Ina tambaya Sai tacemun taoh an binciko an samu Kuma Shi Dan shiaa ne,nan nayi salati jikina yadau rawa nafara tunanin daga ina kuma waye ya samo wannan bayanan,cikin dakiya na aro karfin jiki na sanya ma kaina na fara magana nace Mama ai ni nadade da sanin dan shiaa ne ya fadamun tun farko kuma be boyemun ba,sai tace amma shine baki taba fadama kowa ba ?nace eh Mama tsoro da fargaban irin wanna rana ya hanani.
Cikin Nuna rashin Jin Dadi abunda na fada Mama tace taoh ai shknan yanzu kinji abunda yake faruwa saikiyi adduaa Allah ya zaba Miki Wanda ya fishi,Dan ni a tunanina Dan shiaa da Christian duk daya a yanda na dauka,ban San sanda nace Mama Dan Allah kiyi hakuri wallahi ni naji nagani Banda matsala da akidarsa inasonsa a haka,kuma karku manta shima fa musulmine ya amsa kalmar shahada yana Kuma yin sallah azumi da zakka,cikin tsawa tace mun taoh saikiyi kuma ki kira Babanku yace zai yi magana dake nace toh cikin kuka muryana ya kakkarwa,ta ce Allah ya kyauta Sai kiyi hakuri ta karasa maganan tana mikewa ta nufi hanyar fita,Yayarmu dake kan gado ta sauko domin yi mata rakiya,nikuma nan take na sake fashewa da wani matsananciyar kuka nace ni Mariya na shiga uku wannan shine karo na 5 danake rasa wadanda nake so kuma nayi burin gina rayuwar aure mai cike da so da kauna amma yana rushewa ya zanyi,cikin wannan tunanin na jawo wayana dake gefen saman dressing mirrow na fara lalubo numbern Baba na wanda duk tsawon shekarun dana fara rike wayana shine karon farko da zan kirashi.
Ina Danna Kiran,bugun uku a na hadu ya dauka,gabana Yana faduwa na aro jarumta na sanya tareda fara yin ssllama,nace Ina wuni Baba?lapia ya amsa a takaice nace am dama Mama ce tace na kiraka wai kace zamuyi magana nayi maganan a rarrabe saboda firgici da damewa danayi,Sai naji yace eh bata fada Miki abunda yake faruwa bane,cikin Saudi da magana a hankali nace eh Baba kawae tace na kiraka ne,Sai ji nayi ya hau fada Yana cewa karya ta Miki kenan bayan tace kunyi magana dazu,Sai na bude baki nace eh munyi amma kuma cemun kawae tayi AI an binciko an gano Daddy Dan shiaa ne,Sai yace ohk Amma kince bakuyi magana ba ya Kara da cewa me meyesa kike da karya ne,nace ba karya nayiba ban fahimci akan haka kake tambaya ba shiyasa nace bamuyi ba,yace toh kin deji yanzu me kika yanke,nayi jimm kafin na iya bude lebba na na sama da kasa inajin suna mun nauyi nace eh naji komai amma ni Baba ban ga aibuba tunda de kowa akidarsa zaiyi Kuma bai boyemun ba AI ya mutuntani,cikin tsawa Baba yace taoh mu Bamu yardaba mun ga aibu Kuma inaso ki fadamai ya dakata ba maganan auren tsakaninku,nace kayi hakuri kafin na kara wani magana ya katse kiran.nan na sake rushewa da wani kuka numfashina na sassarkewa zazzabi me zafi take ya rufeni,ina kwance na daddage dakyar na dauki wayana na sake lalubar numbern Daddy bugun farko ya daga yace my daughter zan kiraki Ina Dan aiki NE bani 40mins-1hr haka,Yana shirin katsewa ne nace Daddyna Akwae matsala,naji yayi salati yace ohk lemme call u back,yayi ending Kiran.
Immediately ya kirani yace my daughter yanzu Kuma meye ya sake faruwa nace daddy shknan an gano kai Dan shiaa ne yace taohhh🤔Sai Kuma yace taoh Sai meya faru,cikin Kuka nace Baba yace bazan aureka ba yace in fada Maka Nan yayi salati Yana hadawa da innalillahi wa inna ilaihi rajiun,meye ya faru har ya kawo baka shine tanbayar da yamun?nace Daddy ban sani ba yace taoh barin kira Addana ko na barta nace eh karka kirata pls yanzu komai a hargitse yake,nayi ending call din ya sake kira buh i couldn't pick,the anger, anguish and shock i was in at that moment yasa na gagara daga wayar,nayi mai text kamar haka"Daddy na no matter what pls be wit me karka barni,i love u more than anything more than anyone ni naji ko a yaya kake zan zauna dakai,after sending the text i switched off my phone but zazzabi sai ya Kara zama worst ina karkarwa na tashi na hau gado na dau duvet na rufu har kaina Amma komai ya wargaje na fara tunani take na sake dauko wayata da na kashe na kunna na kira waya friend Dina Ina Kuka nace,,,,,,,,,.