page 9

92 0 0
                                    

*THIS NOVEL IS DEDICATED TO BARRISTER BILKISU GARBA*

*GABA KURAA*

     *NA SADNAF*


*Page 9* 

      Jafar Kankame Ishama da Hisham yayi a  kirjinsa kamar zai Maida su cikinsa yayi matukar kewarsu da ji yake kamar yayi hauka saboda rashinsu.

A jiya suka gama da case din kayan da ya bata na company da yake wa aiki.

Kaya ne na millions of Naira da shi Kansa bai san ya akayi kayan suka bace ba hakane yasa aka hau zargin ko shine.

Haka suka ringa zuba case da Mai gidansa.

Aka ringa bincike abinda ya hana shi dawowa kenan dan ba dama ya dawo har sai an gano gaskiyar lamari.

Yana can ne amma zuciyarsa na wajen yaransa sai yake ganin kamar suna cikin damuwa dan ko Yaya ya kwanta sai yayi mafarki dasu.

Idan bai yi dasu ba zai yi da kudirat tana kuka

Idan ya tashi haka zai tsinci Kansa cikin damuwa har sai ya kira Balaraba a waya ya tambayeta lafiyar yaran.

Duk da tana hada su a waya haka yake fama da tunanin yaran dan gani yake kamar Balaraba ba zata rike su yadda yake so ba.

A karshe sai da duk abinda ya tara ya biya kudin kaya aka Kuma sallame shi daga aiki.

A yanzu ba shi da ko sisi duk kuma bashi ne damuwarsa ba burinsa kawai yaga ya dawo yaga yayansa da sune duniyarsa,su yake gani yaji Dadi.

"Ina Siyama yace yana cika su Ishama ya hau kalle kallen ta inda zai ga Siyama da yake masifar so a cikin yayansa bai sani ba ko dan tana kama da kudirat ne tafi shiga ransa.

Ishama na k'ok'arin bashi amsa cikin sabbin hawayen daya Kara zubo mata na Siyama da take tunanin ko bata tayi shi yasa har yanzu bata dawo ba.

Balaraba ta fito daga dakinta da sauri daya hannunta rike da hijabi ta ari tashin Hankali ta Yafa a fuskarta tana "Abban Ishama tun da Rana Siyama ta fice har yanzu ban ga ta dawo ba yanzu haka ita zan je nema ba inda banje nemanta a makota ba"

Jafar sakin hannun su Ishama yayi cikin faduwar gaba ya Kalli Balaraba dake a hargitse tana saka hijabi Yana "Bangane tun dazu ta fice  ba Ina taje"

"Titi na aiketa fa kayan Miya kawai na saka ta siyo min,dan kaga Ishama idan ba makaranta ba,ba inda take zuwa.

Shi ma Hisham ba aikensa ake ba kaga yayi kankanta ma toh Aiken ma wallahi ni nake kayana yau tsautsayi yasa ni aikenta kaga shiru har yanzu ban ganta ba"

Ta karashe tana satar kallon hisham da Ishama da ta musu gargadi da idonta.

Jafar kuwa bai iya magana ba yayi waje cikin tashin hankali akwai gajiya a tare dashi sosai.

Amma rashin ganin Siyama yasa ya nemi gajiyar da ya kwaso ya rasa.

Balaraba kuwa bayansa tabi bayan ta bugawa Ishama da Hisham gargadi data ga Jafar ya fice akan kar su sake su fadawa Jafar Aiken Siyama tayi ta karbo mata Sako

Dan Sam bata so Jafar ya gane ma Haj Naja tazo gidan dan idan har yasan ma ita tace Siyama tabi kawarta asirinta zai iya tonuwa.

Jafar ba inda basu zaga ba a unguwar suna tambayar Koda akwai Wanda yaga Siyama amma shiru duk Wanda suka tambaya sai suce basu ganta ba.

Balaraba har da kukanta wiwi tana ta shiga uku.

Yadda take kuka yasa Jafar hankalinsa Kara tashi dan da dukan alamu dai Siyama bata tayi.

Sai gasu sune har station da gidajen radio sun bada cigiyar Siyama dan Jafar gida ya koma ya d'auko wani Karamin passport dinta ya kai station da gidajen radio.

GABA KURAA Where stories live. Discover now