BABI NA SHATARA

571 24 0
                                    

           🦋🦋🦋
  WRITING BY                                  
DIJA_WAZIRI
      AND
FIRST LADY

      _Abuja_

Ana gama daura aure bayan anyi liyafar cin abinci (walima Na maxa), akayi pics kala-kala sannan abokanan Mustapha suka nufi gidan su amarya domin daukar ta a taho da ita kano

Amarya banda xumudi ba'abin da takeyi domin 32 teeth dinta take washewa (lol).. Anyi mata nasiha sosai da sosai akan rayuwar da zatayi na gidan auranta...

Karfe 5 dot motoci suka kunno kai cikin gidan Mustapha direct sight din Mustapha aka kaita, dangin amarya sai sanbarka akeyi

Kawayen Maryam suka shiga chan cikin bedroom dinta aka bar iyaye a parlor

"Hmm Maryam yanxu gidan Ku daya da ita dayan matar tashi kenan?"

"kedai bari khady nima kaina abin ya tsayamin arai wallahi "

"to ke maryam kin yarda da hakan kenan?" haba friends karfa ku manta nice Maryam kuma kukan ku kunsan halina in and out so dont bother your self's owk ,

kuma ni abin da yake min dadi acikin mind dina any moments bai wuce na tunawa da Musty baya son ita Fairuzan ba, yace min kawae yana xaman biyayya da kuma kaddara da ita ba, ammah ba komai friends very soon xaiyi out da ita daga cikin gidannan" (suka tafa tare da yin dariya dukkan su).....

"a'ah Beely lafiya naga tunda muke magana baki saka baki ba? "uhm khady kenan ai naji abin naku ne sai ku gaisa,

kamata yayi kuyi mata magana akan tayi biyayya ga mijin ta sannan ta girma ma matar tashi domin kuwa tana gaba da ita ko da kuwa awajan Allaah ne don na tabbata matar nan nashi tana cikin tsananin cikin damuwa gami da yadda Maryam ta fada mana yanxu na cewa baya santa kunga kuwa ita dayan matar tashi tana tsananin ganin *K'IYAYYAR NAMIJI* but kun dage kuna yi mata useless magana"...

"to malama Beely kinga jiya akayi walima kuma baki xoba kinga dakin halarci walimar da saiki bada wannan gudummuwar ammah yanxu kiyi hakuri domin ba inda wannan maganar taki xatayi tasiri acikin xuciyata don wallahi nadau alwashin sai tabar gidan nan very very soon "....

"uhm kinji dashi Maryam Ammah bai kamata ki biye nasu ba don wallahi xasu kaiki su baro ne... ammah idan kinga xakiyi ke kika sani, ku kuma kuji tsoron Allaah dan duk abin da Maryam tace xatayi wanda ba dai-dai ba to kuna da bubban kamasho aciki" (tana kai wanan tabar bedroom din ta nufi parlour).....

"kunji min wannan Beelyn ita duk abin da akace xa'ayi bata ta6a supporting din muba", uhm ita ta sani dai ni bari inje inyi alola don mu fara shirin dinner dinnan kafin lokaci yayi"...

motocin da aka kawo amarya dashi na shigowa gaban Fairuza yayi mummunan faduwa cikin hukuncin ubangiji tayi sauran furta innalillahi wa'in na'ilaihir raji'un haka taita furtawa har taji sanyi a ranta....

Talatu tana ta kwantar mata da hankali tare da karayi mata nasiha a haka har ta samu fairuza ta saki jikin ta suka fara fira..

Mustapha ya kira wayan Abdul domin yaji lafiya baixo wajen daurin aure ba ammah fir Abdul yaki picking call din mustapha ya kira kusan 6* ana bakwai dinne Abdul yayi s.off din wayar shi gaba daya.

xuciyan Mustapha inyayi dubu bai tashi ba ( kuma kunsan abin da muke nufi) haba Abdul yanxu abin da xakayi min kenan? but ba komai...

"haba kaikuwa ya kamata ace ka daga wayar nan tashi domin kaji mai xaice maka".

"punishment din shi kenan da xanyi mashi domin ya gane cewa abin da yayi ba dai-dai bane kwata-kwata"....

"ammah dudda haka ya kamata ace ka amsa wayar tashi tunda har yaga bai ganka awajen daura aure ba yasan kana fushi dashi ne sosai shi yasa kaga harya kiraka" uhm kyale ni kinji bari in dan kwanta kafin la'asar tayi"...

Amarya tayi kew cikin shigarta ta less sky blue tare da net head pink, heal shoe ear ring bangus nickel duk pink color, kawayen tama duk sunyi shigar material brown en milk sunyi kew matuka....

Ango shima ya shirya cikin wata bugaggiyar shaddar shi sky blue wanda taji aikin hannu da light pink din xare haka hular shi da takarmi, ammah xuciyarshi ba dadi domin yaso ace Abdul yana kusa dashi....

maryam da Mustapha banda kamshin turare ba abin da ke tashi awajen nasu gashi sunyi kew matukar gaske... suna takun sy na kasaita har suka isa wajen mota suka shiga

K'IYAYYAR NAMIJIWhere stories live. Discover now