Chapter 1

814 27 1
                                    

*ABADAN DANI DAKE*💝
💝 *ZAMU ZAUNA*

*_Written by F k Ahmad_*

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's_*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
IG PML WRITERS
https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
http://maryamsbello.blogspot.com

*_DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI_*

*_Wannan labarin k'irkiran sa nayi toh idan aka samu wani littafin da yayi kama da wannan toh akasi aka samu dan haka ina rokan marubuciyar da tayi hakuri intaga da matsala to tayi contacting ina_*

*01*

Mari ta sake wa baiwar Allah'n da ke durk'ushe agaban ta tana kuka dafe da kuncin ta, ita kuka wacce tayi marin mik'e wa tayi tsaye daga kan sofa sai faman haushi take yi kamar kare tayi nuni da yarinyar tana cewa "ke yar gidan matsiya ta, ki bini ahankali cikin gidan nan ko gidan ta kasa d'auka na dake, wato har kin isa kai k'ara ta wajen shakiyin mijin naki ko?"

Nuwaira ta d'ago kyawawan manyan idanun ta dake jik'e da hawaye duk sunyi ja dasu cikin muryan kuka tace "Anty kiyi hak'uri amma Allah ki yarda ni ban kai k'aran ki ko ina ba", Anty Fadila ta kai bayan hannun ta zata make ta kenan taji tsawar da Yusuf ya daka mata a lokacin da ya shigo cikin parlour'n yana cewa " kika yarda hannun ki ya sauka a jikin ta to sai na sab'a miki mara mutunci kawai".

"Haba Yusuf wannan yarinyar ba k'anwar baya na bace sam baka bari na na tsawa ta mata idan tayi laifi kafiso tana raina ni ko da yaushe ya za ayi ta kai k'arana wajen ka dan nayi amfani da dukiyar ka ba da sanin ka ba" cewar Anty Fadila.


Afusace Yusuf yace "ai gaskiya ne saboda meye zakiyi hakan baki tambaye ni ba, nan gaba ki sake aikata hakan kigani" ya k'arasa maganar tare da d'aga mata hannu kamar mai daukan ta.

Jiki na rawa Anty ta ja da baya duk da haka bata daina hararan Nuwaira ba. Yusuf ya k'araso gaban Nuwaira ya d'ago ta yana share mata k'walla yace "kar ki damu mata ta, mu shiga daga ciki", ya rik'e hannun ta za su shige d'akin su yaji muryan Hajiya daga baya tana ta cewa " can dai kukarata da matar taka kana kiran yayar ka wacce ta girme ka mara mutunci yo kai mutuncin ne gareka ja'irin yaro".

Yusuf ne ya juyo da jin wannan kalaman yanayin sa duk ya canza kamar wani zaki ya fidda numfashi ya kalli Hajiya wacce ita ma sai da ta tsorata dashi yace " Hajiya da ke da y'arki nasha gaya muku ku fita daga harkar mata ta ko wallahi na muku abun da bakuyi tsammanin saba wannan alk'awari ne ko meye zan iya yinsa" ya juya suka shige ciki.

Anty Fadila ta buga babbar tsaki ta juya ga mahaifiyar ta tace "Hajiya share su amma wallahi sai naci k'aniyar wannan yarinyar ba dai ni ta raina ba zanyi maganin ta", Hajiya ta girgiza kai tace " ni dai wannan yaron ne dai bana so ke kuma matar sa ce ta tsaya miki arai".

Fadila ta samu gu ta hakim ce kan kujera ta d'aura kafa d'aya kan d'ayan tana girgiza su tace "badai ni Abdul ya wulak'an ta ba akan ta toh ai kuwa sai taga kuran ta dan sai na hana ta zaman gidan mijin ta, dan ta nuna min isa ma wato da ta tashi k'ani na ma ta aura ko" ta kad'a kai kamar mai tuno muguntar da zata saka.

Hajiya ma waje ta samu ta zauna tace " ke ai yanzu nayi duk yadda zanyi, na raba ta da Abdul d'in sai kisan yadda zai koma gare ki kawai da ta tashi kuma ta kan k'anin ki ta biyo hmm", ta d'an saki Murmushin yak'e.

Fadila tace "hmm Hajiya ai yanzu narasa ya zanyi Abdul d'in ne sam baya sauraro na acewa wai ke kika raba shi da Nuwaira ya zaiyi ya aure ni". Hajiya ta d'an nisa tace "kwantar da hankalin ki y'ata barshi da ni idan yasan wata bai san wata ba". Fadila ta kalli mahaifiyar tata tayi murmushin jin dad'i.

Yusuf da Nuwaira na shiga d'aki Nuwaira ta fad'a kan gado ta soma rera kuka tana cewa " wata na biyar a cikin gidan nan masifar yau daban na gobe daban ya zanyi da rayuwa ta ni ba iyaye ba".

Yusuf ya d'ago ta ya manna ta ak'irjin sa yana shafa mata baya yace " Nuwaira kina dani baki rasa komai ba kiyi hak'uri da halin y'ar uwa ta da mahaifiyar ta wallahi dan babu yadda zanyi dasu ne saboda nayi wa Abba alk'awarin bazan rabu dasu ba lokacin da yazo mutuwa dan haka yake buk'ata daga gareni, yana son nakasan ce dasu har tsawon rayuwar mu kada na rabu dasu duk rashin mutuncin su amma abu d'aya ne bazan yi ba, shine bazan iya jure ci miki zarafin da suke ba tun ba wannan Fadilar ba".

Nuwaira ta kad'a kanta tace "babu komai Yusuf Allah yaji k'an mahaifan mu baki d'aya, amma ina son kasan idan Anty tana aikata wani abun ko hankali na bana mai dashi wajen ta gudun masifar ta ballan tana nasan abun da tayi har nakawo k'arar ta wajen ka".

Yusuf ya tallab'o fuskar ta ya kalle ta cikin ido yace "kar ki damu nasan bakya yin hakan yanzu kwanta ki huta ni zan fita wajen aiki kinji ko". Kai ta gyad'a masa tace "adawo lafia", kiss ya manna mata a goshin ya d'au jakar sa ya fita.

Hajiya da Fadila ya tarar zaune a parlour'n kallon su yayi cikin takaici dan yasan zancan sa suke da suka gansa ne sukayi shiru. Yatsan sa yayi musu nuni da yace " duk yadda zakuyi haka za ku barni da mata ta, ke Fadila kinsan ni naganki sanda kike bud'e save d'ina ba Nuwaira ba amma kike tuhumar ta duk dan ki had'a ni da ita, toh Allah ya fiki ni da Nuwaira har abada babu mai shiga tsakanin mu".

Fadila dake jujjuya ido cikin takama tace "Mu zuba mu gani idan har zan kasan ce cikin gidan nan sai na raba ku". Yusuf kai kawai ya gyad'a ya fita daga gidan dan ya rasa ma mai zaice da ita.

Nuwaira da taja pillow ta ajiye shi jikin kan gadon ta jingina kanta tana tunanin rayuwar ta a duniyan nan tun daga lokacin rasuwar mahaifiyar ta daga garin su.







Urs Fannah😘

Abadan Dani Dake Zamu ZaunaWhere stories live. Discover now