, ya ja doguwar ajiyar zuciya ya yi tagumi, ba shi da sauran dubara kuma.
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." kawai yake Ambato.
Ya shiga tunanin in da zai je ya nemo su waje xaya ya kamata ya je ya duba su shine 'club' xinsu. Dan haka sai ya nufi can, yana tafe yana ajiyar zuciya. "wannan bala'i da me ya yi kama?" Iziddin ya faxa a bayyane a lokacin da yake qoqarin shiga hotel xin.
Ya sake haxuwa da wani babban bala'in har sai da ya ji tamkar qirjinsa zai tsage gida biyu a sanadiyyar bugun da zuciyarsa ta yi, arangama ya yi, suka haxa ido qiri-qiri da Na'if da Laurat a bakin get xin shiga su kuma suna fitowa, bayan sun kwana sun hantse su. Suka qurawa juna ido ba tare da kowa ya yiwa kowa magana ba har suka wurwuce, Iziddin ya ji kamar ya tsaga qasa ya faxa dan kunya babu mai fitar dashi daga zargi. Ya isa qofar club ya iske a kulle, sai ya tambaya ko akwai wasu mutane da suke ciki suna barci? Aka tabbatar masa babu kowa kuma sai da daddare a ake buxewa. Sai jikinsa ya yi sanyi ya yi saranda babu kuma wani abu da zai iya bincika. Ya shiga mota yayi ta karaxa gari kamar wani mai ciwon hauka sabon kamu, idan ya haxu da masallaci sai ya tsaya ya yi sallah ya wuce haka sai da ya kai qarfe xayan dare a titi yana zagaye daidai lokacin ya tabbatar an fara gudanar da baxala a club sai ya juya motarsa ya nufi can. Bai yarda ya shiga ciki da kamanninsa ba sai da ya shiga shagon nan ya sayi hular gashi da gemu ya saka sannan ya shiga. Yana shiga ya yi arba da Na'if da Laurat suna rawa amma basu gane shi ba ya wuce ta gabansu, yana ta duba Zahida da Khamis bai hange su ba. Sai ya zarce babban falon da ya iske su rannan, akwai jama'a da yawa amma babu su a ciki haka ita ma Aljanna bata nan.
Sai ya qarasa wajen Liyo tunda ya tabbatar ya yi musu fari sani, ya miqa masa hannu. Liyo ya miqe tsaye ya gwaggwafe ya tale qafa ya dungurawa Iziddin hannu wai ita ce gaisuwarsu a nan, daga nan Liyo ya tabbatar Iziddin sabon shiga ne dan bai iya gaisuwar ba ma tsayawa ya yi zangargar yana kallonsa amma gas hi da ruwan 'yan duniya ya tara gashi. Iziddin ya yi murmushi ya tambaye shi ko Zahida ta shigo? Liyo ya yi jim alamar bai gane wacce yake nufi ba, sannan Iziddin ya tuna sunan da suke kiranta.
Iziddin ya ce 'Hidah Easy'
Liyo ya ce "au shugaba zaka ce. Gaskiya nima na yi cigiyarta yau bata shigo ba."
Iziddin ya ji gabansa ya faxi ya faxa a gigice " lafiya bata shigo ba ko daman tana fashi?"
Liyo ya ce "gaskiaya a shekara guda ma bata yi fashi ba kullum sai ta shigo, kuma bata wuce qarfe xaya bata zo ba yanzu gashi biyu saura, daqyar idan zata shigo xin. Iziddin ya sami waje ya zauna ya riqe kai saboda tsabagen ciwon da kansa yake yi masa.
Liyo ya tsiyayo barasa ya miqa masa a kofi ya ce "xan uwa ka kora wannan zaka ji garau."
Iziddin ya girgiza kai ya ture kofin da ya naniqa masa a setin bakinsa, ya tashi ya gaggauta barin wajen dan kada kixa da ganin abinda bai dace su fasa masa kwakwalwa.
Izzyiddin na fitowa ya nufi wajen motarsa ya shiga ya zauna sanna ya yaye gemuna ya watsa ta wundon mota, sai ya ga wani mutum ya zo da sauri ya tsugunna ya xauka. Mamaki ya hana Iziddin rufe bakinsa kallon mutumin kawai yake yi, yana xagowa sai ya haxa ido da Na'if. Ya xaga gashin sama ya jujjuya ya qyalqyale a dariya irin ta mugunta.
Ya ce "Sannu Yaya, shek Iziddin. Barka da shigo harka irin tamu."
Sai Iziddin ya sanqare a zaune ya kasa magana har Na'if ya gama iskantarsa ya juya yana xauke da gashin a hannunsa. Danqari! Tabbas matsala mai qarfi ta qara kankama, sai gyaran Allah kawai. Iziddin bai shiga gida ba sai qarfe biyu da kwata, da sanxa ya shiga amma abin mamaki sai ya iske Amatullah a zaune a falo ita kaxai ta yi tagumi sai tausayinta da tausayin kansa da kansa ya kama shi. Hawaye ya kwaranyo daga idanuwansa shima kamar yadda tana ganinsa ta fashe da kuka, ta taso da sauri ta tare shi.
Ya faxa cikin sanyayyaiyar murya "Amatu ki yafe min kuma kiyi min alqawari za kiyi min addu'a, ki riqe min 'ya'yana idan na mutu."
Sai ta gigice jikinta ya xauki rawa "ta tambaya me yake damunka ne wai?"
Sai ya kasa faxa mata, tayi- tayi ya faxa mata bai faxa ba har suka kwanta tana yi masa magiya amma bata ji kalma xaya daga bakinsa ba. Ta tabbatar a ido biyu ya kwana bai rintsa ba, haka ta san yunwa yake ji bai ci komai ba, ta tashi ta haxa masa ruwan shayi ya xan kukkurva.
RANAR LITININ 9 GA WATAN 6 2014
Da asubah ta tashe shi dan ya yi sallah sai ya kasa tashi, saboda tsananin ciwon kai da ciwon qirjin da yake damunsa. Ya yi iya qoqarinsa ya miqe abu ya faskara sai ta kira likitansa, da gudu likita ya qaraso a gigice yadda ya ji tana kurma ihu a waya. Ya dudduba shi, yaga alamar ya kamata su kwantar da shi a asibiti ko da na kwana biyu ne, dan haka suka xunguma a suka tafi asibiti su dukka hard a Nauwara. Makeken xaki mai banxaki da falo na alfarma aka saka shi a National Hospital. Aka dinga xura masa ruwa (drip) kasancewar ruwan jikinsa ya yi qasa da yawa a sanadiyar rashin cin abinci da rashin hutu, haka zalika ciwon gembon ciki (ulcer) ta yi masa kamun kazar kuku duk a sanadiyar rashin cin abinci akan lokacin daya dace. Amatullah da Nauwara sun saka shi a tsakiya suna kallo suna kuka, suna addu'a Allah Ya tashi kafaxunsa. Yau shine karo na farko da suka tava ganin maigidansu ya yi ciwo haka mai tsanani har ya kai shi ga kwanciya akan gadon asibiti.
Aka rasa wacce zata haqura ta koma gida ta kula da yara kowacce tana ganin ba zata iya zama a gida ba, ba tare da tana ganin yanayin jikinsa ba. Yara an bar su da masu aiki, da direba sai dai a waya su Amatullah suke kira gida suna faxa musu abinda za su zartar a gidan. Iziddin na kwance ido a rufe kamar mai bacci kamar kuma idonsa biyu, tsabagen azabar ciwo ne kawai. Likito na iya qoqari wajen kula dashi, duk da dai ruwa (drip) kawai ake ta saka masa daga ya qare sai a xaura masa wani.
Girkin Amatullah ne dan haka dole Nauwara ta haqura ta koma gida dan ta kula da yara, haka ta shiga motarta ta tafi ba dan tana so ba tana tafe tana haxa hanya saboda damuwa sai ta sulale ta gangara gefen hanya ta tsaya, ta yi ta kuka tana faxawa Allah Ya yayewa mijinta ciwon nan, ya fitar da shi daga masifar da yake ciki dan ta tabbatar akwai wani voyayyen al'amari da yake faruwa a tare da shi ya qi ya bayyana. Ta isa gida ta iske 'yayansu sun yi zugum a falo duk da qarairayin da su Hauwa'u mai aiki suka shirga musu game da in da iyayensu suka tafi amma dai sun ji a jikinsu akwai wata damuwa tabbas, basa walwala kwata-kwata. Su na ganin Mama Nauwara sai farin ciki ya rufe su suka falfalo da gudu suka tare ta suna tambayar Umma Amatullah da Abbansu. Ta yi diri-diri kafin ta qirqiro wata qaryar Hauwa'u ta yi sauri ta kawo mata a gaji.
Hauwa'u ta ce "na faxa muku sun tafi shoprite su duba wajen da za'ayi birth day party faruk wani watan."
Nauwara ta yi ajiyar zuciya ta ce "nima daga can nake, gobe ma zan koma."
Faruk ya ce "saboda kama wajen birth day shine zasu kwana acan?" Nauwara ta ce "ai dole ne saboda dogon layin da ake bi tun daga ciki har bakin get. Sannan mutum ya zo ya bi layin biyan kuxin gyaran wajen (decoration)."
Sai yara suka hau tsalle da murna suna rugume junansu.
Nauwara ta ce su tafi xakinsu su yi tsallen a can zata shiga xaki ta huta kanta ke ciwo. Hauwa'u da Anna suna ta jimanta mata suna masu addu'a Allah Ya bashi lafiya. Amin.
Amatullah kuwa ta saka Iziddin a gaba tana kallo ko qifta ido bata yi, ta yi kuka ta gaji, ta yi addu'a babu adadi sannan ta shiga yi masa hira tamkar da itace take yi dan baya jinta a mimmiqe kawai yake yana barci daga ganin barcin bana lafiya ba ne, aikinta kawai shine kula da ruwan da aka qaqaba masa daga ya qare sai ta garzaya ta kira ma'aikaciyar jinya(nurse) ta zo ta cire ta qaqaba masa sabo. Bata yi bacci ba sai gyangyaxi kaxan –kaxan, haka Nauwara bata rintsa ba bata da aiki sai kiran Amatullah a waya tana tambayar jikinsa.
"Da sauqi za'ace dai." Amsar da Amatullah take bata.
Nauwara ta qara tambaya "ya farfaxo kuwa?"
"Har yanzu bai farfaxo ba." in Amatullah.
"Ina maganar sauqi kuwa a mutumin da bai san waye akansa ba ma." Nauwara ta faxa a lokacin data fashe da kuka. Sai hankalinta ya sake tashi, abu kamar wasa tabbas ba qaramin ciwo ba ne wannan.
A haka dai har Allah Ya wayi gari.
RANAR TALATA 10 GA WATAN 6 2014
Qarfe bakwai da rabi a asibiti ta yiwa Nauwara sai gata riqi-riqi da kayan abinci, qaton food flask xauke da soyayyen dankali da kwai sai kuma 'flask' xin ruwan zafi. Amatullah ta tare tad a sauri ta tayata saukewa, bayan sun gaisa suka tsaya carko-carko suna kallon mijinsu, jikin dai jiya kamar yau, hakan dai yake. Sai hawaye ya cika musu ido, Amatullah ta karvi mukullin motar Nauwara ta tafi gida dan ta yi wanka ta canja kayan jikinta da suka yayyaqune. Ta iske yara sun tafi makaranta sai masu aiki kaxai a gida. Tabbas kallo xaya zaka yi mata za ka tabbatar tana cikin masifa, idanuwanta duk sun kumbura saboda rashin bacci da kuka.
Hauwa'u na lallashinta "Hajiya so kike a yi biyu" Ki na zaman jinya ke ma za ki jawowa kanki ciwo ki kwanta ciwo Allah Ya kiyaye, shima fa kin ce ulcer ce ta kama shi a sanadiyyar rashin cin abinci ke ma kuma idan kika saka damuwa a ranki ki ka qi cin abinci hakan za'ayi. Ko dan yaranku ai ba zaku so gaba xaya ku kwanta ciwo ba."
Sannan ta yarda ta karvi ruwan shayi ta sha da 'yar wainar kwai, sannan ta lallava ta shiga xakin Iziddin ta yi wanka, tana fitowa ta jiyo rugugin qarar wayarsa a qarqashin filo ta shiga duddubawa sannan ta lalubo ta. Ta ci sa'a bata katse ba, da baquwar lamba ake kira a sabon layin Iziddin, babu suna sai ta yi mamaki dan haka ta gaggauta dannawa. Ta kara a jikin kunnenta ba tare da ta yi magana ba, muryar mace ta ji tana magana cikin kuka.
Ta ce "Aljanna ce ina cikin matsala ka taimake ni."
Mamakin da fargabar da suka ruftowa Amatullah bashi da yawa saboda daman Iziddin ya basu labarinta.
Ta laluba gado ta zauna a gefe a sanyaye, ta yi ajiyar zuciya, ta ce "Aljanna, ki kwantar da hankalinki ki daina kuka. Mai wayar baya kusa ni qanwarsa ce. Ko za ki iya faxa min abinda yake tsakaninku?"
Aljanna ta yi shiru da ta ji muryar mace, sai can ta ce "taimakona yake yi kawai."
Amatullah ta ce "taimako kawai? A ina ku ka haxu?"
Sai Aljannah ta kashe waya tana tsoron ko matarsa ce kada ta haddasa masa rigima a cikin gida.
Amatullah ta yi tagumi tana mamaki a inda Iziddin ya samo wannan yarinya, tabbas ta san shi da tausayi da kyauta amma dangantakar tayi nisa, sannan damuwar daya shiga ne matsala an rasa akan abinda yake yiwa.
"Anya ba a sanadiyar yarinyar nan ba neb a kuwa?" Amatullah ta tambayi kanta a bayyane.
Ta zabura ta lolubo lambar da Aljannah ta kira ta sake kira tana so ta tabbatar da abinda yake faruwa, ta ci sa'a kuwa wayar ta shiga amma kuma muryar namiji ne ya amsa.
Ta gaishe shi sannan ta qara da cewa "ina so in yi magana da yarinyar da ta kira ni yanzu da wannan lambar."
Sai ya shaida mata akan hanya ya haxu da ita ta roqe shi ya bata aron waya ta kira kuma ta shiga mota ta tafi.
Amatullah ta sake tambayarsa "da Allah a wanne gari kake?"
Ya ce "Sule ja."
Sai ta yi godiya ta kashe waya, cike da damuwa take tambaya " har Suleja ke nan ya je ya haxu da ita? Me ya kai shi Suleja? Tabbas akwai alamar tambaya akan Iziddin da yarinyar nan." Ta na magana tana shiryawa ta gama ta fito ta kama hanyar asibiti.
Tana ta fargaba kada idanuwanta su nuna mata mugun gani, tat a addu'a har ta shiga xakin. Ta yi farin ciki da ganin mai gidansu a Zaune yana kurvar shayi, har ya yi wanka ya canja kaya, sai ta fara tunanin ko mafarki take yi.
Ta jefar da Jakarta qasa ta qarasa kan gadonsa da sauri ta kama baki ta ce "Alhamdulillah! Me nake gani haka?"
Iziddin da Nauwara dai dariya suke yi mata kawai.
Nauwara ta ce "Allah abin godiya kina fita ya buxe ido ya ce min zai je banxaki, na ce zan fita in kira maza su xaga shi su kai shi, sai ya ce zai iya da kansa. Na kira Nurse ta cire masa ruwa (drip) na kama shi ya shi tashi ya shiga banxaki da qafarsa, sai kawai ya yi wanka ya zo ya yi salloli shine ya karvi ruwan shayi yake sha."
Amatullah ta ce "ai ruwan shayi ba zai riqe ka ba, ka haxa ko da wainar kwai ne ko ayi waya gida a dafa maka wani abu, tunda ba'a son mai ulcer ya dinga cin soyayyen abu."
Nauwara ta ce "ki kira Hauwa'u ta dafa indomie ta bawa direba ya kawo yanzu tunda yana sonta."
Amatullah ta xauko wayarta da sauri ta kira Hauwa'u ta sanar mata.
Qarar wayar Iziddin ce ta xauki qara daga cikin jakar Amatullah sai aka hau kallon-kallon ita da Nauwara da Iziddin. Ta saka hannu a jaka ta zaro wayar da sauri ta duba, sunan Khamis ne ya bayyana sai ta danna ta miqa masa da sauri gami da ce
"Khamis ne."
Ya karva a sanyaye ya kara a jikin kunnensa.
Khamis ya ce "ka tashi lafiya? Yau litinin na ga ban ganka a ofis ba. Lafiya baka shigo ba.?"
Iziddin ya yamutse fuska ya ce "lafiya qalau, ba na ji daxi ne, amma gobe in sha Allah zan shigo."
Amatullah ta girgiza kai ta faxa cikin raxa "ka faxa masa baka da lafiya gobe ma ba zamu barka ka fita ofis ba, sai jikinka ya yi kwari."
Iziddin ya kashe waya ya ce "bana so ayi ta yaxawa bani da lafiya hankalin jama'a yana tashi, ai na ji sauqi ma."
Nauwara ta ce "ai kuwa na gama yaxawa ma dan na faxawa Daddy da Mummy xazu, anjima ma zasu shigo dubiya na san Daddy zai sanar a ofis dan a ci gaba da aiki kada ayi ta jiranka, amma abin mamaki Khamis bai ji a ofis ba."
Iziddin ya ci gaba da duba missed calls da saqonnin da aka tutturo masa babu lambar da bai sani ba a ciki sai wacce Aljanna ta kira. Amatullah tana so ta yi masa bayanin yadda suka yi da Aljannah tana gudun kada Nauwara ta ji, ta san tabbas zata yi fushi saboda tana da tsananin kishi akan duk macen da yake hulxa da ita. Kuma ga ta da rashin gamsuwa idan aka yi mata bayani, ba zata yarda ba. Amatullah ta xauko wayarta ta koma kan kujera a gefe ta rubuta masa saqo tana mai yi masa bayani akan yadda suka yi da Aljanna, da kiran da ta sake yi yiwa lambar wani mutum ya xauka ya ce ta shiga mota ta tafi a Suleja. Duk da bata faxa masa cewar Aljannah tana kuka ta ce tana cikin matsala ba, amma ta lura da ya karanta saqon hankalinsa ya tashi, ya yi shiru sannan ya ajiye wayar a qarqashin filo, ta yi hakan ne saboda ko hankalinsa zai kwanta ya tabbatar Aljannah tana raye kuma tana cikin qoshin lafiya idan ma akanta ne ya kwanta ciwo.
Ba jimawa direba ya shigo xauke da 'food flask' xin indomie, ya gaishe su ya yiwa mai gidansa sannu da jiki, Nauwara ta tashi ta karva sannan ya tafi. Ta xauko plate da cokali ta zuba ta miqa masa, ya karva ya ci amma lauma biyu ya yi zai ajiye sai ta hana shi tana lallava shi yana ci har sai da ya ci da yawa, ta miqa masa ruwa ya sha.
Dai-dai lokacin likita ya shigo, Dr. Saleh ya dube shi ya yi murmushi ya ce "jiki ya yi kyau, amma fa zan ci gaba da riqe ka har sai ka yi kwanaki uku da mu anan, saboda ka samu ka huta sosai, rashin bacci yana damunka.
Nauwara da Amatullah suka haxa baki "gaskiyarka likita haka ya yi dai-dai."
Ya dudduba Iziddin ya rubuta magunguna ya miqawa Nauwara ba tare da vata lokaci ba ta xauki Jakarta ta rataya.
Ta ce "bari in je pharmacy in siyo magani dan ya fara sha yanzu." Amatullah ta ce "toh, sai kin dawo."
Nauwara da likita suka xunguma suka fice, Amatullah ta taso ta dawo gefen gado ta zauna kusa da Iziddin ta dube shi, ta ce "ya na ga kamar hankalinka ya tashi da ka karanta saqona? Kada fa ka damu, gashi baka jin daxin jikinka, Aljanna tana cikin qoshin lafiya. Abinda ban gane ba shine yaushe ka san yarinyar nan da har matsalarta ta zama matsalarka? Menene asalin matsalolinta da take neman taimako a wajenka? Ka da dai ace damuwa da Aljanna ne ya kai ga kwanciya a gadon asibitin nan?"
Sai ya girgiza kai ya ja filo ya kwanta ba tare da ya bata amsa ba. Ba jimawa Nauwara ta shigo xauke da ledar magunguna, ta bashi ya sha, ya koma ya kwanta bacci mai nauyi ya xauke shi.
'Yan dubiya suka fara zarya, waxannan suna shigowa wasu na fita, amma Iziddin bai farka ba matansa ne a falo suke ta karbar 'yan dubiya. Kan kace kwabo xaki ya cika da kwanukan abinciccika kala-kala, amma farfesun kaji da lemuna sun fi yawa. Surukansa ma sun zo iyayen Nauwara wato Alh. Jibrin da mahaifiyarta Haj. Aisha suma sun ciko abin arziqi, 'yan uwa da makwabta waxanda labari ya iske su suma sun zo kowanne yana yi masa fatan Allah Ya bashi lafiya.
Khamis da matarsa Sahiba ne suka iso dai-dai sanda ake kiran sallar magruba, a gigice ya shigo cike fushi yana mamaki, ya na ta faxa da kumfar baki wai ya za'ayi Iziddin ba lafiya har ya kai da kwanciya a asibiti amma aka kasa buga masa waya a faxa masa, ya kira kuma Iziddin ya voye masa ya ce lafiyarsa qalau xan ciwo ne kaxan. Iziddin yana jinsa a lokacin ya yi bacci ya gaji idanuwansa ne kaxai bai buxe ba, baya so ya buxe idon kuwa dan baya so ma ya sake ganin Khamis da idanuwansa saboda maci amana ne, kuma shi ya jawo masa duk wannan damuwa da yake ciki. Amatullah ce take ta bayani tana bada haquri haka Sahiba qawar Amatullah ta ke ta qorafi itama ba'a kira ta an faxa mata ba. Kalaman haquri dai suke ta firfitowa daga bakunan matan Iziddin. Khamis ya daxe a tsaye akan Iziddin yana kallonsa gami da jero masa addu'oin fatan samun sauqi yana tofa masa. Sannan ya juya ya dubi Amatullah da Nauwara.
Ya tambaya ya ce "tun yaushe kenan ya fara ciwon nan ne? Menene asalin abinda yake damunsa?"
Nauwara ta ce "jiya da asuba ya fara an tabbatar ulcer ce baya son cin abinci kwanan nan."
Khamis ya zabura ya yi juyi ya ce "daman na lura da haka, Iziddin ya canja halinsa. Tabbas yana cikin damuwa ashe kuma matansa bai faxa muku ba balle ni. Idan ya yiwa kansa faxa ya cire damuwa ya taimaki kansa, idan yaqi ji zai jawowa kansa matsala, gashi ma yanzu ya jawowa kansa ya tashi hankalinmu mu masoyansa."
Ran Iziddin ya sake vaci da jin wannan kalma ta soyayya a tsakaninsu tabbas khamis mayaudari ne.
Khamis ya gama hayaniyarsa ya ja matarsa suka fita, Nauwara da Amatullah suka tafi yi musu rakiya bakin mota sannan Iziddin ya yunqura ya tashi daqyar yana layi ya lallava ya shiga banxaki, ya xauro alwalla ya zo ya yi ta jero sallolin da suka hau kansa. Da matansa suka dawo sai suka ji daxi da ganinsa yana sallah tabbas mijinsu mai juriya ne kuma mai riqon addini, banda larurar ciwo ba su tava ganinsa ya haxa salloli ba. Daya idar suka gaishe shi suka shiga zayyano masa xinbun jama'ar da suka zo duba shi yana bacci, ya yi mamakin yadda aka karaxa gari aka sanar har kowa ya san bashi da lafiya. Nauwara ta bashi labarin faxa da kumfar bakin da Khamis ya zo yana ta yi wai ba'a kira shi a waya an faxa masa ba, ya yi murmushi kawai bai ce komai ba. Amatullah ta xauki mukullin mota da mayafi ta rataya jaka gami da harhaxa wasu da yawa daga cikin kwanukan da zata tafi gida da su, dan a rabar da abinciccikan idan aka bar su anan lalacewa zasu yi. Kaxan-kaxan Nauwara ta xixxibarwa Iziddin a plate, ta bashi ya karva yana ci, daman su tunda yamma sun ci sun qoshi, sannan ta taya Amatullah kaiwa mota.
Da ya tabbatar sunyi nisa da xakin sai ya xauko wayarsa ya na shirin kiran lambar da Aljannah ta kira shi saboda damuwarta ya kwanta har da wasu mafarkai da ya yi akanta mararsa daxi. Ya na duba wayar sai yaga an kikkirashi da wasu lambobi da yawa waxanda bai gane su ba, ya gane lambar Zahidah kaxai tabbas ya san Aljanna ce. Sai dai kash! baya son ya kira Zahida ta gane shine balle ta san yana da alaqa da Aljannah duk da ya tabbatar Zahidah bata lambarsa dan Khamis ba zai tava bata ba, har abada dan kada a siri ya tonu. Ya rasa yadda zai yi sai ya tuna dabarar voye lambarsa yadda idan ya kira ba zasu ga lambar ba sannan ya kira.
Aljanna ce ta xauka ya na jin muryarta sai ya shaida tad an ya tabbatar sai ya tambaya "Aljannah ce?"
Nan da nan itama ta shaida muryarsa, ta zabura cike da murna ta ce "yauwa kawuna! Kai nake ta nema kwana biyu."
Ya faxa a gaggauce dan baya so Nauwara ta dawo ta ji yana waya da mace "lafiya kike neman taimako daga gare ni?"
Aljannah ta nisa ta ce "matsala mu ka samu da uwar xakina Zahidah har ta kore ni daga gidanta, a dalilin saurayinta ya dawo ya ke sona, ni wallahi ban ma san yana yi ba, ban tava kula shi ba na ga alamar yana shiga harkata kullum na lura so yake ya vata min rayuwa shine ya yi min sharri a wajenta wai nayi masa wasiqa ina sonsa ta zo ta yi ta zagina tana dukana ta watsar min da kayana a waje ta yi min korar kare na rasa in da zan koma." Ta fashe da kuka.
Iziddin ya runtse ido sai hawaye ya cika masa ido ya faxa a fusace "ki na ina yanzu? Ba da lambarta kike kira ba yanzu?"
Ta gyaxa kai ta ce "eh ta zo ta nemo ni da kanta ta dawo da ni, da ta gane gaskiya, dan har na tafi Suleja sai na rasa in da zan je, sannan na hau mota na dawo Abuja gidan makwabtanta ta ji labari ina nan ta aiko ta ce in dawo. Yanzu ta sha ta bugu tana bacci wayarta a hannuna take shine na kira ka. Yaushe zaka zo club ka bani kuxin abinci na kashe waxancan a kuxin mota."
Ya girgiza kai ya ce "ba zan zo kwanannan ba ki sami wani waje ko a makwabtan Zahidah ne ki ranci naira dubu goma zan baki ki biya idan mun haxu. Ko ba zasu yarda su baki ba?"
Aljannah ta yi dariyar jin daxi ta ce "zan samu, na gode Allah ya saka maka da alkhairi."
Ya kashe waya dan ya ji tahowar Nauwara, ya ci gaba da cin abinci, ta shigo ta same shi, suka ci gaba da hira har sai da suka raba dare.
RANAR LARABA 11 GA WATAN 6 2014
Ya tashi da asuba ya sami sallar asubah, shine ma ya tashi Nauwara ta tashi daqyar saboda bata samu ta yi bacci da wuri ba kasancewar taurin kafet daqyar ta iya bacci abinka da sabo da kwanan akan lallausar katifa. Su ka yi sallar asuba, suna idarwa wayar Nauwara ta yi qara, Amatullah ce tana gida amma hankalinta yana asibiti. Bayan sun gaisa, kafin ma ta tambayi mai jiki ta san lafiya qalau tunda ta ji muryar Nauwara raxau ta san lafiya ta samu. Nauwara ta miqawa Iziddin waya suka gaisa, Amatullah ta yi hamdala tayi ajiyar zuciya mai sanyi.
Ta ce "ga yara nan suna so su gaisa da kai."
Yara suka dinga karva xaya bayan xaya suna gaisawa, ya yi mamaki da ya ji maganar birth day ta qi ci ta qi cinyewa a bakinsu, ko ba'a faxa masa ba ya san da haka a ka fake idan sun tamabayi in da ya tafi, sai ya biye musu ya ce za'ayi birthaday xin idan ya dawo. Bayan ya ajiye waya Nauwara ta bashi labarin qaryar da Hauwa'u ta yi ta tula musu, ya sha dariya.
Gari ya sake wayewa sai ga Khamis ya yi sallama ya shigo xakin, a shirye yake tsaf cikin riga da wando (suit) baqaqe, da alama aiki zai tafi. Ya iske Iziddin a zaune akan sallaya, ya miqa masa hannu suka gaisa. Khamis ya sami kujera ya zauna, Nauwara ta gaishe shi suka ci gaba da jajanta abinda ya faru. Ya ci gaba da maimaita abinda aka yi masa wanda bai ji daxi ba.
Kalma xaya Iziddin ya faxa "yi haquri."
Daga nan bai sake cewa komai ba.
Khamis ya miqe tsaye ya dubi agogo ya ce "bari in qarasa ofis, sai da yamma idan na tashi zan sake biyowa. Sahiba ta ce a qara yi maka sannu da jiki jiya da ita muka zo kana a bacci, ta so in kawo yau ma ta yi da su Nauwara a sibiti, na qi na san halin mata dandali zasu buxe na hira su dame ka gashi baka da lafiya gata da goyo yarinyar bata ji varna zata yi ta yi."
Iziddin ya yi murmushi ya ce "jiki ya yi sauqi da ka kawo su ma ba damuwa."
Khamis ya yi musu sallama ya fita, ba jimawa sai ga Amatullah ta shigo da manyan filasan abinci da na ruwan zafi, bayan sun gaisa sai suka haxu su dukka suka karya kumallo, da suka gama ya shiga ya yi wanka ya sha magani. Likita ya shigo ya dudduba shi gami da yi masa aune-aune ya sake jaddada masa ba zai sallame shi ba sai ya qara hutawa. Daman hamma yake ta yi alamar yana jin bacci sai ya haye kan gado, ya ci gaba da biye musu suna hira har barci ya kwashe shi.
Nauwara ta karvi mukullin mota ta tafi gida dan tayi wanka ta canja kaya, bata dawo ba sai da aka gama abincin rana ta ho musu da shi.
Yau ma Iziddin ya yini yana bacci sallah kaxai yake tashi ya yi ya koma bacci, yana shan magani yana cin abinci akan lokaci, sai sauqin ya qara samuwa fiye da jiya. 'Yan dubiya ma yau suna ta dandazon zuwa dan taron har ya fi na jiya, Iziddin yana buxe ido suna gaggaisawa, ana ta tururuwar aiko da abinci daga kowacce kusurwa har ya fi qarfin cin marar lafiya da matansa.
Da yamma Khamis ya dawo asibiti xauke da qatuwar leda ya shaqota da kayan itatuwa ya kawowa marar lafiya, Amatullah ta karva ta kai gaban Iziddin ta nuna masa sai ya yi murmushin qarfin hali ya yi godiya. Khamis ya daxe bai bar asibiti ba har sai qarfe gomar dare shima sai da aka dame shi da kira a waya, ya qi amsawa daga na kira sai ya yi sauri ya katse (rejecting), har sai da Amatullah ta dame shi da magana ta ce masa ya tashi ya tafi gida Sahiba ta gaji da jira gata nan tana ta kira.
Iziddin ya kalle shi kawai ya kawar da kai gefe yana kyautata zaton Zahidah ce ke kira ba Sahiba ba, dan lokacin tafiya baxala ya qarato ya san idan ya fita ma daga asibiti ba gida ya nufa ba. Khamis ya ga dai abin bana qarewa ba ne sai ya zabura ya miqe tsaye, ya yi musu sallama ya fice da sauri, nan da nan Iziddin ya ji ransa ya vaci, zuciyarsa ta hau tafasa dan babu yadda za'ayi ya hana Khamis shigowa wajensa da ya ji daxi, dan gaba xaya ma ciwonsa shine sila. Da likita ya san abinda yake damunsa ma da bai yi wahalar bashi kwayar magani ba, da zai hana Khamis shigowa asibitin nan da ya wadatar. Amatullah ce za ta kwana awajensa dan haka Nauwara ta harhaxa kwanuka ta koma gida.
RANAR ALHAMIS 12 GA WATAN 6 2014
Da sassafe likita ya shigo ya duba Iziddin, ya tabbatar jiki ya yi sauqi sosai kuma ya huta, sai ya jero masa dokokin daya kamata ya kiyaye sannan ya rubuta masa takardar sallama da wata takarda ta magunguna. Amatullah ta karvi takardar da ya rubuta magunguna ta je ta siyo, daga nan ta kai file xinsa inda ake biyan kuxin kwanciya ta biya maqudan kuxi. Ta kira Nauwara a waya ta ce kada ta dafa komai ta zo ta xauke su an sallame su, ba daxewa sai ga Nauwara ta bayyana, suka xunguma suka tafi gida. Iziddin bai damu ya kira Khamis ya shaida masa an sallame su ba, duk da ya san zai zarce asibiti daga wajen aiki.
Sai ga Khamis da magaruba ya shigo falon gidan Iziddin ransa a vace, ya tarar da Iziddin a zaune a falo ko sallama bai yi ba ya ce "haba Iziddin wanne irin abu ne haka wai? Me ya ke damunka ne kwanan nan kake yi min wulaqanci haka?"
Iziddin da matansa suka yi carko-carko suna jiran su ji laifin da aka yi masa, sai ya shaida musu ba'ayi masa waya ba an sanar masa an sallame shi ba aka barshi ya sha wahalar xebo abokan aikinsu daga ofis suka tafi dubiya suka iske xakin wayam ba kowa, har hankalinsu ya tashi sun zaci ta Allah ce ta kasance.
Amatullah ta ce "kar ka zargi Iziddin, shi fa ta kansa yake, wayar ma a silent take baya amfani da ita. Mu kuma mun sha'afa murna da cuku-cukun dawowa gida ya sha gabanmu."
Khamis ya harare ta ya ce "yauwa jakadiya ana tava Iziddin sai ki shiga kare shi, ki bar shi yayi magana da bakinsa mana. Ko ciwon ne ya sa ya daina yin Magana kuma?"
Su dukka suka yi dariya, Khamis ya sami kujera ya zauna ya naxe hannayen riga da wando, ya cire safa ya ce faruk ya samo masa silifas zai yi sallar magruba. Sai Iziddin ya ce su qarasa masallaci kawai su yi alwalla da sallar a can. Suka tafi masallacin qofar gida acan suka yi alwalla suka yi sallah, suka fito daga masallaci sai Khamis ya dubi Iziddin ya yi murmushi.
Ya ce "abokina anya ba damuwar rashin ganin Zahida ba ne ya fara tava lafiyarka ba kuwa?"
Iziddin ya dube shi duba na takaici ya kawar da kai gefe bai amsa masa ba. Khamis ya sake cewa "ni dai na lura ka canja tun ranar da ka fita neman Zahida. Ko ka ji wani labari ne akanta wanda bai yi maka daxi ba?"
Iziddin ya zura masa ido yana yi masa kallo na takaici can ya nisa ya ce "ni ban ji labarin komai akanta ba, idan na ji ai ka san zan faxa maka saboda na riqe ka da amana kasan komai nawa, nima kuma a tunanina baka voye min komai."
Khamis ya gyaxa kai ya ce "kwarai kuwa, na san da haka kuma ina baka shawara ka kwantar da hankalinka Allah zai bayyana maka ita alfarmar manzon Allah (S.A.W)."
Sai mamaki ya kama Iziddin, day a ji yadda Khamis yake kiran Allah a baki a zuciyarsa kuma ba haka ba. Daman haka mutane suke basa tsoron Allah kwata-kwata, lallai mutum abin tsoro ne.
Khamis ne ya katse masa tunaninsa ya ce "yau dai baka da lafiya ba zan cika ka da surutu ba amma da weekend zan zo in xauke ka mu fita wajen gari in da babu hayaniya muyi maganar nan, sosai akan Izzatu. Gaskiaya fa ni ban gane abinda yake faruwa ba ai ya ci ace mun tsayar da magana xaya kafin babar sallah."
Iziddin ya sha kunu ya gyaxa kai ya ce "haka ne."
Su ka qaraso cikin falo Khamis ya saka safarsa ya na shirin tafiya sai Amatullah ta ce "ba zaka tafi ba sai ka ci abinci."
Nauwara ta ce "so kike Sahiba ta yi faxa da mu, tana can ta jerewa mijinta abinci tana jira kice ya ci anan."
Kafin ta rufe bakinta Khamis ya haye teburin cin abinci ya xauko filet yana zubawa, ya ce "kanku ake ji wai mahaukaci ya faxa rijiya. Na kwaso yunwa kafin in koma gida ai sai in faxia hanya. Kin san go slow garin nan kuwa idan magaruba ta yi?"
Nauwara ta ce da Iziddin "Abban Faruk, ka je ku ci abincin tare ka fi ci ma da yawa."
Ya wurgo mata harara sai ta yi shiru.
Amatullah ta ce "gara Khamis ya taimake mu ya tursasa ka ka ci abinci kada ya tafi ya bar mu da kai mu yi ta fama."
Itama hararar ya jeho mata, sai ta qunshe baki tana dariya.
Khamis ya ce "ai a faranti xaya zamu ci gashi nan ma na cika mana, idan ya qi ci nima ba zan ci ba, sai in ajiye abincin in tafi gida, zan xauka rowa ce ya yi min a yau."
Iziddin ya ce "kada fa ka biye maganarsu, sun san ban daxe da cin abinci ba ka ci abincinka kawai."
Khamis ya ce "wallahi ka ji na rantse idan baka ci abincin nan ba nima ba zan ci ba, duk da waxannan zuqu-zuqun kifin da naman da raina yake biyawa haka zan ajiye in tafi. Qamshi turu matanka kuwa a kawai iya abinci mai daxi." Su dukka suka kwashe da dariya amma banda Iziddin haushi ne kawai ya kama shi, a dole ya taso ya zo ya zauna ya xauki cokali ya fara ci badan yana so ba, ko kallon fuskar Khamis bai cika so yana yi ba. Babu abinda zuciyarsa take yi sai tafarfasa, yana kyautata zaton Khamis ba gida ya nufa ba idan ya fita, shiyasa ma yake cin abincinsa anan. Gidan Zahidah zai je daga nan su wuce Hotel har asubah. Iziddin ya ajiye cokali ya dubi Khamis yace "Sahiba ta san kana nan ko? Ka da ta ga dare ya yi baka qaraso ba, ka kirata ka faxa mata kana nan."
Khamis ya yi mamaki da jin waxannan kalamai sai ya yi dariya ya ce "kai haba kamar wani yaro zata tutsiye ni ta ce ina na ci abinci."
Iziddin ya girgiza kai ya ce "ba tsoro ba ne, ai haqqi ne da kuma kyautata zamantakewa. Musamman ni da kai da muka yi sa'ar mata na gari masu yi mana biyayya sai mu yi ta qoqarin kyautata musu."
Khamis ya gyaxa kai ya ce "haka ne." Amatullah da nauwara suka haxa ido suka ci gaba da saurar hirar.
Iziddin ya ci gaba da cewa "babu abinda ya fi kwanciyar hankali a duniya irin kaga hankalin matarka ko matanka a kwance, saboda rayuwar mata ba zata yiwu ba sai da mu maza, haka muma mazan rayuwar mu sai da mata dan haka mu kyautata musu, mu tausaya musu saboda suna da rauni."
Khamis yana tura loma yana gyaxa kai da alama jikinsa ya xan yi sanyi har ya zargi kansa saboda ya tabbatar baya kyautatawa Sahiba, amma a tunaninsa babu wanda ya sani dan ya shaidi Sahiba da riqe sirrinsa ba zata tava faxawa kowa ba.
Nauwara ta tave baki ta faxawa Amatullah cikin raxa "ji mutuminki yana wa'azi kamar shima yanzu bai canja halinsa ba. Ashe duk abinda yake yi yana sane ya danne saninsa."
A haka dai Iziddin ya dinga yi masa hannunka mai sanda har suka gama cin abinci, ana ta kiran Khamis a waya yana amsawa a tsorace. Amsa xaya yake bayarwa "gani nan zuwa nan da mintina talatin."
Tabbas ba Sahiba ba ce, da ita ce da ya bashi sun gaisa ta yi masa sannu. Kallon da Iziddin yake yi masa na tara saura kwata shi ya sa Khamis yin bayanan qarya ba tare day a shirya ba, wai Sahiba ce take kira ta ji shi shiru. Wannan bayanai sun sake tabbatarwa da Iziddin Zahida ce take kira.
Khamis ya gaggauta gamawa ya yi musu sallama ya fita da sauri, ran Iziddin ya sake vaci ya wuce cikin xakinsa ya kwanta ba tare da yayi niyyar kwanciya da wuri ba, sai cikin dare ya farka ya yi sallar isha'i da nafiloli. Addu'a ita ce makamin mumini, Allah Ya na tare da mai gaskiya. Ya na ta neman agaji daga Rabbil samawati Ya yi masa maganin masifar nan data addabe shi. Amin
RANAR JUMA'A 13 GA WATAN 6 2014
Ranar juma'atu babbar rana bai fito daga xaki ba sai sha biyu da rabi na rana, ya fito idanuwansa a kunbure gaba xaya kamar wanda aka nausa, hankalin matansa ya tashi suka nemi su hana shi zuwa masallacin ma ya ce babu komai zai iya, shi lafiyarsa qalau yawan bacci ne ya kunbura masa ido. Ya haxu da yara da direba suka tafi masallaci. Ana idarwa ya ce da direba ya kai shi unguwa wuse zone 6. Gidan Zahida ne ba komai ya yi niyyar yi ba illah ya duba ko zai ga motar Khamis, ai kuwa suna shiga cikin get xin gidan sai ga motar Khamis a ajiye a gefe.
Faruk ya zabura ya ce "Lah Abba ga irin motar Baba Qarami har da wannan xan catoon xin da ya saqala a jikin mudubi."
Izidin ya ce "ba ita ba ce irinta ce dai."
Direba ya yi murmushi ya sosa qeya ya ce "ranka ya daxe ai ina ga motar ce saboda ga lambar ma iri xaya ce."
Iziddin ya yi shiru, sai ya yi murmushin qarfin hali ya ce "oh haka ne fa kun fini gaskiya mu juya mu koma gida kawai bana jin daxin jikina zai dame ni da surutu idan muka haxu, da naso mu shiga mu gaisa."
Su ka juyo suka kamo hanyar gida zuciyarsa tana ta tafasa tabbas yau badan da direba da yara ya zo ba babu abinda zai hana shi ya shiga ya ritsa Khamis ayi wacce za'ayi, dan ya gaji da wannan takaicin da yake neman ya halaka shi a banza. Ya ji kamar ya xauko xaya motar ya dawo gidan ayi wacce za'ayi yau a qare a yau. Amma da ya dinga karanto Innalillah wa inna ilaihi raju'un sai ya ji tafasar da zuciyarsa take yi ta fara hucewa. Amatullah ta bashi abinci ya ci suka zagaye shi har yara suna yi masa hira, tausayinsu yake ji gaba xaya kwanan nan bashi da lokacinsu ya fuskanci daxi suke ji yau da suka ganshi a kusa da su sai ya zauna a gida bai fita ba har dare. Bayan sun idar da sallar isha'i shi ya ja su jam'i ma,sannan ya umarci kowa ya je ya kwanta, shima ya shiga ya kwanta.
Nauwara ta dinga yi masa hira ta ji babu amsa har ta gaji ta kwanta ita ma, ranta ya vaci ya juya baya ya yi shiru kamar mai bacci amma idanuwansa biyu, Khamis ne matsalarsa a duniya gaba xaya ma.
RANAR ASABAR 14 GA WATAN 6 2014
Tunda garin Allah ya waye Iziddin bai fito daga xaki ba haka bai tashi ya yi wanka ba balle ya ci wani abu, Nauwara ta dinga yi masa magiya akan ya tashi ya yi wanka ya ci abinci har ta gaji ya qi tashi, a kwance yake kawai a kan gado yana ta juyi. Tunani kala-kala yake yi yadda zai vullowa wannan matsalar da ta addabe shi a rayuwa.
Ta fice a fusace ta nufi vangarenta, Amatullah na ganin giftawarta ta tabbatar ba lafiya ba, dan haka sai ta bita a baya da sauri, tana tambayarta ko lafiya?
Nauwara ta fashe da kuka ta ce "gaskiya na gaji da halin Iziddin idan ke za ki iya ni ba zan iya ba, gara ya salihe min mu haqura da juna in koma gidanmu in san bani da miji . . . ."
Bata rufe bakinta ba Amatullah ta toshe mata baki ta ce "Nauwara! kina da hankali kuwa, me ya yi zafi har da kika fara yin irin wannan mummunan tunani? Haba Nauwara ba kya ganin bashi da lafiya shekaran jiya ya dawo gida daga asibiti? Ban tava zaton yadda kike da Iziddin za kiyi tunanin rabuwa dashi ba akan wannan 'yar qaramar matsalar. Me aka yi ma da har zaki ce kin gaji? Tun kwanakin baya ma alamomin rashin lafiyar ne ya fara shiyasa kika ga ya susuce, tun ma kafin ya kwanta amma yanzu da ya sha magani ya huta a asibiti ba ki ga jiya ya yini a cikinmu ba muka sha hira damu da yara gaba xaya."
Nauwara ta sake fusata ta ce "da daddare fa?"
Amatullah ta yi dariya ta ce "wannan sai a hankali idan ya sake samun qarfin jikinsa."
Nauwara ta ce "idanuwansa biyu jiya ya juya baya ina ta yi masa hira ya share ni kamar baya ji na, yau da safe babu yadda ban yi da shi ba akan ya tashi ya yi wanka ya ci abinci ya yi min shiru, ni dai na gaji da wannan wulaqancin gaskiya. Na bar miki kwanan ba zan sake shiga xakinsa ba har sai ya canja halinsa."
Kafin Amatullah ta yi magana suka ji ana ta kwaxa sallama a falo muryar mace da Namiji da yara suke jiyowa, Amatullah ta fito falo da sauri tana amsa sallamar. Khamis, Sahiba da yaransu ta gani gaba xaya gidan sun zo zasu yi musu yini. Sai ta tare su da murna ta nuna musu kujeru suka zauna.
"Ina sauran tagwayen naki suke?" Khamis ya tambayi Amatullah yana dariya.
Amatullah ta ce "au a gidan nan daman akwai 'yan tagwaye ne?"
Khamis ya ce "har da 'yan uku ma, Iziddin, ke da Nauwara, kan ku a haxe kullum kuna tare. Ko sun fita sun bar ki a gida ne?"
Amatullah ta qyalqyale da dariya ta ce " ai su ma ba za su fara tafiya su bar ni ba qafarsu qafata ba ma ware kowa. Kowannensu yana xakinsa, bari in kira Nauwara."
Ta shiga xakin Nauwara ta iske ta tana shirin shiga wanka, Amatullah ta ce "kash! Wanka za ki shiga? Kan ki shiga saka hijabinki ki kira Iziddin su Khamis ne suka zo."
Nauwara ta harareta ta murguxa baki ta ce "wallahi ba zan shiga xakinsa ba, ai na faxa miki ba zan sake shiga ba har sai ya canja halinsa."
Amatullah ta yi ta bata haquri ita kuwa tana sake rantsewa ba zata je ba Amatullah taga dai ba sarki sai Allah Nauwara ta bujire ta fito cikin sanyin jiki ta nufi xakin Iziddin.
Khamis ya zabura ya tsayar da ita ya ce "Iziddin xin shi kaxai ne a xakin? Bari kawai in shiga in taso shi. Meye kuke wani zagaye dan za ku taso min abokina, ko doka ya sa muku idan yana barci kada a tashe shi ne?"
Amatullah ta dawo ta zauna Kahmis ya shige falon Iziddin ya iske baya nan sai ya wuce can cikin xakin kai tsaye, ya hango shi a kwance akan gado yana fuskantar bango. Khamis ya je ya tsaya akansa yana kallonsa kawai, Iziddin yana riqe da wayarsa a hannunsa yana danne-danne, sai ya ji alamar an tsaya akansa dan ya xaga ido a hankali ya dubi mutumin da yake tsaye a tunaninsa Nauwara ce ta dawo a ci gaba da faxan. Ba zato, ba tsammani sai ga Khamis, Iziddin ya fara tunanin ko Khamis ya fara yi masa fatalwa ne ya zo zai halaka shi.
Ya yi cilli da wayar da ke hannunsa ta faxo qasa kan kafet, ya zabura ya tashi zaune a gigice yana faxin "A'uzu billahi minal shaixanirrajim."
Khamis ya sa hannu zai tava shi sai Iziddin ya daka tsalle ya koma quryar gado yana makerketa!
Khamis ya qyalqyale da dariya ya ce "Iziddin haka ka zama wai? Tsoro ka fara ji kamar wata mace?"
Har yanzu Iziddin bai yarda Khamis xin gaskiya ba ne, ta bango ya tsaga ya shigo, dan ba shi ya kamata ya shigo ya same shi har quryar xaki ba, tunda ga matansa a falo a shara'ance.
Khamis ya qyalqyale da dariya ya ce "taso ka fito abokina tun xazu gari ya waye har azahar ta kusa yi."
Ajiyar zuciya masu qarfi Iziddin ya dinga jerowa ya yin da kansa ya dinga sarawa yana ciwo.
Ya faxa a tsorace "ka je zan fito."
Khamis ya tsugunna ya xauki wayar da Iziddin ya cillar ya duba sai ga missed calls xinsa nan guda uku, ashe ma wayar a hannunsa take amsawa ce kawai bai yi ba. Khamis ya ji ransa ya fara vaci ya miqawa Iziddin wayarsa ya fita a sanyaye. Iziddin ya kula da abinda Khamis ya gani sai ya ji daxi a ransa ko Allaah Zai sa ya yi fushi ma ya fita harkarsa. Ya na zauna yana ta addu'a dan bugun da zuciyarsa take yi ta sauka, sai ya ji kira daga wayarsa yana dubawa ya ga lambar Zahidah ce ya tabbatar Aljannah ce, sai gabansa ya hau dukan uku-uku. Ya amsa a tsorace wannan karon muryar Zahida ya ji bata Aljanna ba, dan haka sabuwar masifa ce ta qara afkuwa akan ta da.
Zahida tana huci cikin fushi mai tsanani ta ce "malam kai ne ka ce Aljanna ta ranci kuxi za ka biya?
Ya tabbatar bata san da wa take Magana bad an haka sai ya canja murya ya ce "eh."
Ta sake fusata ta daka masa tsawa ta ce "ka buxe baki kayi magana sosai saboda in sani, an ganta da kuxi tana kashewa ta ce rantowa ta yi a makwabta. Na je maqwabta na tambaya sun tabbatar min a wajensu ta ranta har naira dubu goma sannan nima na rasa kuxina naira dubu ashirin a jaka ta ce bata xauka ba. Shine ta bani lambarka ta ce a tambaye ka kai ka ce ta ranta zaka biya."
Ya ce "ni na ce ta ranta zan biya."
Ta ce "kai ka ce ta saci nawa ma zaka biya?"
Ya ce "in kin tabbatar ita xin ce ta xauka zan biya ki, saboda na hana ta aikata zina da cin kuxin zina."
Ta yi shiru tana huci zuciyarta tafasa kawai take yi tana tunano amsar data dace da maganarsa, can ta ce "to ustazi kai xin a ina ku ka haxu da ita, kuma meye alaqarka da ita idan ba barikin ba? Dan a iya sanina Alajanna bata da wani xan uwa a duniya."
Ya ce "au Aljannar ma karuwa ce kamar ke?"
Ta ce "ni da uwarka muke karuwanci, xan rainin wayo ka sami yariya kana lallavawa kana cutarta kana faxa min ka hanata zina. In ba iskanci ba me ya haxa ka da ita? Kuma a yau ba sai an kwana ba Alajanna zata bar gidana ka zo ka xauke ta ka kaiwa matarka ko uwarka ita, marar mutunci har kana kirana karuwa."
Ya yi shiru yana jin zafin zagin da Zahida ta yiwa iyayensa da sanyin safiyar nan, ya tabbatar a rashin sani ta yi da ace ta san da wanda take magana ko wacce irin giya ta sha ba zata zage shi ba.
Ya na jiyo ihun Aljanna tana faxin "wayyo Allah na Anti ki rufa min asiri ni ba zan bishi ba dan ban san shi ba a wajenki zan zauna. Kuma wallahi bana sata ban xaukar miki kuxi ba, amma ki tambayi Anti Barira qawarki na ganta da asuba ta shiga xakinki ta fito da wania abu a hannunta."
Zahidah ta duba wayarta ta tabbatar yana kan layi bai kasha bat a ci gaba da cewa "ai ko saboda wannan xan iskan daya faxa min baqar magana a waya ba zan zauna da ke ba."
Ya ji qarar mari da duka ta sakarwa a Aljannah, tana ihu kamar ranta zai fita sai ya runtse ido hawaye yana kwaranya daga idanuwansa, sai ya ji an kashe wayar.
Ya faxa a bayyane "wannan wanne irin bala'i nake ciki? Me yake shirin afkawa a rayuwata?"
A fusace ya jawo wayarsa ya kira lambar Zahida, ta qi xauka, ya sake kira ta sa hannu ta katse, ya sake kira ta katse, da ya ci gaba da kira sai ta xauka.
Tana magana cikin hasala "menene kuma?"
Ya ce "ki yi haquri kada ki kori yarinyar nan dan bata san inda zata je ba." Ta miqe tsaye a fusace ta kama qugu ta ce "da daga ina ta taho? Ka zo ka xauke ta ka kaita gidanka tunda ka damu da ita."
Ya ce "to ki taimake ni ki bata waya mu yi magana."
Ta jet a dungurawa Aljanna wayar akan cinyarta tana zaune a bakin qofa tana kuka tana linke kayanta data yi mata wastsi da su.
Hannunta na karkarwa ta xauki wayar ta ce "Aljannah! ka taimake ni na shiga uku yau ba ni da in da zan je, ba ni da kuxin mota, an kwace kuxin dana ranto gaba xaya."
Ya yi shiru ya kasa magana dan takaici yana jiyo muryar Zahida tana magana.
Zahida ta juya ta kalli qawayenta da suka cika falo ta ce "kun ji wani rainin hankali ko, wai shima xan iskan nata Aljannah sunansa sunansu xaya ma. Yarinyar nan da kuke gani ba qaramar makira ba ce, Allah ne kaxai Ya san abinda take shirya mana na tuggu a cikin gidan nan. Ta san sunansa fa amma take ce masa Aljanna dan kada mu gane shi, aka bibiya ma a cikin gidan nan yake saurayin wata a cikinmu ta kwace suka vatar da kama."
Su ka yi shewa gaba xayansu
Huda ta ce "rabu da qaramar 'yar iska, har mu za'a faxawa shiya irin wannan makircin, ni saboda haxa makircina ma na tava haxawa wata mata makircin da ta nemi ta xaga min hankali dan mijinta yana bina sai da mijinta ya kashe ta mixik har lahira shima daga baya aka yanke masa hukuncin kisa na je na kwashe dukiyarsa na gudu daga garin."
Ya girgiza kai ya sake qudirar niyyar vanvaro Aljanna daga cikin makiran matan nan kafin su halaka ta,ba gidan zamanta ba ne nan tabbas. Ya yi ajiyar zuciya ya ce "ki kwantar da hankalinki, ki yi yadda za ki yi ki zo club da daddare mu haxu ko bakya gidan ki hau tasi ki je can ki jira ni zan zo in biya kuxin mai tasi . . . . ."
Bai gama magana ba ya ji Zahidah tayi kukan kura ta rufe tad a duka da zagi tana cewa "da kika faxa masa na qwace kuxinki me zai yi min?"
Wayar sai wayar ta katse, ya na xaga ido sai ga Amatullah a gabansa, ranta a vace da alama ta gama jin abinda yake faxa tun daga falonsa. Jikinta ya xau karkarwa bakinta na rawa, ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un. Iziddin da wa kake waya haka? Me nake ji kana kira? Ku haxu da mace a club?"
Sai ya ji hankalinsa ya tashi ya rasa amsar da zai bata ta sulale ta zauna a gefensa ta xora hannu aka yayin da hawaye mai raxaxi ya fara kwaranyo mata. Ya faxa ya maimaita har sau uku shima "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un."
Ta ci gaba da cewa "yanzun nan na gama bawa Nauwara haquri akanka ta ce ta gaji da halinka ba zata iya zama a haka ba. Na shaide ka, na kare ka, na ce ta yi maka uzuri ba halinka ba ne dan baka da lafiya ne. Ko a mafarki kunnuwana ba su tava jin mummunanr kalmar da naji a yau ba. Ko zan zargi kowa a duniya da aikata wannan mummunan aiki ba zan tava zarginka da bin mata a club ba sai gashi Allah ya tona asirinka da bakinka na ji kana faxa, da ace wani ne ya ji ya zo ya faxa min wallahi ba zan yarda ba. Iziddin ka ci amanta, ka cuce ni a rayuwa, ka yaudare ni da kyawawan halayyarka, har nake ganinka tamkar wani waliyi na aura. Ina dukan qirji ina yabonka a cikin mata wai ni nan mijina ya fi mijin wata hali na gari, kula da ni da riqon addini. Wayyo Allah! Wai uban 'ya'yana ne wannan mai mugun halin, wayyo maraicina yau ya bayyana, yau na tabbatar ni marainiya ce ada da na rasa uwa da uba bana kiran kaina marainiya saboda ga ka ka zame min uwa kuma uba kuma gatana amma a yau dana rasa ka na zama marainiya."
Ta fashe da kuka mai tsanani ta faxa kan cinyarsa.
Ya daskare a zaune ko motsi baya yi, ya zuba mata ido yana kallo bai tava ganin masifar da yake gani ba irin ta yau. Amatullah ce kaxai a duniya bayan mahaifiyarsa da suka yi AMANNA da halinsa, komai ya ce musu basa tantama sun san gaskiya ne amma yau gata tana da hujjar da zata zarge shi, bashi da kalmar da zai furta mata wacce zai iya kare kansa. Lallai abin da ta ji ya faxa hakan ya ce kalaman ba zasu canju ba kuma ba zasu dawo bakinsa ba.
"Magana zarar bunu ce, idan ta fito bata komawa." In ji masu iya magana. Ya tabbatar Ban da Allah babu mai fitar da shi.
Ya faxa a bayyane cikin marainiyar murya "Amatullah kiyi haquri, ki yafe min, kuma ke ba marainiya ba ce tunda ina raye har abada b azan canja daga riqon amanar da nake yi miki ba. Bai zama lallai ki yarda da ni ba amma ina roqarki ki ci gaba da rufa min asiri, ki ci gaba da goyon bayana, ki ci gaba da yi min kyakykyawan zato, ki ci gaba da yi min addu'a Allah Ya bayyana gaskiyar al'amarin nan. Kada ki zarge ni akan abinda kika ji na faxa ba haka nake nufi ba." Amatullah ta xago ta dube shi duba na takaici fuskarta a cike da hawaye, gumi da majina ta fusata ta miqe tsaye t ace "Zargi? Zargi fa ka ce? Ai ba maganar zargi anan, muna magana ne akan zahiri abinda na ji da kunnuwana kuma na gani da idanuwana. Iziddin ka bani mamaki ba zan sake yarda da abinda zaka faxa kuma da wanda zaka aikata ban an gaba. Idan aure zaka yi kayi aurenka mana amma karuwa a club kake bi. Ba zan sake yarda da wani mutum a duniya ba kuma tun daga kanka, na yi maka alqawarin zan rufa maka asiri babu mai jin maganar nan ta vangarena amma ka sani yadda Allah ya tona maka asiri a wajena in har baka daina ba sannu a hankali duniya gaba xaya zata gane halinka, dan Allah ba azzalumin bawanSa ba ne. Na gode Allah da Ya sa ni ce na ji wannan abu ba Nauwara ba, da ita ta ji yau sai ta yi maka ihun da kowa sai ya ji har da surukanka. Iziddin mai muka rage ka da shi da zaka ci amanramu? Dama ace mafarki nake zan farka daga bacci in ga ba gaskiya ba ne."
Ta rushe da kuka ta jawo gefen mayafinta tana sharce hawaye da hanci. Ya sunkuyar da kai qasa ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye shi, muryarsa na rawa ya ce "ni ne zan ce dama ace bacci nake zan farka daga bacci in ga mafarki nake yi ba gaskiya ba bake ce zaki ce haka ba. Allah Ka san komai, Kai ne shaidata, Ka fitar da ni daga cikin mawuyacin halin nan dana shiga na zargi."
Ta ci gaba da magana cikin murya mai karkarwa saboda masifar da ta shiga ciki "zan zauna da kai amma ka sani ba'a vari a kwashe dukka, kuma mutunci madara ne idan ya zube baya kwasuwa. Zan rufa maka asiri ba zan faxawa kowa ba saboda idan na tona maka asiri na tonawa 'yayana asiri kuma na tonawa kaina, haka ban yiwa mahaifina adalci ba saboda ya mutu yana alfahari ya zavarwa 'yarsa kwaya xaya tal da yake ji da ita miji na gari."
Ta fashe da kuka yayin da hawaye mai raxaxi ya surnano daga idanuwa Iziddin, ya cije baki ya runtse ido ya girgiza kai girgiza mai tsanani har sai da Amatullah ta tsorata ta zaci ihu zai kurma, alhali suna maganarsu a cikin sirri.
Ya yi ajiyar zuciya ya jingina kai da bango ya ce "ni na san akwai ranar da da bakinki zaki dawo ki canza wannan kalaman da kika jefe ni da su. Za ki dawo ki tabbatar min ni xin nan da kika shaida tabbas hakan nake ba yaudararki nake ba, sai kin dawo kin tabbatar min tabbas ba ki zama marainiya ba kina da mijin da yake kula da ke. Za ki yi AMANNA da duk abinda na ke aikatawa."
Ta dube shi duba na takaici ta ce " Na daina AMANNA da daxaxan kalamanka, wannan maganar zargi da kake yi ka ajiye ta a gefe abu na gani varo-varo a zahiri. Ina kokonton zuwan ranar da wannan gurvataccen suna dana laqaba maka zai gyaru, babu ranar da gurvatacciyar halayyar nan taka data bayyana zata gushe, ina kokonton wannan ranar da zan yi AMANNA da kai."
Ta shiga banxaki ta wake fuskarta ta goge da tawul ta fito, ta dube shi taga yana zaune ya riqe kai, jikinsa ya yi sanyi, ta ji kamar tausayinsa zai kama ta, nan da nan ta yi qoqarin yakice shi ta wurgar ta galla masa harara, ta ce "ka fito ka salami baqinka kada su zaci wulaqanci ka ke yi musu ko su gane halinda kake ciki. Sun daxe da zuwa har na ga kamar ran Khamis a vace ya fara zargin kana yi masa wulaqanci. Hakan ne kuma dan gaba xayanmu wannan abu ya shafe mu babu wacce kake so, babu wacce kake tunawa sai Aljannah."
Ta fice a fusace, ya bita da kallo yana karanta "inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un."
Da qyar ya tashi ya shiga wanka, wankan ma babu sabulu ya fito ya saka jallabiya ya qaraso falo yana tafiya daqyar kamar wanda kwai ya fashewa a ciki, ya miqawa Khamis hannu suka gaisa. Shima Khamis a sanyaye jikinsa yake baya walwala, Sahiba da yaranta suka gaishe shi suka yi masa sannu da jiki. Iziddin ya sami kujera ya zauna aka yi jigum kowannensu hankalinsa ba'a jikinsa yake ba daga matan Iziddin xin har da shi kansa, haka Khamis da matarsa dan suma sun rikito wata masifar da safen nan ma kafin su fito sun tafka rigima dan Sahiba ta gama bincike ta binciko Zahida wacce ya yi mata laqabi da 'Sahiba 2' a wayarsa har ma ta kira Zahidah sun yi zage-zage a waya. Sahiba dai qiris take jira ya bata takardarta ta yi gaba.
Su na zaune a cikin wannan hali sai wayar Khamis ta xauki ruri, ya qi ya amsa sai Sahiba ta harare shi, Iziddin ma hararar yake jefa masa, tabbas sun fahimci mai kiransa a waya Zahida ce babu tantama. Da Khamis ya ga ba sarki sai Allah sai ya amsa kiran da aka damu ana ta tayi, yana xauka ta fara magana basu ji me take cewa ba amma tabbas sun jiyo muryar mace ce take magana. Shi dai sun ji amsar da ya bata ya ce "meya faru aka kore ta?"
Iziddin ya gasgata maganar Aljanna, Zahida ta ke yi masa.
Khamis ya sake cewa "tunda haka ne ya zo ya kaita in da yake mana." Iziddin da Sahiba suka haxa ido gaba xaya suka juyo suka dube shi sai ya katse wayar, ya miqe tsaye.
Ya juya ya dubi Sahiba ya ce "daman kin ce anan za ki yini ko? Zan dawo da yamma in mayar da ku gida."
Sai ta zabura ta miqe tsaye a fusace ta ce "qafata-qafarka ko mu yini anan tare ko mu koma gidan mu yini tare."
Amatullah ta ce "haba Sahiba ya haka ne wai? Me yake faruwa?"
Sahiba ta surnano da hawaye ta ce "Amatullah ba zaki gane ba ni nasan abin da yake nufi, ni ya zo ya jifge ni anan gidan kamar wata banza shi ya shiga gari yana yawo ko."
Sai mamaki ya kama Amatullah da Nauwara suka rasa abinda take nufi da wannan kalamai na ta. Ya za'ayi ta ce duk in da mijinta ya saka qafa sai ya tafi da ita, a ina ake yin haka?
Nauwara ta ce "au yini a gidanmu shine aka zamar da ke banza, ya za'a yi kuwa ya zo ya yini a cikin mata? Kin san dan Iziddin bashi da lafiya ne da tare zasu fita su bar mu a cikin gida."
Iziddin ya miqe a sanyaye ya dubi Sahiba ya faxa cikin murya ta bada umarni yace "Sahiba koma ki zauna akan kujera, kada ki tayar da hankalinki ki barshi ya je da yamma sai ya zo ya xauke ku xin, babu komai."
Ta koma ta zauna tana huci zuciyarta na tafasa. Mamaki ya hana Khamis yin magana, hararar Sahiba kawai yake yi,
Iziddin ya dafa kafaxarsa, ya ce "wuce ka tafi uzurinka kada ka damu da hayaniyar mata, dan Allah."
Khamis ya ce "au! Dan kin samu ma na fitowa unguwa da ku har abin ya zama haka? To ki sani, kuma ki rubuta ki ajiye, yau 14 ga watan 6 2014 yau ce ranar qarshe da kika fito unguwa a wannan shekarar sai dai ki fito bada yawuna ba."
Sahiba ta ce "bismillah mu zuba."
Iziddin ya raka Khamis bakin mota yana bashi haquri shi kuma yana ta faxa da kumfar baki yana ta jero masa qarairayi akan abinda yasa Sahiba ta ke yi masa wai kishi ne dan ta ji zai auri Izzatu.
Wayarsa ce ta ci gaba da qara Iziddin ya leqa ya hango sunan mai kira 'Sahiba 2' amma da dan rainin hankali ya ce masa Sahiba ce mai lambobi 2.
Khamis ya xauka da sauri bai bari ta yi magana ba ya ce "na ce maka gani nan zuwa, ina hanya."
Ya juyo ya kalli Iziddin ya ce "Haruna ne dillalin nan da na ce zai nuna min filin siyarwa a Kubuwa, shine zan je in gani. Ka san na faxa maka na fi so in yi gini kafin in auri mata biyu ga yara a gidan haya ai ba daxi. Gara in gina vangarorin mata biyu kamar yadda kayi xin nan."
Iziddin ya turo baki ya gyaxa kai ya ce "hakan ya yi daidai. Allah ya taimaka."
Khamis ya shiga motarsa ya tafi yayin da Iziddin ya shigo gida ya kalli Sahiba, ta kalle shi ya yi mata magana da ido alamar zasu yi maganar nan gaba. Nauwara da Amatullah suna ganinsa suka kawar da kai gefe babu mai kallon fuskarsa, har ya wuce cikin xakinsa, alwalla ya xauro ya kama hannun xansa Faruk suka tafi masallaci, basu dawo ba sai da yamma liqis. Har yanzu dai Sahiba da matansa suna zazzaune a falo suna hira, daga ganin hirar ta yaqe ce babu wanda ransa yake da daxi. Ya wuce xaki jikinsa a sanyaye, Amatullah ta xaure ta tashi ta zubo masa abinci a filet ta bishi xaki ta kai masa yana rawar jiki ya karva yana ta godiya, ta buxe firij ta xauko ruwan sanyi ta ajiye masa a gabansa nan ma godiyar yake yi, ta vata fuska babu walwala a tattare da ita, ta fice ba tare d ace masa uffan ba. Ya dinga tura abincin nan badan yana jin daxinsa ba sai dan kada ciwo ya dame shi, ya gama ci, ya sha maganinsa ya miqe qafa ya yi zaman davaro a qasa kansa a sunkuye a qasa ya rasa abinda yake yi masa daxi a duniya, haqiqa rayuwarsa ta gama wargajewa tunda Amatullah matar da tafi kowa sonsa ta fi kowa yarda da shi yau tafi kowa zarginsa da rashin yarda.
"Allah Ka fitar da ni daga cikin wannan masifa, abu sai gaba-gaba yake qara yi." Ya faxa a bayyane ya yin da qwalla ta cika masa ido.
Ya ji ana kiran magaruba, ya tashi ya yi alwalla ya fito babban falo ya iske babu kowa a falo sun shiga xakunansu dan yin sallah, sai ya wuce masallaci anan ya yi sallar magriba da isha'i sannan ya dawo gida. Akan 'darning table' ya iske su dukkansu da yara suna cin abinci.
Amatullah ta yi qarfin hali ta qirqiro murmushin dole ta ce "Abban Faruk! ka qaraso ga kujerarraka mu ci abinci." Ba dan ransa yana so ba sai dan ya kasance mai laifi baya so ya qara yin wani laifi, ya zo ya zauna suka haxu aka ci abinci tare. Nauwara dai ta dage gaba take yi da shi ko kallon in da yake bata yi har Sahiba ta kula da hakan. Ya gama ci ya tashi ya shiga xaki ba tare da ya cewa da kowa uffan ba, yana shiga xaki ya kashe fitila ya kwanta ya xora hannu aka ya yi kuka ya gaji yana mai addu'a idan masifar nan mai qarewa ce Allah Ya kawo qarshenta cikin gaggawa, idan kuma ba mai qaraewa ba ce Allah ya yayyafa mata ruwan sanyi, ko Allah Ya xauki ransa ya huta. Bayan ya mutu gaskiya sai ta bayyana.
Amatullah ta shigo xakin ta kunna masa fitila, ya buxe ido ta lura idanuwansa yayi jajawur saboda tashin hankali ta yi kamar ta ji tausayinsa sai ta tuna da kalaman da ta ji yana furtawa wata sai tsanarsa ta dasu a ranta.
Ta tsuke fuska ta ce "Khamis ya dawo xaukar iyalansa bai shigo ba yana cikin mota ya ce ta fito su tafi. Za ka fito kayi masa sallama ko kuwa ba zaka fito ba?"
Ya girgiza kai ya ce "ki bawa yaranta Naira dubu ashirin ki ce ta saya musu alewar makaranta, ni na kwanta."
Ta kashe fitila ta fice.
Yana kwance yana kallon agogo har qarfe goma sha biyu da rabi na dare, gidan ya yi tsit da alama kowa ya kwanta. Sai ya tashi ya saka riga da wando qananan kaya na tsukewa, ya xauko mukullin mota ya fito yana tafe yana sanxa a hankali yake buxe qofar dan kada 'yan gidan su ji motsi su farka. Ba tare da ya san Amatullah tana lave a jikin labule qofar falonta tana kallonsa ba, tabbas ta lura club xin zai je. Saboda haka mijinta ya tabbata tantirin xan bariki ne ashe bata bava sani ba sai yanzu hali ya fito. Da ta rabu dashi taga iya gudun ruwansa idan ya dawo sai ta ji qaryar da zai shirga mata kuma ta sake tuhumarsa da laifin qarya amma ta ji ba zata iya daurewa ba, sai da ta da ya buxe motarsa zai shiga sannan ta yi wuf ta fito da sauri.
Ta ambaci sunansa cikin kuka mai firgitarwa "Iziddin ina zaka je da tsohon daren nan?"
Ya firgita da ganinta, jikinsa har tsuma yake yi muryarsa na karkarwa, ya ce "zan je in da kika ji na yi alqawari zan je xazu."
Ta dafe qirji ta ce "Izddin ni kake faxawa za ka je club wajen karuwa da bakinka?"
Ya ce "zan je wajen Aljannah in taimaka mata saboda tana cikin matsala." Aljannar ashe ba 'yar mutunci ba ce da baza'a same ta a gidan iyayenta ba sai a club?"
Ya girgiza kai ya ce "bata da gida a club ta ke amma ba karuwa ba ce. Za ki ji labarinta idan har kina buqatar ki ji kuma kin yarda za ki yarda da duk abinda zan faxa miki."
Amatullah ta fashe da kuka ta ce "bana buqatar jin wannan bauxaxxen labari marar tushe, ba zan tava fahimtarka ba. Ka ci amanar gaskiya da yardar da na riqe ka da ita."
Ya taho a fusace ta zaci marinta zai har ta tsugunna ta kare fuska, sai ya fisgo hannuta, ya ce "ki zo mu je in da zan je sai ki ganewa idanuwanki abinda nake aikatawa."
Ta fisge hannunta ta ce "wallahi ba zan bika club ba, Allah ne shaidar ka." Ya fara tafiya da baya, ya ce "na ji daxi da kika faxi haka, Allah ne shaidata kuma Shi zai fitar da ni. Na yi alqawari zan je wajenta in taimaka mata shiyasa na qi fasa zuwa, dan idan na fasa zuwa za ki qara zargina ki ce dan na san kin ji abinda nake faxa kunya ta hanani zuwa. Tabbas zuwa Hotel cikin dare kuma cikin club babu tantama sai 'yan iska amma ni a nawa vangaren ba abinda yake kai ni ba kenan, kuma na san ba mutuncina ba ne tabbas nima ba'a son raina nake zuwa ba dole ce ta kama ni. Na yi miki alqawarin yau shine zuwana na qarshe ba zan sake zuwa ba har abada in sha Allah, kuma ko da ace baki ji ba wannan qudiri yana raina daga yau b azan sake zuwa ba. Da za ki taimaka min ki taimakawa marainiyar yarinyar nan da sai in kawo miki ita gidan nan ki riqe ta har Allah Ya bata miji ta yi aure. Saboda ba ta da in da zata je, babu uwa, babu uba, babu dangi, 'yar tsuntuwa ce."
Amatullah ta ji tamkar ashar yake qunzuma mata, gaba xaya maganarsa a rainin hankali ta xauke ta sai ta sake fusata. ta ce "ba zan riqe 'yar kowa ba, sai dai ni ka kore ni ita ka saka ta a gidan. Na sake tabbatarwa ba ka sonmu yanzu, na tabbatar Aljanna ta juyar maka da tunaninka gaba xaya duk duniya ita kake so har baka kunya da jin nauyin nunawa duniya kana tare da karuwa. Wa'iyazu billah! Yau me nake gani da idanuwana, wanne irin bala'i mijina yake so ya jefa ni? Gara mutuwata da ganin wannan takaici a rayuwata."
Ya juya ya shiga mota da sauri ya tafi a fusace.
Amatullah ta fashe da kuka ta shigo falo da gudu a gigice, sai kawai ta yi kicivus da Nauwara a lave a jikin labule, idanuwanta itama a cike da hawaye. Matuqar razana Amatullah ta yi tana qoqarin goge hawaye ta qirqiro dariya dan kada Nauwara ta gane, sai Nauwara ta nuna mata ai ta gama jin komai kada ma ta voye mata.
Su ka zauna su ka yi tagumi hawaye ne kaxai yake kwaranya daga idanuwansu.
Nauwara ta sharce hawaye ta xago da jajayen idanuwanta ta kalli Amatullah ta ce "sarkin biyayya, sarkin sauqin kai, sarkin zaqewa da shaidar mijinki. Yanzu kin gani da idanuwanki ko? Iziddin ya zama abin tsoro, ba zan sake yarda da shi ba kuma ina nan ina jiransa gobe za'ayi ta ta qare daman xana xaya da shi zan tafi da xana iyayena zasu iya riqe ni su riqe shi. Daman Laurat ta yi min hannuka mai sanda rannan dan ta lura Iziddin yana hana ni harka da ita ta nuna min varo-baro duk abinda take yi na bariki da yake nisanta ni da ita shima yana yi kuma ita ganau ce ba jiyau ba, sannan ta faxawa qawayena komai sun xan voye min ne amma na fahimci wata magana cikin magana da suke yarmin akan in nutsu dai in san halin mijina, shiyasa kika ga na qi yarda da shi har ina tunanin rabuwa da shi. Bari ma in shiga in fara haxa kayana yanzu wallahi ba zan zauna ba."
Ta tashi a fusace ta shiga xakinta, yayin da Amatullah ta xora hannu aka tana runguza kuka kira ta ke "wayyo Allah ga marainiyarKa, Allah Ka duba ni, Allah Ka dubi maraicina Ka rufa min asiri. Ina zan saka raina yau a duniya?Allah Kai ne gatana, Ka duba min mijina, Iziddin ya zama abinda ya zama. Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."
Iziddin ya na tafe a mota hawaye kawai yake kwaranya daga idanuwansa gaba xaya zuciyarsa tafasa take yi, ji yake yau bai qi duk abinda zai faru ya faru ba. Ya shiga cikin Hotel a guje har said a masu gadi suka razana, ya sami waje ya tsaya bai damu ya lulluve motarsa ba kamar yadda yake yi ada dan kada a gane shi, a buxe ya bar ta kowa ma ya gan shi xin. Sai me? Ai babu abinda ya yi saura tunda Amatullah ta gane shi matar da duk duniya tafi kowa yin AMANNA da kyawawan halayensa. Yau ba zai canja kama ba ma a haka zai shiga ciki gara kowa ma ya shaida shi, har gaban Zahidah da Khamis zai je kuma zai tabbatar musu ya san komai, ya gaji da zurfin cikin da ba zai tsinana masa komai ba sai halaka, kuma kunyar marar kunya asara ce.
Ya isa a lokacin da aka fara shishshigowa, qarfe xaya dai-dai ya tunkari qofar shiga xakin kixan. Disko ne kawai yake tashi kamar kunne zai tsage, sai ya ja ya tsaya cak a bakin qofar yana tunani
'Abinda ya tuna shine Aljannah ba zata yarda ta tsaya da shi da wannan kamar ba, a waccan kamar ta 'yan caburos ta yarda shi mai taimakonta ne amma da wannan kamar take ganinsa a gidan Zahidah. Ita da Zahidah gaba xaya gudunsa suke idan ya je gidan, Aljanna ta xauke shi a mugu.'
Sai ya fasa shiga ciki, ya juya ya nufi kantin sayar da kaya a inda ya sayi hula da gemu da qaton gilashi ya saka, ya fito ya shiga ciki. Yana ta dube-dube bai ga wanda ya sani ba, sai ya zarce kai tsaye zuwa wannan fadar da su Zahidah suke zama. Ya tarar dandazon jama'a, yau taron kamar ya fi na kullum kasancewar asabar ce babu aiki gobe. Ya dinga tura kai har sai da ya shiga inda manyan suke zaune akan kujeru, ya iske wasu mutane ne daban babu Zahidah, babu Khamis a cikinsu balle ya ga Aljannah. Ya sake komawa cikin masu rawa da shaye-shaye, ya ci gaba da duba su tabbas babu idon sani har Na'if da Laurat ma bai gani ba yau. Sai ya tuna fa ya cewa Aljanna ta xauko tasi ta zo zai biya, ko suna waje suna jiransa dan haka sai ya fito farfajiyar Hotel xin yana duba ta, ba ta nan.
Ya zaro wayarsa ya duba babu missed call ko xaya, sai ya ji zuciyarsa ta qeqashe babu tsoro, babu kara, gara ya kira Khamis su yi abinda zasu yi a raba garin kowa ya kama gabansa. A fusace yake sai huci yake, ya ci sa'a wayar kuwa ta shiga.
Khamis ya amsa waya a fusace shima yana huci, ya tambaya "waye yake magana?"
Sai tambayar ta bawa Iziddin haushi matuqa ya zabura ya ce "au baka san mai kira ba ma ko? Saboda idanuwanka sun rufe."
Khamis ya yi ajiyar zuciya ya ce "oh! Sorry ashe Iziddin ne na gane muryar. Wallahi ina cikin masifa da tsakar daren nan gaba xaya screen xin wayar a fashe take, bana ganin suna. Sahiba ta farfasa wayar da kayan gidan nan gaba xaya kamar wata zautacciya saboda tsananin kishi. A garin fashe-fashen ma ta yanke hannu ta gurxe qafa gamu a asbiti ana yi mata xinki, likita ya ce ta samu hawan jini ya kwantar da ita. Ga ni a asibitin ni kaxai da yara suna ta kuka babu macen da zata taimaka mana. Na rasa yadda zanyi in kira wayarka ko ta Amatullah Screen baya nuna komai kuma ni ban haddace lambobinku da ka ba, ita kuma wayarta ma ba'a ga in da ta jefa ta ba balle in kira ku da ita. Gara da Allah Ya sa ka kira ni, dan Allah ka xauko Amatullah ta zo ta taimake mu ko ku bamu aron mai aikinku xaya ta zo ta zauna da yara a gida. . ."
Iziddin ya sauke waya a hankali daga kunnensa sannan ya katse, ya faxa a bayyane "kowa tasa ta fishshe shi Khamis."
Ya na juyawa sai ya yi kicivus da Aljanna ta taho a sukwane gudu-gudu sauri-sauri, da alama shi take ta nema afujajan. Tana ganinsa ta fara murna ta durqusa ta gaishe shi, ta ce "ga mai tasi can a wajen get an hana shi shigowa da motar, akan Naira dubu huxu ya kawo ni saboda ina da kaya da yawa a hakan ma daqyar ya yarda."
Iziddin ya tsaya kawai yana kallon bakinta, sai ya maimaita abinda ta faxa ya ce"kaya! Kaya wanne iri?"
Ta yi shiru saboda matuqar razanar da ta yi, fargaba ta kamata dan kada ya ce bai san zancen biyan kuxi ba koma ya ce ba shi ne suke waya ba ma gaba xaya.
Sai ta ja da baya cikin sanyin jiki muryarta na karkarwa, ta ce "da kayana na taho akwatuna 3 ne, kai ka ce in zo da tasi zaka biya kuxin mota. Ka taimaka min dan Allah babu in da zan je tun da safe a bakin hanya nake zaune wajen wata mai sayar da abinci. Ka kai ni inda za'a riqe ni."
Sai ta durqusa a qasa tana hawaye.
Iziddin ya ji hankalinsa ya tashi ya ce "miqe tsaye meye abin kukan?"
Jikinta yana rawa ta miqe tsaye tana sharce hawaye, ya saka hannu a aljihu ya zaro kuxi naira dubu huxu ya miqa mata, ya ce " ki je ki biya mai tasin kuxin ki kwaso kayan, kiyi sauri kada ya gudu da kayan."
Ta karvi kuxin ta tafi da sauri, yana wajen ya kasa tsayuwa a waje xaya sai zurga-zurga yake yi a farfajiyar, ya je ya dawo, ya koma ya dawo ya rasa abinda yake yi masa daxi a duniya, bai san yadda zai yi da Aljanna da kayanta ba yau.
Sai ga Aljanna ta rugu da gudu wajensa a gigice tana kuka, ta ce masa "mai tasin ya gudu da kayana na fita ban ganshi ba."
Iziddin ya harare ta ya ce "ke kar ki raina min hankali fa. Da man baki san shi ba baki haxa shi da kowa ba kika shigo kika bar shi da kaya a mota?"
Jikinta yana ta karkarwa, muryarta tana rawa ta ce "eh, ban san zai gudu ba an hana mu shigo cikin get sai na ce ya tsaya a gefen get zan karvo masa kuxinsa shine ya gudu da kayana gaba xaya. Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un. Yaya zan yi da rayuwata, a ina zan saka raina?"
Ya daka mata tsawa a fusace, ya ce "ke! ki rufe min baki, ba ke kaxai kika shiga masifa ba. Mutane nawa kika jawowa bala'i da kike wannan kururuwar dan an sace miki kaya? Ba nauyi aka rage miki ba? Ina zan kai ki da kaya riqi-riqi? Gara ma da ya yi gaba da su, Allah Ya saka miki a lahira."
Sai Aljanna ta tsagaita da kukan tana kallonsa cike da mamakin jin kalamansa. A tunaninta sai wanda bashi da imani ne zai ji masifa ta sami musulmi xan uwansa ya ce Allah Ya qara, gara ma da aka yi haka. Amma da ta tuna a in da ta san shi sai ta daina mamaki daman watsatstse ne a wajen watsewa suka haxu, dan haka imaninsa dole mai rauni ne.
Ya juya ya fara tafiya yana karkaxa mukullin mota, ya ce "ki biyo ni mu tafi ko kiyi zamanki anan ni dai yau ne rana ta qarshe da za ki qara haxuwa da ni a wannan waje."
Nan ma ta kasa fahimtar abinda yake nufi, tana kyautata zaton ko a buge yake dan haka ta fara kokonton binsa. Tana ta sanxa tana tafiya kamar bata so, salati kawai take jerowa ta tabbatar rayuwarta tana cikin haxari idan ta bi wannan halittar, Allah ne kaxai Ya san hannun da zai jefa ta. Idan ya waiwayo ya dube ta sai ta ja da baya idan ya juya ya ci gaba da tafiya sai ta ci gaba da binsa a baya. Har suka isa wajen motarsa ya buxe ya shiga ya zauna ya buxe mata gaban mota sai ta tsaya daga nesa tana fargabar shiga motarsa.
Ya na kallonta tana kallonsa babu wanda ya yiwa wani magana har fiye da mintina 5, ya gaji da jira sai ya daka mata tsawa, ya ce "Ke! In za ki shigo ki zo mu tafi, kin bar ni da qofa a buxe fitilar mota a buxe kowa yana wucewa yana kallona. Idan kina jin tsoron zan cutar da ke to kada ki biyo ni zan ja motata in tafi amma kada ki kuskura ki qara kirana a waya dan kina tayar min da hankali da fitina a cikin iyalina."
Sai ta shigo motar a tsorace ta zauna ta takure a jikin qofa, ya kunna fitilar mota haske ya bayyana, ya sa hannu ya yaye gashi da gemun da tula ya wurga ta wundo, sai ga fuskarsa ta bayyana nan da nan ta tuna in da san shi. Za ka iya jin qarar ajiyar zuciyarta tun daga nesa. Su ka hau kallon-kallo tsakaninsu idan ka kalli idnuwan Aljanna a wannan yanayi sai ka rantse mujiya ce aka jefa a cikin kwalba, aka rasa wanda zai yi magana a cikinsu. Ya ji an qwanqwasa masa wundon mota, ya juya da sauri sai ya haxu da wata gagarumar faxuwar gaba tun daga saman kansa har qafarsa ya ji wani abu ya tsarga masa.Ya gigice ya fita hayyacinsa yana ganin abinda idanuwansa suka nuna masa, ashe a baya ba tashin hankali ya gani ba yanzu zai adar da ya shiga bala'i. Sai ya rasa addu'a xaya da zai furta duk sun gushe daga qwaqwalwarsa, ya buxe baki kawai yana kallo. Jira kawai yake ya ji an tashe shi daga barci idan ma mafarki yake yake yi, sai ya ji daxi a ransa amma abu ya faskara tabbas a ido biyu neb a mafarki ba.
Alh. Jibrin, surikinsa kuma a shugabansa a wajen aiki, Alh. Abbas qanin Alh. Jibrin da kuma Na'if ya gani a tsaye akansa.
Na'if ya zabura ya nuna Iziddin da hannu ya ce "yauwa ai ba ni kaxai ba ne nake kwana a club, har da surikinku da ku ka xauki dokiyarku amana ku ka bashi, gatan duniya babu wanda baku nuna masa ba, ni xanku ku ka hana ni ko kobo, shine na kira ku ku zo ku gani da idanuwanku."
Alh. Jibrin ya yi shiru yana kallon Iziddin kawai fuskarsa cike da damuwa mai tsanani, sai Iziddin ya sunkuyar da kai qasa saboda kunya.Ya yi saranda babu wata dabara ko wayo da zai harhaxo ya wanke wannan baqin tabon da ya damvaru a jikinsa.
Na'if ya tsugunna ya xauki hular gashin da Iziddin ya jefar a qasa ya xaga sama, ya ce "ga irin hular da yake sawa ya canja kama ba'a gane shi kullum yana zuwa shekara da shekaru sai kwanan nan na gane shi, a cikin Hotel xin nan na tava kama shi ya cire gashin da sassafe ya fito, anan ya kwana kuma da karuwai yake kwana. Kalli waccan tsigigiyar yarinyar da ya xauka zai tafi da ita xaki na santa a club xin nan gata nan a qanjame, kowa ya san qanjamau ne da ita. Da ita yake kwana dan haka ta shafa masa qanjamau kuma ya shafawa Nauwara 'yarka mace kwaya xaya kacal da kake ji da ita Daddy."
Sai Aljanna ta zabura ta dafe qirji ta ce "subhanallahi! Ni ce mai qanjamau? Na shiga uku."
Ta xora hannu aka ta kwalla ihu.
Iziddin ya zabura ya daka mata tsawa ya ce "rufe min baki, idan kika sake yin magana sai na make ki. Ki yi ta karanta Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un kawai."
Alh. Jibrin ya yi doguwar ajiyar zuciya ya riqe baki ya sunkuyar da kai qasa, ya gyara tsayuwa yana gyaxa kai da alama mamaki ne ya addabe shi.
Alh. Abbas ya ce "Wa'iyazu billah! Iziddin abinda Na'if yake faxa gaskiya ne ?"
Iziddin ya girgiza kai ya ce "ba gaskiya ba ne Alhaji . .."
Alh. Jibrin ya zabura a fusace ya katse shit un bai qarasa magana ba ya ce "Abbas dan me zaka vata bakinka wajen tambayar gaskiya? Ba wani ba ne ya baka labari ga abu muna gani varo-varo. Allah Ya tona asairinka Iziddin, ina ganin ma ka daxe kana cuta ta a ofis ganewa ne kaxai ban yi ba. Idan da gaske ka xauko qanjamau ka sakawa 'yata wallahi sai na yi qararka a kotu, mutumin banza mayaudari."
Iziddin ya girgiza kai dan takaici, bai iya xaga idanuwansa ya kalle su ba, balle ya yi magana .
Idanuwan Alh. Jibrin suka yi jajajwur muryarsa na rawa saboda tashin hankalin da ya shiga, ya ci gaba da cewa "Iziddin ka sani ba mu ka zalunta ba kanka ka yiwa."
Alh. Abbas ya ce " Na'if! Ko da shi ku ka raba dalolin da ka satowa Daddy ka?"
Iziddin ya xago da kai da sauri ya dubi mai magana sannan ya juya ya kalli Na'if, yana jira ya ji amsar da zai bayar.
Na'if ma ya tsare Iziddin da ido, ya cije baki ba kunya ba tsoron Allah ya ce " Eh mana! Da shi muke rabawa, na bashi."
Wannan sharri ya fi vatawa Iziddin rai, ya ji kamar ya fito ya shaqe shi sai ya haqura ya ci gaba da sauraron yadda Allah Zai yi dashi. Wannan bala'ai da ske ta rikito masa ya san wata babbar jarabawa ce daga Allah. Ya na addu'a Allah Ya bashi nasarar tsallake ta.
Alh. Jibrin ya xauko wayarsa hannunsa na karkarwa ya kira lambar Nauwara.
A lokacin da Amatullah ta shiga xakin Nauwara tana roqarta ta yi haquri ta daina haxa kayanta kada ta tafi daidai lokacin wayar ta shigo sai gaba xayansu suka tsurawa wayar ido cike da fargaba. Cikin sanyin jiki Nauwara ta xauko wayar a tunaninta zata ga lambar Iziddin.
Sai ta ga lambar babanta, ta zabura ta amsa, a firgice ta tambaya, "Daddy mutuwa aka yi ka kira ni da tsakar dare?"
Ya buxe muryar a fili (hand's free) yadda Iziddin zai ji komai, ya ce " a'a ba mutuwa aka yi ba. ina mijinki?"
Sai ta jawo Amatullah ta buxe muryar (hand's free) suka durqushe a qasa suka saka waya a tsakiya suna karkarwa haxe da zafafan hawaye.
Nauwara ta xora hannu a kai ta rusa kuka, ta ce "baya gida. Me ya faru da shi?"
Alh. Jibrin ya ce "gashi nan ina tare dashi, lafiyarsa qalau. Amma ina so ki haxa kayanki kakaf gobe da safe zan zo in xauke ki."
Ta sake fasa kuka ta ce "A club ka ganshi ko?"
Mamaki ya kama Alh.Jibrin ya ce "ashe ma kin san a club yake kwana amma baki tava faxa min ba. Gashi nan tare da Na'if na zo na rutsa su. Tun jiya a garin nan nake neman Na'if bam u gan shi ba sai yau, ya sace min daloli sama da bandir goma. Na sami labarin a club yake kwana shine muka biyo dare muka zo muka cafke shi, ya kasha kuxin saura kaxan aka samu a wajensa, shine yake faxa min bashi kaxai ba ne mai zuwa club har da Iziddin. Da ya faxa min ban yarda ba har da hotunan Iziddin ya nuna min da ya xauke shi bai sani ba a club, ya saka gashi ya canja kama na ce qarya ne ba hoton Iziddin ba ne dan Iziddin ba zai tava aikata wannan baxalar ba, ba halinsa ba ne. Allah cikin ikonsa sai ya nuno mana motar Iziddin, muna qarasowa muka tarar shine xin ne shi da gashin da yake sakawa hard a wata . . . ga su nan dai abin sai addu'a kawai."
Nauwara ta fashe da kuka ta ce "wallahi zaman da shi ya qare, Daddy ni tafiya zan yi."
Ya ce "ki ma daina ratsuwa ni ne fan a kira kin a ce zan zo in xauke ki, ki yi haquri har zuwa gobe da safe zan zo gidan naku da kaina, karki damu komai ya zo qarshe."
Su ka kashe waya, Iziddin ya runtse ido sai hawaye ya surnano daga idanuwansa, ya girgiza kai.
Tunda Amatullah ta xora hannu akai ta tsugunna bata qara miqewa tsaye ba har ta gama jin abinda suke faxa a waya. Nauwara ta qare mata tsiya ta fito daga xakin tana sanxa ta fito babban falo ta zauna, zazzavi ne ya rufe tad a ciwon qirji, Nauwara kuwa da qarfin gwaiwarta ta ci gaba da haxa kayanta har da labulen xakin sai da ta sauke su qasa.
Alh. Abbas da Na'if suka gama cashewa Iziddin suka qara gaba daman Alh.Jibrin bai sake cewa komai ba tunda ya kashe waya ya yi gaba. Su ka tafi suka bar shi a zaune kamar gunki. Aljanna tana ta makerketa kuka ya tunkaro mata, tsoro ya hana ta rusa, tasa hannu ta toshe baki dan kada ta varke.
Iziddin ya yi shiru ya kasa xaga hannuwansa balle ya yi tuqi, ya qara gyara zama ya riqe kai, bakinsa ne kawai yake motsi da alama addu'a yake yi. Aljanna ta laluba murfin mota ta buxe ta fasa kuka ta yunqura zata fice da gudu sai ya damqo gashin kanta, nan da nan tayi cara kai kace rai zai cire mata.
Ta faxa a gigice "ka rabu da ni, in tafi ko halaka kaina ma in yi. Ina zan saka raina?"
Ya daka mata tsawa ya ce "ko ki zauna ko in tsinka miki mari kuma idan kika qara fita daga cikin motar nan sai na fasa miki baki."
Ta zauna ta rufo qofar mota amma sai ta maqale a jikin qofa tana ta kuka. Ya yi shiru sannan ya yi ajiyar zuciya, ya juyo ya dube ta, ya ce "ina kike so in kai ki yanzu?"
Ta girgiza kai ta ce "so nake ka bar ni anan?"
Sai ya harare ta ya ce "a Hotel xin za ki zauna?"
Ta gyaxa kai ta ce "eh."
Ya ce "wajen wa?"
Ta yi shiru tana ta kuka, bata bashi amsa ba.
Ya ce "Allah Ya na tare da mai gaskiya ba damuwa Allah zai fitar da mu. Ki daina tsorona ba zan cuce ki ba in sha Allah. Idan da ina goyon bayan iskanci Zahida ba zata dinga guduwa ba idan ta ganni. Dan haka ki saka a ranki babu abinda zan yi da ke, ba kece a gabana ba, matana biyu sun fi ki komai. Ina tausaya miki ne kawai nake so in taimake ki, amma ki tabbatar abinda kika faxa min gaskiya kike faxa ba qarya ba, kuma ina fatan ba Zahida ba ne suka turo ki dan ki zo ki yaudare ni."
Ta zare ido dan mamaki, ta girgiza kai.
Shima ya zare mata ido ya ce "Eh mana. Muddin na gane haka ne babu abinda zai hana in maka ki a kotu a xaure min ke. Ga shi nan yanzu kin ja sunana ya vaci, na rasa zaman lafiya a gidana, aka bibiya ma sai na rasa matana gaba xaya."
Jikinta ya yi sanyi bata ji daxin abinda ya faxa ba hawaye kawai take ta surnanowa. Amma ta xan ji daxin wasu daga cikin kalamansa da ya ce iskanci baya gabansa, kuma ita kanta ba ta yi masa ba matansa sun fi ta. Tabbas daya fito da kamanninsa ta shaide shi ba xan iska ba ne, ta xauke shi dai marar mutunci marar taimako. Yanzu kuwa ta gasgata ya fi kowa tausayi da taimako sai ta fara tsagaitawa da kuka. Abu xaya take kokonto aka shine idan ba iskanci ba me ya kawo shi Hotel gidan rawa? Akwai alamar tambaya akan wannan batu, gashi kuma har surikansa sun zo sun ritsa shi a gabanta suna tuhumarsa da sata da bin karuwai. Amma kuma haqiqa ta san qarya ne, tunda da ita aka yi masa sharrin iskancin alhali shi ko kalmar soyayya bai tava furta mata ba, hatta kamanninsa na asali ma bata sani ba sai a yanzu.
Ya fara tuqa mota yana tafiya a hankali har ya fito daga get xin hotel, yana tafe akan titi yana layi, gashi dare ya yi sosai. Ya juya ya kalle ta haushi kawai take bashi, ba Zahidah ba ce ta jawo masa vata suna ba, ita ce ta vata masa suna. Ko da yake ya yi imani komai rubutacce ne a wajen ubangiji ita ma Aljanna ba yin kanta ba ne.
"Haka Allah Ya qadadara min." Iziddin ya faxa a bayyane.
Aljanna ta matse hawaye ta ce "Allah Ya dafa mana, Ya fitar da mu daga cikin quncin nan."
Sai ya ji tausayinta ya kama shi, ya ce "amin. Ke! Wai ina zan kai ki ne?" Ta yi narai-narai da ido ta ce "Anti Zahidah ta ce ka kai ni gidanka, can zaka kai ni sai in dinga yiwa matarka wanke-wanke."
Haushi ya kama shi bai san sanda ya taka burki a tsakiyar titi ba, ya juya ya galla mata harara, ya yi qwafa ya gyaxa kai sannan ya ci gaba da tafiya.
Ya ce "kina da hankali kuwa? Ashe daqiqiya na xauko ban sani ba? In kai ki gidana in ce na kawo musu wa? Ki na ganin baban matata abinda ya ke faxa a gabanki. Hotel zan samu mai araha gajab xan in ajiye ki."
Ta zaro ido ta dafe qirji ta ce "Hotel?"
Ya ce "idan ban kai ki can ba gidan wa zan kai ki? Ki xauka qaddara ce ta hau kanki zamanki a Hotel kina mace, musulma kuma yariya qarama. In kin ga dama ki kama kanki ki zauna a waje xaya, idan kin ga dama ki fita ki gudu ni dai taimakon da zan iya yi miki kenan kafin in san in da zan kai ki. Kuma idan abu ya faskara sai in kai ki gidan marayu ko in kin ji wuya tai she ki sai ki faxi gasakiyar inda kika fito, dan ban yarda da ke ba ma gaba xaya."
Ta qif-tqif-ta idanuwa zata yi kuka, ta dai ta daure dan kuka ma zai yi mata magani ba.
Ya juya kan mota ya nufi wani Hotel da yake nesa da gidansa, kai tsaye ya saka kan motar a bakin get xin, masu gadi suka taso da sauri suka buxe musu ya shiga. Ya sami waje ya ajiye motar, ya juya ya harare ta ya ce ta fito su shiga, ta fito a tsorace tana tafe tana sanxa, ta ji a ranta kamar ta gudu kar ta shiga ciki dan tsoro take kada ya ce a xakin shima zai kwana saboda dare ya yi sosai ba zai iya komawa gida ba.
Ya wuce ya yi gaba abinsa da ya ga bata da niyyar shiga, idan ta gama shawara da zuciyarta ta biyo shi. Ya shiga receiption ya iske ma'aikata biyu mace da namiji bayan sun gaisa ya tambaya. Ko akwai xaki? Suka tabbatar masa akwai sannan suka zano masa kuxaxen xakuna daban-daban. Akwai na dubu biyar, dubu bakwai da na dubu goma. Ya zavi na dubu biyar, a take ya biya na sati xaya, sannan ya tambaya ko akwai Hotel xin yana dafa abincin siyarwa (restaurant).
Su ka ce "akwai."
Ya juya ya kalli Aljanna, sai ta ja da baya a tsorace.
Ya harare ta, ya yi mata tsawa ya ce "ki matso ki faxa musu irin abincin da kika so safe, rana da na dare har na sati guda."
Jikinta na rawa ta matso suka miqa mata doguwar takarda aka jero sunaye abinciccikan, ta zazzava, nan ma ya biya kuxi masu ya yawa.
Ya juyo ya kalle ta ya ce "sai me kuma?"
Ta gyara tsayuwa ta ce "ba ni da komai kayan sakawa, brush, makilin. turare da . . . . ."
Ba ta gama zanowa ba ya katse ta ya ce "ke! Ya isa haka dalla malama. Gidanki ne da zaki tara musu shirgi?"
Ya miqa mata naira dubu goma ya ce "ki riqe wannan, gobe da safe ki tsallaka shagunan bakin titi ki siyo duk abubuwan da zaki buqata. Idan da wata matsala ki ari waya ki kira ni ai kin haddace lambata, idan babu wata babbar matsala kada ki kira ni. Dan kiran wayarki yana jawo min matsala a gidana."
Ta gyaxa kai, ta duqa ta yi godiya.
Ya juya ya kalli ma'aikatan hotel sun bi layi sun yi carko-carko suna kallonsu, zuciyoyinsu cike da kokonto da zargi kala-kala.
Ya ce "ga qanwata nan, ku kula da ita marainiya ce, ku tausaya mata."
Sai gaba xaya suka langwabar da kai suna faxin "ayah, sannu."
Matar ta dafa kafaxar Aljanna ta shafa, ta xauko mukulli sannan ta ja hannuta zuwa xakin da suka bata. Hawaye ya fara kwaranya daga idanuwan Aljanna ta fara tausayin kanta da kanta, ta waiwayo ta kalli Iziddin shima ya kalle ta, sai tausayinta ya kama shi, ya yi sauri ya sunkuyar da kai qasa hawaye ya cika masa ido.
Ya juya ya fice da sauri ya nufi wajen motarsa, ya buxe zai shiga sai ya ji magana daga cikin wata baqar mota da take gefensa, ya firgita da ganin mutane da ya gani. Har ya fara tunanin ko qwaqwalwarsa ta zautu ne gezau idanuwansa suka fara yi masa. Direba ne yake tuqa motar, Na'if a zaune a gaban motar ya yin da Alh. Jibrin da qaninsa a zaune a kujerun baya, ya sake gani sun biyo shi a baya dan su tabbatar da inda ya kai karuwarsa ya voye.
Na'if ya yi magana a fusace ya ce "nan ka kawo ta ka voye dan ka ga an gane ka a wancan Hotel xin ko? To mun biyo ka a baya mun ga komai Allah Ya tonu asairainka."
Alh.Jibrin ya yi shiru yana hararar Iziddin kawai, ji yake kamar ya fito ya shaqe shi, ya kashe shi kowa ma ya huta. Ya fusata ya ce da direba "Ibrahim ja motar nan mu tafi gida kawai."
Alh. Abbas sai girgiza kai yake yana faxin "Allah Ya sawaqe maka Iziddin, Allah shirye ka Ya sa ka gane gaskiya."
Na'if ya ce "in me shiryuwar ne ba, amma idan ba mai shiryuwa ba ne Allah Ya wargaza shi."
Alh.Jibrin ya ce "Kai! Dalla ka rufe mana baki kai da shi ai duk jirgi xaya ne ya kwaso ku xan iska kawai."
Direba ya juya kan mota ya fice suka bar Iziddin a tsaye ya daskare kamar qanqara, ya rasa yadda zai kwatanta wannan savani da yake ta afkuwa a jere- a jere kamar wanda wani daraktan fim ya tsara a wasan kwaikwaiyo.
"Allah mai yadda ya so da bawanSa. Ni Iziddin ni ne na zama haka marar mutunci a idanuwan matana da surukaina." Iziddin ya faxa a bayyane.
Yayin daya sulale ya zauna akan kujerar mota, ya gagara saka qafafuwansa a cikin motar balle ya tuqa. Idan ma ya fita ina zai je da tsohon daren nan? Ya tabbatar bala'i kawai zai je gida ya tarar na Nauwara, ya san Amatullah ba zata ce masa komai ba sai dai ta yi ta kuka amma hawayenta ba qaramin dafi ba ne a cikin zuciyarsa.
A haka ya kwana har aka kira sallar assalatu, ya ta shi daqyar ya fito daga motar bai damu ya kulle ta ba, haka ya bar ta da mukulli a jiki ya fice ta get da qafa ya shiga laluben daga in da kiran sallah yake fitowa a cikin unguwa.
MU HAXU A
AMANNA
KASHI NA
BIYU
ABIN TAMBAYA ANAN SHINE:
*Shin yaya rayuwar Iziddin zata kasance anan gaba: tsakaninsa da matansa, tsakaninsa da sirukinsa, tsakaninsa da Aljanna, tsakaninsa da khamis, tsakaninsa da Zahidah?
*Shin wai wacece Zahidah, menene alaqarta da Iziddin daya damu da ita yake bibiyarta har yake kishi da Khamis?
*Shin menene asalin labarin Aljanna, da gaske take bata da iyaye ko qarya ta ke yi masa kawai?
*Shin yaya zata kaya tsakanin Iziddin da Khamis, anya zai ritsa shi da Zahida ko haka zai ci gaba da zurfin cikin?
*Shin yaya rayuwar auren Khamis da Sahiba zata kasance zasu gaba ko zasu rabu?
*Shin Iziddin zai bari Khamis ya auri qanwarsa Izzatu?
Amsoshin wannan tambaya suna nan tafe a cikin littafin
AMANNA
kashi na
2
daga
JUT.