باسم الله الرحمن الرحيم .
Allah ya bani ikon rubutun da zamu amfana, Ameen.
Kyautace ga duk masoyana.1
A hankali take tafiyarta hankalinta kwance, ta tura ƙofar ajinsu ta shiga ta samu wajen zamanta da ta saba zama a gaban aji, ta zauna.
Littafinta na ƙurani ta ɗauko ta buɗe inda taji ana karantawa cikin suratul Nisa'i.
Bata ankaraba taji saukar bulala a bayanta. A tsorace ta miƙe ta
damƙe bullarar, ta kalli mutumin da ya tsala mata bulalar, ta ƙara da "lafiya malan?"
"Ke baki da idanu ne har sai kin tambaya, ko bakiga sauran yaran ba, kowace a tsaye ta ke?" Ya fizge bulalar daga hannunta.
"Na gani amma ai ban san laifin da sukayi ba malan kawai sai in miƙe tsaye nima ba tare da nayi laifi ba" Lallai wanna malamin babu ko shakka sabon malamine, dan babu malamin da ya taɓa aza koda tsinke a jikin Hannan da sunan hukunci, ba a islamiya ba har ma boko. Sam bata son a taɓa lafiyar jikinta, hakan ya sa ta ke kiyaye duk wata doka da aka gitta mata.
"Mi sunan ki? Ya tambayeta tare da komawa wajen zamansa a gaban allo.
"Sunana Hannan AK" Ta amsa a taƙaice.
"Minene kuma AK? A dai-dai lokacin idanuwansu suka harƙe.
Ta ɗauke nata ta na tura baki ta na hura anci, idanuwanta suka ƙanƙance. Babu wanda bai san sunanta ba duk inda ta shiga. Bugu da ƙari bata son faɗin sunan mahaifinta kai tsaye. Amma da alama wannan sabon malamin ya fita tsaurin ido "Hannan Abdulkarim" Ta faɗa cikin ɗaure fuska.
"Laifinki na farko Hannan, shine zuwa makaranta ba a kan lokaci ba, na biyu na san irinku kan ku ba komai ciki sai daƙiƙanci da takkwalanci, dan haka kema sai ki miƙe tsaye kamar yadda sauran yaran su ka miƙe dan basu iya karatu ba" Ya ƙarasa maganarsa yana murmushin mugunta.
"Indai kace na makara zuwa, to na yarda, amma karatu kam har gaba da inda aka tsaya ma zan niya karantowa a hardace" Take ta kawo ayoyi goma da aka basu harda, sannan ta kawo tafsirinsu a taƙaice.
"Da ka yi rantsuwa malan da kayi kaffara, dan ban ji ka cini gyara ko ɗaya ba".
Malamin, bayyi zaton hakan daga Hannan ba, ba shiri ya ce kowaccensu ta zauna. Ya kalli Hannan yace "Hukuncin makarar da ki ka yi zai biyo baya" Ya kira ɗaya daga cikin malaman makarantar ya cigaba da koya ma su karatu, shikuwa ya bar ajin, a ransa ya na sake-sake. Wannan yarinyar ta raina ma shi hankali, har tana gaya ma shi magana. Amma dole ne ya samu hanyar da zai hukunta ta, dan dalilin makara kawai bai isa ya hukuntata ba yadda ya ke so. Sannan dan dai karatunta na yau bai isa ya sa ta cikin jerin wa'anda ya ke d'auka masu maida hankali ba na makarantar.
Fitar malamin dake tsare dasu keda wuya, Hannan ta tsinci sunan malamin daga ƴan ajinsu. Watau malan Lukman. Ƙawayenta Marwa da Halima (Sa'adiya), wanda kuma maƙotansu ne, suka lallaɓo zuwa gefenta.
Sa'adiya ta ce "Wallahi ƙawas kin taimaka mana yau, wataƙila da har a tashi muna tsaye".
"Indai ƙeta ce ba na biyunshi" Faɗar Marwa, yayar Sadiya.
Haka sauran ƴan ajin kowace ta rinƙa tofa albarkacin bakinta suna zagaye da ita, suna ƙara zuga ta.
"To wai yaushe ya fara koyarwa a wannan makarantar ne? Ni kam ban taɓa ganinshi ba ma" Hannan ta faɗa, ta na ƙanƙance idanuwa ta tsuke baki tana ƙara tuno yadda ya kirata daƙiƙiya, da yadda yasa ta faɗi sunan babanta, sam sai taji bata son shi a take.
"Ai da yake kina zuwa makarantar kwana, kuma yawancin lokuta kina Bakori, shima ba koda yaushe yake nan ba, shiyasa baku taɓa haɗuwa ba, da alama wannan ne karon farko da kuka taɓa haɗuwa" Sadiya ta faɗa tana dariya ta kai ma Hannan duka a baya cikin wasa.
Hannan ta tsala Ihu tana murza wajen, da malan ya duke ta.
"Kai Hannan wallahi kin cika raki, wannan ɗan dukan" Faɗar Marwa.
"Hmmm, Allah Ya sa ya ma ki irin bulalar da ya mani gobe" Ta faɗa.
"Mu kam ai mun saba" Marwa ta bata amsa cikin dariya.
Sauran ɗaliban makarantar ma dai malan Lukman ne hirarsu a ranar, kamar kowane lokaci in ya zo.
Ba ƙarya, ya kai cikakken matashin saurayi.
Kyakykyawan saurayi ne mai ɗan tsayi. Gashin kanshi kwance ya ke, wannan baya rasa nasaba da alaƙarshi da larabawa. Sajen fuskarshi yana ƙara ma fuskar yalwa. Hakanan bai cika yin dariya ba, amma baya ɗaure fuska, hakan ya yasa duk wanda ya kalleshi ba kasafai zai tunkareshi ba farat ɗaya. Mutunne mai kwarjini.Asalin kakanninsu Lukman larabawan ƙasar Yamen ne, amma ko iyayensu tun daga kan mahaifinshi dake babba a gidansu har ƙaramin ƙanenshi na bakwai cikin garin Kano aka haifesu. Wanda harkar kasuwanci yasa su ka yi kaka gida a garin. Iyakarsu da Yamen baifi suje hutun ƴan kwanaki ba zuwa sati biyu, duk bayan shekaru biyu, har girmansu. Har yakai ga an had'a auren zumunci tsakanin iyalansu, inda babanshi Alhaji Muhammadu, mai lakanin "Balarabe" da ƴar kawunsu, Haj KHadijat. Hakan yasa su kansu su Lukman a Kano su ka tsinci kansu.
Yanzu haka Lukman ya gama makarantarshi da ya bashi matsayin dacta fannin ilimi a wata jami'ar kasar Saudiya, (watau education), ya dawo gida ne da niyar hutu kafin ya koma ya cigaba, dan ya riga ya samu gurbin cigaba da karatu a wani fannin kuma. Haka Allah ya yishi da son karatu, da rubuce -rubuce, haka kuma ya na son duk wani mai son karatu. Yawancin lokuta yana hukunta k'annenshi musamman Marwa da Sa'adiya, a cewar shi sun cika wasa da karatu. Hayatuddeen da Shamsuddeen yan biyi ne su ne ƙanana a gidan su Lukman. shekaru ne kusan goma tsakanin Lukman da mai bi mashi Marwa. Inda ita kuma Marwa ta ba Sa'adiya kusan shekaru biyu. Marwa ta gama sakandari a wannan shekarar, Sa'adiya na aji biyar sakandiri, su kuma yan biyu su na aji biyar makarantar firamare.
Lukman kan ɗauki lokaci bai zo gida ba, dan iyayenshi na yawan kai ma shi ziyara, dan yawanci in su ka je azumi, to sai bayan sunyi aikin hajji su ke dawowa. Ya kan samu ƴan aiyukan da ba'a rasa ba na koyarwa a can ɗin lokuta da dama. Haka kuma, duk sadda ya samu zuwa gida yakan yi koyarwa a wannan islamiyar wadda ta ke mallakar mahaifinsu. Hali ɗaya dake gareshi shine, ya na bi duk ta wata hanya da ya sani don cimma gurinshi. Sai dai kuma baya tsallake maganar iyayenshi. Hakan na matuƙar ƙara mashi kima a idonsu.
Sai dai daga Lukman har Hannan ba su taɓa sanin juna ba, duk da kuwa maƙotakar da suke, kuma ƙannenshi biyu Marwa da Sa'adiya duk ƙawayenta ne. Kasancewar duk sadda zaizo ita kuma tana makaranta, ko gidan kakanninta hutu. Kila yanzu ma sa'a akaci ta zo hutu mai ɗan tsawo, bayan gama aji uku makarantar gaba da firamari, watau (jss 3).Ɗan buzu dillali, shine lakanin Alhaji Abdulkarim Sadi. Wanda shima asalin iyayenshi buzayen garin Agadas ne a k'asar Niger. Bayan rasuwar mahaifinsu da daɗewa ya sayar da dabbobinsu, da su ka had'a da shanu da raƙumma ya shiga harkar kasuwanci, daga baya harkar tashi tafi karfi ta ɓangaren saye da sayerwa, na filaye da gidaje. Tun suna zaune a garin Bakorin jihar Katsina, inda ya auri mahaifiyarsu Hannan, Hajiya Aisha, har kasuwanci ya bunƙasa ya koma Kano da zama. Suka yi maƙotaka da Alhaji Balarabe, domin sun kasance abokan juna kuma abokan kasuwanci.
Shekarun Hannan kusan goma sha huɗu, itace yarinya ta biyu a cikin jerin ƴaƴan gidansu su biyar. Maimunatu wadda suke kira Bebi, itace babba kuma ta bata shekaru uku, itama yanzu haka ta zana jarabawar ta ta ƙarshe a sakandiri (SSCE). Tare suka taso kuma su na son junansu sosai, kasancewar Hannan nada dan girman jiki, in ka gansu tare ma kana iya ɗauka itace yayar Maimunatu.
Maimunatu da Hannan duk a can Bakori suke makaranta a makarantar gwamnatin tarayya dake garin.
Sun shaku sosai da kakanninsu musamman ta wajen mamansu da suke kira da Goggo, ita kuma ta wajen babansu Hajiya Malka, sukan kirata da boss, in suna jin tsokana, dan ba wanda ya isa ya tsallake maganarta.
Hannan, itakam, kusan fiye da rabin rayuwarta a Bakori ta yi ta, tun daga yaye.Shiga gida tayi ba tare da sallama ba, da alama tayi zurfi wajen tunani. Hakan ya sa mahaifiyarta ta dafa ta a kafaɗa hakan ya dawo da ita cikin hankalinta, ta kalleta tayi murmushi. "Lafiya ba sallama" Komawa tayi baya kamar zata bar gidan sannan tayi sallama cikin fara'a. Mama tayi dariya mai sauti sannan ta amsa. Aje jakarta tayi tsakar falo, tabi mamanta kicin, inda suka iske Maimunatu tana tu'kin tuwo. Ta bude firij ta ɗau ruwa ta kwankwada.
"Hummm, wallahi Bebi gara da ba ki je makarantar nan ba, yau na sha bulala" Ta fad'a a dai-dai lokacin da ta aje robar ruwan da ta gama sha.
"Mi kikayi?" Ta tambaya cikin murmushi da zakuwar jin labarin.
"Humm, wani sabon malamine sunce haka yake da zafi, amma ni kam ya gama dukana in sha Allah, dan indai zuwa kan ka'ida ne to zanyi, in karatu ne kuwa duk randa na san ma ban iya ba, ba zan je ba kar rana ta b'aci, dan ni kam bana son duka wallahi" Ta bata amsa.
"Ai kuwa baki isa ba, dole ne ki je makaranta, in bokone za ki ce ba za ki je bane? Gara ma ki dage yarinya, ba dai nan gidan ba" Mama ta fad'a.
"Haba Mama kin fi so in je a tsatstsaleta ni, wallahi mugune malamin, ni dai na san da ba a duka makarantar" Ta faɗa ta na tura baki kamar zata yi kuka.
"Ai gara ya gyara maku zama, kila kowa ya shiga hankalinshi, da yawanku ba abunda kuke ko islamiyar kukaje sai hira, sun mun dai-dai da suka kawo shi" In ji Mama.
"Nifa Mama kin san ina son islamiya, kawai dai in banyi laifi ba aka duke ni ai kinga ba a kyauta mun ba ko"
Haka dai Mama ta gwada ma Hannan ba ta da wata mafita sai ta je makarantar islamiya, kuma in tayi laifi ta goyi bayan a hukunta ta. Har aka kira sallar magrib sunanan a kicin suna muhawara kan duka a islamiya.
Sauran ƙannensu maza uku, Abdullah mai shekaru sha ɗaya, da Abubakar mai shekaru tara da Ahmad mai shekaru bakwai, suka barsu nan su ka wuce masallaci.
YOU ARE READING
NI CE SANADI
General FictionYa da qanwa ne, sun tashi cikin gata da kulawar iyayensu da kakanninsu. Sannan aqwai dangantaka mai qarfi tsakanin gidansu da maqotansu da ta zamana kamar y'an uwantaka. Soyayya mai qarfi ta kullu a tsakanin Lukhman da matarsa Bebi bayan aurensu. A...