PAGE 4

267 22 3
                                    

*_♡LAST EMPRESS♡_*
      Historical fiction hot romance story
_Mai_Dambu_
Wattpad:Mai_Dambu
Arewabooks:Mai_Dambu41
Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu

The journey of a miles is begins with a single step.....✨

https://whatsapp.com/channel/0029VadYczJLY6d8BbzsbY0s
*MASU NIMA DAGA FARKO DON ALLAH GA LINK NAN SU SHIGA ZASU SAMU* 👆

______________4

Sosai dare ya raba, yayinda barci barawo yayi gaba da kowa. A bangaren Maina wani irin wahalallen barci yake me cike da tashin hankalin, domin kuwa kamar a mafarki kamar a zahiri yake ganin wani irin halitta yana kaiwa Aliyah hari, amma bai same ta ba, shi kuma yana rike da wani irin bulala da zaran abin ya kawo mata cafka zai zuba mishi duka.

     Kad'a fukafiko abin yayi tare da girgiza Maina ya zube can, tsalle abin yayi tare da dirka akan cikin Aliyah. Ihun da tayi yasa duk suka farka, sai a lokacin ya shiga karanto Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, yana yi yana nanatawa, d'ago ta yayi yana kallon fuskarta da take zufa kamar ana gasata.
"Aliyah?" Ya kira sunanta tare da d'agota,  bude idanu tayi tana kallonshi. "Papan twins lafiya?" Ta faɗa tana kallonshi. Ganin babu wani abu a tare da ita yasa shi sauke ajiyar zuciya, ya zare ta a jikinshi yana tab'e baki. Kamar bai damu ba nan kuwa damuwa ce cikin ranshi.

"Zuwa gobe ku tattara, Haisam zai kai wuce daku Scotland." "But why?" Juyawa yayi cikin duhu, ya zuba mata idanu. So yake ya tambayeta yaushe ta fara mishi musu, amma sai ya cije lips ɗinshi ya mike tare da shiga ban daki, yayi alola sannan ya dawo ya kwanta a dogon kujeran dakin, ya tsani musu da taurin kai, shi yasa basa shiri da Bahi domin ta cika taurin kai. Juya mata baya yayi abin shi.
    Kwanciya tayi tana ji a ranta ba zata bar garin nan ba, ta gaji da yawo da ita da Maina yake, ko shekaru uku ba'a yi ba, yanzu ya sake kirkiro zuwa wani wurin ita km ba zata ko ina ba,wallahi gara ya sake ta zata huta.
              Tana wannan tunanin barci ya ɗauke ta, sai wurin Asuba ciwon mara haɗe da tsinkewa jini ya tashe ta lokacin Maina ya tafi masallaci. Ita daya tayi ta birgima sai wurin 6:45 ya shigo lokacin da ya shigo ta suma.  Farar Jallabiyar jikinshi da ya je sallah da ita bai ko cire ba, ya d'auketa a stairscase ya hadu da Amra da Kukun dinsu cikin yanayi mara dadi ya ce musu. "Ku saka idanu akan Yaran!" Ya wuce da ita, tun kafin ya fita Amra da Kukun sun isa bakin kofar suka bude mishi kofar,  security din gida da kullum suke jiran ko ta kwana suka bude mishi motar da take gaban gidan, ya sakata ya shiga gaban, drivan ya figi motar a haukace, don ko Maina bai furta mishi kome ba, yasan kan aikinshi a zamanshi da su na tsawon shekaru.
                     Koda suka isa asibitin, karban gaggawa aka musu kasancewar Asibitin na royal family ne, ba na kowa da kowa ba ne,  kafin wani lokaci doctors biyu da nurse biyar ne akanta, kamar wasa sai da gari yayi haske har wurin 9:26am, mota Ammar Wazir da Salahudeen, "Maina wani b'arin ne?" Murmushi yayi me ciwo domin dai yana wani daki ne na daban, haka yasa suka shigo.
"Na je security suke gaya min kana nan." Inji Ammar, shaf ya manta da wayarshi, hannu ya saka cikin aljuhun rigarshi ya ce. "Muje Palace!"
"A haka?".inji Salahudeen.  Haɗe rai yayi tare da nufar hanyar waje, da sassarfa Ammar ya bi bayanshi. "Look Maina." Yadda yayi wani kicin-kicin da fuska yasa Ammar Wazir ya ce mishi. "Ina tare da duk abinda xaka zartas"
"Ban gane ba"
"Muje!" Ammar ya tura Salahudeen.
"Kai ban fahimci kome ba"
"Muje dai!" Ammar ya kara gaya mishi.
"Na gaji!"
"Kayi min shiru ka biyo ni" Maina ya daka mishi tsawa, yadda yayi tsawan yasa hatta likitoci da nurse da wasu marasa lafiya, kamewa domin kaf Baihak ba a tab'a jin yayi faɗa ba, yana daga cikin manya mutane da suke da daraja Baihak kuma ake ganin girmansu, haka yasa baka jin ko motsin kowa domin tsawar da ya dakawa Salahudeen, shugaban rundunar sojojin tsaron fadar da kasar, yasa aka kashe tvs da takaita zirga-zirga, sannan wadanda suke tsaye suka zube kasa, tare da sunkuyar da kansu. Wannan tsawar tasa Salahudeen ji kamar zai mutu. Maina ya kunyata shi a gaban jama'a.
     Suna fita suka bude mishi mota, ya shiga tare da jingina kanshi a jikin motar, haka suka nufi Palace, duk da babu wanda ya kawo Maina zai shigo masarautar da karfe goma na safe haka, sun san karfe tara yake shiga sannan zai fita karfe tara da rabi, duk yawan maganar da zai yi yana bata minti ashirin ne zalla.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 25 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

LAST EMPRESS ||FREE BOOK Where stories live. Discover now