WAHALAR RAYUWA 5-10

711 23 0
                                    

UMMIN ABBATEE 😘

                 5~10

WAHALAR RAYUWA😪😪

WAYE
AFAF wato asalin sunan shine MUHAMMAD AFAF shine ake kiranshi AFAF  baban shi dan asalin garin sokoto itako mahaifiyar sa babanta dan birnin kebbi ne mamar ta kuma yar agadaz  nan ne tasamo asalin baiwar kyau saboda alabarin da mahaifiyar ta tabata shine mamar ta ita kuma yar kasar sudan ce...........sunan mahaifiyar AFAF Fatima mahaifin sa kuma sulaiman......sulaiman ya hadu da fatima ne awani bukin abokinsa da sukaje birnin kebbi tana cikin manyan kawayen amarya  itace babbar kawa ma dan ita akakira zama a high table wanda shikuma sulaiman ya zama babban abokin ango suka zauna tare dalilin hakan ne har sukayi exchangin numbers suna gaisawa akai akai bai wani mayar da  hankali akan taba saboda alokacin bashi da plan din yin aure anan kusa....akwai wata rana taje gidan kawar tata amarya suna zaune suna fira sai yakira mijin kawar yace gashinan yashigo garin zai biyo su gaisa yana sauri zai juya sokoto  ayau nan idris  ya fadama amarya Amina cewa ga babban aboki nan zuwa wato sly  dan sly suke kiran  shi tun a school nan amina suka shiga kitchen itada fatima dan hada abun tarban sly ita fatina batama gane wanene zaizo ba cos tana daki Fatima ta kirata......... bayan yazone sunata fira da  amina tashigo dakin da Fatima ke zaune tana jiran dawowan ta tafada mata zata wuce gida amina tace kai kawalliya kibari anjima mana tace aa gaskia  bari nayi sauri natafi kedai kar mama tajini  shuru tana fitowa palour suka hada ido dashi tace ina wuni  yace ahhh lafia kalau dama kina ciki tace eh zasu fitane amina ta rakata sai ya juyo yace badai har zaki tafi bane tace eh zan wuce tun dazu nake gidan ayya kalli agogon hannun sa yace to bari nazo na saukeki nima zan wuce kenan.......tace ayi haka kayi zaman ka kuyi firar ku bakomai nagode yace nooo ninace zan kaiki ay dama nima wucewa zanyi idris yace sly hooooow far sarar da sukeyi kenan tun a school idan wani yayi abun da basu ganeba instead sai suce howww far harda jan howwwww far din sukeyi......yace bana son iskanci fa yamike madam tnk u very much fa abinci yayi dadi ya ajiye 10k  yace ga shi  madam kisa credit ta ce harda walaha sly yace aykuwa ba wahala bane wannan irin  gara haka da aka hadamin  aynine ma nabaku wahala.......suka rakosu har bakin mota sukayi sallama......motar shuru sai kiraa dake tashi acikin motar nan yace hmm wannan irin shuru haka haba ke baki iya fira bane tayi murmushi tace to me zance malam sly yace kome kikeso ki fadi tace bakomai ma yace kinga niko akwai komai tace mefa yace hmmm gaskia nidai kamar ranar bukin nan banganki dakyau ba kallon tsoro nayi miki tace kamar yafa yace kamar ki tayi murmushi tace yauwa ina  nufin yanxu nafi ganin ki dakyau ashe haka kike kyakykyawa amma dai kin hada jini da larabawa  ko ta dukar da kanta tana murmushi tace aa yace muyi yar gaskia  dake yan mata tace shiga nan yace au ni ay namanta ma cewa ajiyeki zanyi agidan ku nazata har andaura sokoto zamu wuce tare tazaro idanu tace me aka daura yace um  um wai ke ba bahaushiya bace haba ina tayi miki kin kasa ganewa tace nikam ban gane ba kam kamin bayani yace ummh to gaskia nagani inaso ta ce me ka gani yace zankadediyar budurwa kuwa mai hankali ta fuske kamar bata ganeba tace a ina?yauwa kashiga left ga gidan muje mai icen umbrella a bakin gate yace ok baba nanan ne tace ahhh gaskia lokacin dawowar aa baiyi ba da saura yace kashhhh tace lafia kuwa yace ayda tun yanxu zanje nafara kai gaisuwa tace tame fa yayi parking daidai gidan tace nagode sosai sly Allah Ya tsare hanya zata balle murfin motar tafita yace fateeeema yanda yakira sunan yamata dadi sosai ta juyo ta kalli fuskarsa taga yayi  serious ya nutsu tace lafia kuwa yace Fatima inata miki bayani kinkasa ganewa haba fatee tace wane bayani kenna tana mai duba agogon dake manne ahannun ta tace magrif ta kusa kanaso kayi tafiyan dare ne yace bakomai nasa a ay pls fateema kibani hankalin ki  nan wallahi fateema bantaba son wata yarinya ba ni bana soyayya nasa ma raina cewa bazan taba soyayya dako wace mace ba sai matar aurena ko kinsan kuwa cewa har rokon Allah nake da karya samun son  kowace mace sai matar aurena? tayi dariya tace ahh lallai kai kuwa saboda me yace har sai kin tambaya ay bata lokaci ne wallahi yanxu dai Fatima gaskia nakamu da sonki alokaci daya wallahi tinda naganki a dinner inata jin Abu agame dake amma ina sharewa sai yau kawai naji kinkara shiga raina wallahi kowa zaki tambaya kije ki tambaya bantaba son ya mace ba tayi ajiyan zuciya hmmmm yace pls pls don't say no to me ta kalleshi tayi murmushi tace zanyi shawara tnx ta bude motar tafita yace Teema ta juyo yace pls teema kiyi tunani sosai dan Allah tace Allah yatabbatar mana da alkhairi yace amin........ya tsaya yana  kallon ta yace gaskia idan na auri wannan nayi dace ga hankali da nutsuwa ........Fatima kenan yarinya fara atsayi madaidaiciya hancin ta irin wannan ne dabaacika sabon halitta da irin shiba saboda dan karami ne kuma dogo wanda yayi daidai da tsukakken bakinta mai dauke da lebba jajaye ida idanuwa wadan da aka kira as sexy eyes farare kal shikam gashi baa magana tunda akace dangin buzaye ce......tindaga lokacin soyayyar fatima mai karfi takamashi kullum yana kan kiran ta amma takasa bashi amsa ita kuma tanaso tafara fadama Maman tane kafin ta bashi amsa dan itama gaskia sly ya burgeta.........

BY rukky😘

WAHALAR RAYUWA Where stories live. Discover now