*FAƊIME*
Kan Uba!
Uwale! Uwale!! Uwale!!!
Fito ki gani, fito maza ki ga abinda Faɗime ke yi.
Mtss! Uwalen daga ɗaki ta ja tsaki bayan ta ƙara miƙa kan gadon da ta haɗa shi da tarin tsummokara.'Allah ya yi dare gari ya waye, yanzu za a fara kiran mutum kamar wanda ya gille kan sarkin Mayu.'
Ta faɗa a zuci, sai kuma ta ɗaga muryarta.
"Wai me ya faru ne Hansa'u? Ba fa zan fito daga ɗakin nan ba idan ba kokon nan kika gama damawa...""Uwale wallahi fito ki gani Fadime ce ta yi kashi take lakace shi tana haɗiɗiya kamar sakin Ɗanwaken Kuluai..."
Ai kan ta rufe bakinta ta wuntsulo bisa gadon, zani yana kwancewa tana sake maidawa haka tayi waje tana kudunduma ashariya.Kai tsaye bakin murhu ta nufa ta sunkuci ruwan da za'a yi mata damun Kokon ta sheƙa ma hargitsattsiyar matsakaiciyar budurwar dake yashe a ƙasa tana damalmala ƙazantarta haɗe da tanɗe hannun.
Yarinyar ta fasa ihu bayan saukar ruwan a jikinta, kafin kuma tayi tsit sakamakon marin da aka bi ta da shi.
"Kwashe shi ki zubar masai shegiya mai siffar jakai, kwashe shi na ce dan kan lalataccen ubanki kanki aka fara hauka? Ki kwashe na ce tun kafin na sunkuta ki cikin rijiyar can na rantse da Allah!"
Yarinyar ta zuba mata ido tana sauke ajiyar zuciya kafin kuma ta kwashe mata da dariya, tana kai hannunta dake cike da kashi kusa da bakin Uwalen.
Baya ta ja da sauri tana waige- waige kamar mai neman madoki, sai kuma ta ji tsit yarinyar tabar dariya.
Duƙawa ta yi ta fara tattara ƙazantar, ta haɗa cikin hannunta ta miƙe tana yiwa Uwale murmushi kamar ba ta da wata matsala. Uwalen ma shiru ta yi tana kallonta ganin ta doshi banɗaki tamkar wata mai cikakken hankali. Sai dai kafin ta juya ta yiwa Hansai magana, yarinyar ta daka wata sufa ba ta zame ko'ina ba sai gaban Hansai dake juya kokonta da ta gama damawa. Ca6al, Haka ta watsa kome da ke hannunta bisa damammen zazzafan kokon, ji kake facal! Sai a fuskar Hansai.
Hansai ta zabura jin saukar zazzafan kokon bisa fuskarta, kafin kuma ta rarumi buta ta fara ɗauraye fuskar tana yi tana fidda kwallar azaba.
Baƙin takaici da ya lulluɓe Uwale shi ya hanata kataɓus ta tsaya tsai tana kallon Faɗime ta rasa wane irin hukunci za ta mata. Wannan Kokon burin da ta sha kansa yawa gare shi. Babban takaicinta da Geron da aka dama Kokon ma aronsa tayi a shago. Ita bata sha ba, ita da biyan bashi ke nan? Tuna hakan da ta yi ya sa ta rarumar Faɗime da bugu tare da luƙa-luƙan ashariya. Faɗime na ta kyakyata musu dariya abinta. Ganin hakan Hansai ma ta taho suka haɗu suna ta jibgarta. Sai dai fa kamar ƙara mata sautin dariyar suka yi, sai ma sune hannuwansu suka fara zafi. Abin da ya fusata Uwale ke nan ta danƙeta ta watsata ɗakin kajinta haɗe da garƙame kofar tana faɗin. "Wallahi ko Ubanki bai isa ya fidda ke ba idan ba kuɗin Gerona ya ba ni ba."
Hansai ta sauke numfashi tana duban Uwar ta ta, kafin kuma takai kallonta kan kokon da ya canja launi. "Uwale yunwa nake ji fa, ai duk ke kika ja mana. Na faɗa miki tunda kin samu cikar burin naki ta haukace ki fidda ta daga garin nan kinƙi. Wallahi watarana kina ji kina ganin abincin da zamu ci zai gagare mu..."
"Yi mini shiru da Allah can sokuwa kawai. Ke kinsan sakamakon da zan samu duk ranar da na wayi gari bata kwaryar ƙauyen nan? To bari ki ji, ke din da na ci burirrika kanki sai kin zama tsohuwar guzuma mai shekaru Hansin kafin ki auru, a hakan ma kar kiyi zaton abin arziki za ki aura. Kuturu shi ne mijinki, kuturun ma mabaraci me yawo da yagaggen wando. Dan haka idan har kika ga Faɗime ta bar ƙauyen nan to ba na numfashi ne a doron duniyar nan."
Hansai ta zumɓuri baki cikin ƙunƙune take faɗin. "To Uwale kinsan hakane ki kyale ta da lafiyarta mana, ina dalilin baɗi ba rai? Wannan abin fa da kika aikata daidai yake ace ki danƙi ruwa cikin tafin hannunki ki yi mintuna biyu da shi kacal ba tare da ya tsiyaye ba! Abu ne kinsan da ba zai taɓa yiwuwa ba dawwamarta anan ɗin me ya sa za ki yarda ki yi duk tarin waɗannan sharuɗan ? Haka ni fa ba zan iya zama gida ɗaya da mahaukaciya ba Allah ma ya sani. Kina gani rannan Takalmin sallata ta ɗauka ta yanka mini kamar ta samu nama. Idan ma ba mugun abu irin naki ba tunda kin samu nasara kan..."
STAI LEGGENDO
FADIME
AdventureFADIME "Wannan fa da kai na na jarrabata na ga aikinta, ka ga da fatar bakar kyanwar da bata bude ido ba aka yi rufin farko, sa'annan aka sake nad'eta da fatar d'an tayin cikin tunkiya, sa'ananan aka nad'eta da fatar bakin kumurci, sa'annan aka ke...