*FADIME*
_"Kafin sati ya kewayo shaƙuwa mai ƙarfi ta ƙullu a tsakaninsu. Kullum suna tare, idan ba ya gidansu da dare, to kuwa za ka tarar shi wurin sana'arta."_
_A sati na biyu da haɗuwarsu ya fara bijiro mata da batun aure. Shi fa zai zo gida kawai a tsaida lokacin biki. Dan kuwa duk sun gama shirin su da albarkar gonar gadonsu da ta rage musu.__Ita ɗin ma hakan take so kasancewar duk sa'anninsu sunyi aure dama. Sai dai fa ba yadda za a yi a tambaye ta ba tare da Uwale ba. Dan haka ta samu uwar Uwalen ta faɗa mata kome dan a aikawa Uwale wannan fa da ta ce a riƙe mata shi ɗin so yake ya fito._
_A sanda Uwale ta samu saƙon ba ƙaramin farin ciki ta yi ba. Tunda ta tafi ba ta da aiki sai tunaninsa. Duk a takure take jinta, gashi an ce sati huɗu za ta yi. Wannan saƙon shi kwantar mata da hankali jin cewar shi ma son ta yake yi. Gashi har zai aure ta ba tare da ko sunanta ya sani ba, ko ya yi hira da ita. Dan haka ba ɓata lokaci ta ce a sanar masa ya je ya samu Malam ta amince. Kuskure na uku_
_Nan da nan kuwa kowane ɓangare ya amsa. Aka tsaida lokacin bikinsu watanni huɗu._
_Ba a daɗe da hakan ba Uwale ta dawo, ta tarar da abin da ya ya sata suma sau uku a yini. Ya kuma tarwatsa duk wani buri da take da shi a duniya. Ya rusa kyakkyawan zumuncin da ke tsakaninta da Falmata. Ta zame mata maƙiyar da ba ta ƙi ta tsira tsinin mashi a tsakiyar maƙogwaronta ba._
_Mutumin da take mafarkin ta gama mallaka, take jinsa daidai da numfashin da take shaƙa bai fishi muhimmanci ba, ba ita yake so ba, 'yar uwarta maƙociyarta yake so. Har ma ya tsaida lokacin aure da ita. Yayansa kuma, wanda suke jini ɗaya shi ke sonta. Har ma da yawunta ta tura shi gurin mahaifinta a rashin sani, an tsaida lokacin aurensa da ita. Abinda ko karen haukane ya cije ta ba za ta koma gurin Malam ta ce ba shi take nufi ba, ba shi take so ba, ƙaninsa saurayi ga Falmata shi take so, shi kuma take nufin ta turo. Wannan abu ne ta sani da ba zai taɓa yiwuwa ba ko da kuwa a mafarkinta na barcin safe. Tana tuna sau uku Malam ya turo yana tambayarta ita ta wuro wane. Tana ba da amsa da eh. Ƙarshe ma har korar 'yan aiken ta yi ganin ana ta tambaya kamar ba a son a ba ta shi. Abinda ba ta sani ba shi ne, Malam na ta nanata tambayarsa ne ganinsa da ya yi Alaramma, bai burge shi ba sam, a matsayinsa na Malamin soro irin mutanen nan na yawan kawo matsala da wannan haram ne wannan makaruhi ne. Wannan abu ne da ba za ta taɓa yafewa kanta ba, haka Bashari. Dan kuwa ai ita ya fara gani, tana tunawa har murmushi ya mata. Me ya sa sai da ya kula tana rawar jiki kansa zai komawa Ƙawarta?Ko bai gane shi take so ba? Wane irin zalunci ne zai sa ya haɗa ta aure da yayansa, saboda karma ta yi zaton za ta same Shi ko? Menene Falmata ta fita? Ta ga dai ta fita manyan idanu, ko kuwa dan nata jajaye ne? Amma ai ta fita hasken fata, ko kuwa shi duka wannan bai burge shi ba? Waɗannan wasu tambayoyi ne da taje ta zube a gabansa ta kwarara masa su. Ya kuma amsa mata da hujjojin da suka tabbatar mata Bashari bai taɓa sonta ba daidai da kwayar gero. Ya tabbatar mata dama yayansa ya rako ya ganta. Murmushin kuma da take zaton ita ya yiwa. Ya yi ne a matsayinta na wadda Yayansa zai aura. Ta zube a gabansa a kan gwiwowinta, tana roƙansa da ya hakura da Falmata ya dawo gare ta, ya ji ƙanta ya duba girman soyayyar da take masa ya aure ta. Ta yarda idan Falmatan ce ita ma ya aure ta. Amma ya ce a'a. Falmata kaɗai yake da ra'ayin aure, ba ma yada damar auren mace sama da biyu. Ta ce masa idan wannan ne ba damuwa ko sadaki za ta ba shi ya biya. Ya ce a'a, shi fa tsakani da Allah ma idan ta matsa masa zai sanarwa Falmatan dan ta san irin zaman da za ta yi da ita. Tsoron hakan ya sa ta barshi da zancen da wani da mummunan ƙuduri cikin ranta. Sai dai abinda ba ta sani ba shi ne, da ace an faɗawa Falmatan da ta gane wacece ita a rayuwarta. Falmata za ta iya bar mata kome, za ta iya bar mata kome ciki harda mijin da take aure. Zuciyoyinsu ba iri ɗaya ba ne._
_Amma kuma da Allah ta yi rantsuwa ba za ta taɓa barinsa ya ji daɗin auren ba, yadda ita ma ta tabbata ko wa za ta aura, ko da ace zai bata duka daɗin duniyar nan to fa ba za ta ji daɗi. Mutum ɗaya ne take so ya kuma mata nisa. Ƙudurinta ba za ta barsu su haihu ba, ita ba za ta haihu ba haka shi ma ba zai haihu bare 'ya'ya su shiga tsakaninsu ya ƙara yi mata nisa. Dan haka ta haɗa kai da wani yaron Babanta da aikinsa yake kamar yankan wuta. Ya mata aikin da ya bata tabbacin duka su biyun ba za su haihu da su ba._
STAI LEGGENDO
FADIME
AbenteuerFADIME "Wannan fa da kai na na jarrabata na ga aikinta, ka ga da fatar bakar kyanwar da bata bude ido ba aka yi rufin farko, sa'annan aka sake nad'eta da fatar d'an tayin cikin tunkiya, sa'ananan aka nad'eta da fatar bakin kumurci, sa'annan aka ke...