Meerah P1

13 0 0
                                    

Zaune nake a dakin Yaya ta na hade kaina da gwiwa Ina rusar Kuka Mai cike da kunci da tarin fargaban me yake shirin faruwa dani in akace na sake rasa wanda nake burin da gama tsara rayuwata dashi,a karo na ba adadi na daga kaina,na tambayi yaya ta dake zaune bisa kan gado tana rike da wayarta tana dannawa.nace yaya haryanzu inna tambayeki meye yake faruwane kince baki sani ba in jira mama tazo naji,kuma naji Aunty beeyah tace mun maganar aure nida daddy babu shi,cikin gunji da dacin rai nace me hakam yake nufi,umh shine abunda ta furta ta cigabada da danna wayarta.nikuma na cigaba da kuka na  kasa kasa ina fatan da adduar  ba abun da nake fargaba  bane ke shirin faru.
   Cikin wannan yanayin danake na tsinci muryan Mama Tana sallama,Nan take bugun zuciyata ya tsanan ta bansan dalili ba,suka gama gaisuwa da yaran Yaya ta da suke zaune a pallor,ta karaso cikin daki ta zauna akan kujerar da ke gaban gadon facing me,Nan take nadago kaina Ina kallonta hawaye na zuba daga idona,dakyar na iya dariya na bude baki na ce"Mama Ina yini" tace mun lapia ke Kuma kukan me kikeyi.fashewa nayi da wani sabon kukan na fara cewa Mama dazu nace ma Yayan mu gobe Daddy zai turo kudin sa auren mu Amma tace injira zuwanki muji me ake ciki,cikin kaguwa da fargaban son jin abunda ke faruwa nake jiran inji abunda zatace,saina tsinkayo muryarta cikin kunnena tana cewa wani sadaki kuma bayan an yanke hukunci,ko bakiji abunda aka bin ciko a game dashi bane?ras naji gabana ya fadi nace shknan abunda na jima ina boyewa a game da Daddy ya fito,amma saina dake nace me kuma aka binciko aka samu Mama ??.

rayuwar meerahWhere stories live. Discover now