YAR ADAMAWA cplt story

6 0 0
                                    

life story...

Baƙuntace ta kai ni jahar Adamawa gidan wani abokin mahaifina. Bari dai kuji yadda labarin ya samo asali.
Sati na ɗaya da kammala jarabawar fita daga matakin secondary sai mahaifiyata ta sanar dani cewar gobe zamu tafi Adamawa, saboda tsabar zumuɗi haɗe da yarinta a wannan ranar da maurna na kwana domin nasan a lokacin shekaruna ba wasu masu yawa bane.
Mahaifina ne ya jamu a motarshi domin jagorantar tafiyar, da isarmu Adamawa bayan naci abinci na ƙoshi sai ɗaya daga cikin yaran gidan mai suna Faruq ya jani waje domin yawatawa.
Bayan munyi yawanmu mungaji sai mu dawo gida mu zauna a ƙofar gida domin shan iska.
Jim kaɗan da zamanmu sai faruq ya tashi ya shiga wani gidan da yake kusa da nasu gidan, ganin hakane yasa nima nabi bayamshi, bansani ba ashe tsokanace ta kai shi gidan.
Da shigarshi sai ya fusge sweet daga hannun wata yarinyar da shekarunta basu yawaita ba yai waje da gudu.
Ganin yadda na saki baki ina kallan yarinyar ne yasa mahaifiyar yarinyar tayi dariya haɗe da cewa "lafiya kuwa?
Sai nace "ai naga ya ƙwace mata sweet ne ya gudu kuma ta kasa buɗa baki tayi magana kawai ta bishi da kallo.
Sai mahaifiyar yarinyar tace "to yazatai dashi dama kullun idan bai sata kuka ba bayajin ɗadi gashima har ta saba da abun da yake mata.
Nan take na ciro #100 daga aljihuna na bata haɗe da cewa "kije kisai wata kuma idan ya kwace miki ki fadamin.
A wannan lokacin ji nayi kamar kar na fito daga gidan saboda tun da nake a rayuwata ban taɓa sanin menene kyau ba sai a lokacin da nayi ido biyu da yarinyar da faruq ya kwace ma sweet.
Ga fuskarta cif-cif, hasken fatarta dai-dai musali, idanunta yan madaidaita gasu farare tas, haɓarta abar burgewa, kai da ganin gashin kanta kasan yarinyar ta musammance, gata ƴar ɗas da ita.
Bayan ta siyo sweet ɗin sai tazo ta zauna kusa dani haɗe da yima faruq gwalo.
Satinmu 1 a Adamawa amma duk da kasancewata mai makatsaitun shekaru hakan bai hana fadeela shiga zuciyata ba.
Bansani ba ashe nima nayi nisa a tata zuciyar kuma ban tashi gane hakan ba sai a lokacin da tafiyarmu tayi nisa....... Click this link to read complete story
👇
https://kotunmasoya.blogspot.com/2024/06/yar-adamawa-complete.html

YAR ADAMAWA cplt storyWhere stories live. Discover now