Kwance nake bisa kan makeken gado na yayin da kida ya ke tashi wakar Sadik Ahmed ce nake saurara domin kuwa ina mugun jin dadin wakokin sa shiya sa a koda yaushe nake sauraron ta.lumshe ido na na karayi a lokacin da ya ke fada a cikin wakar sa kece sanyin ida niya ta so na ke
namutu a cikin idaniyar farinciki na.buga kofar a ka soma yi a hankali na furta oui entre (yes come in)momy na ce ta shigo fuskarta dauke da murmushi ta zo ta zauna kusa dani yayin da ta rike min hannu kafin ta ce khaira na hutawa ki ke ne? Wato bakya gajiya da sauraron wakar mutumin ki KO ? murmushi nayi game da shagwabe fuska nace haba momy ta ya zangaji da sauraron abinda yake sanyani farinciki uhum ina matukar son wakar sa momy kallo na tayi yayinda naga damuwar a fuskarta ta ce ina matukar jin tsoron kar son ya koma da maiyinta a hankali na ce haba momy ki daina wanan tunanin mana can ta nisa tace kinga na manta Abban ki ne ya ce na kira ki ay kuwa da Sauri na tashi na fice ina isa falon mu na Haye saman cinanu sa ya ce haba khairan Abba so ki ke ki kalla ni ne a shagwabe na ce hay dai Daddy niba ma wanan ba gani momy ta ce kana kira na a daidai lokacin momy ta ISO tare da zaunawa kusa da Abba yayin da su ka kalle juna tare da yin murmushi wa junan su a raina fadin kawai nake wanan soyayyar Ta su momy ba dama a kodayaushe kara kaunar junan su su ke uhum Khair magana nake miki fa na'am Abba ya ce cewa nayi me ki ka shirya na birthday dinki ? Aw ni har na ma manta da jibi ne zagayowar ranar haihuwata ranar da zancika shekara goma sha shida Wanda yayi daidai da shekara ashirin Kenan da auran iyayena murmushi nayi nace Ashe fa akwai biki babba momy ce ta jefomin harara saboda ta fahimci inda na dosa Abba ya ce karbi wanan ki rarabawa kawayen ki sanan ki je kiga wane irin shiri zakuyi dadi ne ya cika min zuciya na rungume Abba kafin na ce i love you so much Dad you are the only in the world shima ya mayarmin da i love you too My angel momy ta ce ni kuma fa yayin da take kallon mu cike da murmushi a fuskarta a tare ni da abba mukace I love you so much more a take kuma muka kyalkyale da dariya nace to ni bari naje na shirya zanje gidan su Safina.su ka amsa da toh adawo lafiya hayewa nayi asama inda daki na ya ke a take na shiga toilet na yo wanka kafin na dawro alwala domin na soma jin Kiran sallar la'asar .ina fitowa daga toilet na daura zane tare da sanya hijab na haw kan darduma na soma Sallah ina gamawa nayi wa iyayena addu'a dani da sauran al'umma musulmi tashi nayi na zauna kan gado na yayin da na soma shafa mai har dai nagama shirya cikin doguwar Riga maroon na sanya plat shoes maroon sai jaka ta fara da na dauka na kara fesa turare na Couture da Black Berry ina matukar son turaren na kara kallon kaina a madubi simple make up ne a fuskata nayi matukar yin kyau KO da yake na kanji kawayena na zuzuta irin kyau na har cewa suke KO barci na taso sai sunga na kara kyau Kyakyawa ce ni ta gaske kuwa fatar jiki na fara ce tas fuskata na dauke da manyan fararen ido sexy eyes hanci na dan daidai dauke da dan karamin baki na pink idan nayi murmushi kuwa fararen hakora na ne masu dauke da 'yar siririyar wushirya mai karamin kyau kumatu na sunkan doba da zaran nayi murmushi KO da kadan ne kuwa kirar jiki kuwa siririya ce ni sai d'Ai ina da boobs 'yan daidai ina da kirar kalangu kamar yanda ake fada bangaran murya kuwa ba'a magana domin wata irin zazakar murya ce dani Wace sai dai nakara godewa ubangiji na da ya halicce ni a bisa baîwar da yayimin sam bani da daukar kai mahaifina shahararen me kudi ne Wanda zan iya cewa zai iya zama na uku a fanni kudi a africa GABA daya umma na 'yar mulki ce domin mahaifinta shine shugaban kasa a Cameroon zan iya cewa kab dangin mu ba talaka amma hakan bai sanyani girman kai ba saidai banci kayin dariya ba saidai murmushi umma na bafulatana ce mahaifina kuwa kanuri ne dan Borno ne su uku su ke ga iyayen su Abba na Wanda sunan sa Abdoul Hakim sai mai bimasa usmane sai autar su hajiya sakina su dukan su masu kudi ne kodayake hakan ya samo asali ne tun kakanin su a yanzu haka muna zaune a Kaduna ne saboda kasuwanci Abba na momy kuwa su hudu suke d'à iyayen su Wanda ita ce auta Zahra babban yayan Malik Wanda a yanzu yana New York yana aiki Likita ne yana da mata Amira da diyansu biyu tawaye Moucha'ir da Mujahid shekarun su ashirin sai mai bima Malik Harun ma'aikacin Banki ne a Sudan sai Attuma Wace kuma barister ce .zan iya cewa karaf family namu shahararu ne kuma wayayu
Nacika ku da surutu batare da na sanar da ku sunana ba sunana ummeisat ni kadai a gun iyayena wa 'yanda suke cewa ni khairate din suce suna matukar kaunata nima haka tun ina da shekara goma sha biyu na sawke alkur'ani mai girma na karanta litatafan addini da dama ina da ilmin addini Dana boko daidai gwargwado a yanzu haka idan hutu ya kare university zan shiga ina matukar son wakar Sadik Ahmed Wanda mawaki ne dan Kano ne saidai komai NAwa da lokacin sa.
Fitowa nayi harabar gida yayinda duk masu aikin gidan da bodygard su ka duka tare da gaisheni cikin rashin jin dadin haka nace wai bana hannaku dukamin bâ ? Cikin rawar murya su ka furta kiyi hakuri ranki shi dade bazamu iya gaishe ki a tsaye bâ girgiza kai nayi yayin da bodygards hudu suka zagaye ni na kalle su na ce yau fah babu Wanda zaimin rakiya a hankali cikin kaskantar da murya su ka ce kiyi hakuri ummarni Abbanki ne idan muka saba zamu iya rasa aikin mu tausayin su naji kafin nace muje driver yace ina zamuje Khairan daddy cikin sakin fuska na ce masa gidan shugaban kasa gun Safina an gama cewar driver.