Chapter 11

81 4 0
                                    

*ABADAN DANI DAKE*💝  
             💝 *ZAMU ZAUNA*

*_Written by F k Ahmad_*

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's_*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
IG PML WRITERS
https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
http://maryamsbello.blogspot.com

*Kuyi hak'uri da kuka jini shiru kwana biyu.*

*Dedicated to Matan Real PML Writers, ina gai da ku kaman su*

Hajiya Faty Azland
Maryam Muktar
Lady Fulani
Mss Hafsy
Sadnaf 4real
Miss Bhal
Mommyn Musaddiq
Mommyn Sultan
Husnah Bauchi
MaryamSBello
Ummu Basheer
Sadiya Adam(Sadnaf)
Sadia Tahir
Nana Fa'ad
Hafsat Musa
Rafe'at Dikko
Ummee Garkuwa
Real Mmn Khadija
Aunty Khady
Zee yabour
Fashuna
Fareeda Sweerie
Biebie Dee
Salmah
Deee

*I love you all Sweethearts, Allah ya barmu tare.*


*11*

       Fadila ta fito zata koma gida a hanya taga mai saida Fruits, nan ta tsaya ta siyi kala biyar ta kama hanya.

       Tana isowa ta samu Nuwaira a kitchen, sallama ta mata a nitse, cike da mamaki Nuwaira ta juyo dan gaskatawa idon ta muryan wacce taji.

       Murmushi mai kyau Fadila ta mata sannan tayi approaching nata ta ajiye ledar fruits dake hannun ta a gaban Nuwaira tare da fad'in "Hajiya Nuwaira ga fruits ne na gansu a hanya sai na tuna kina son su dan ina ganin kina yawan siyo wa shine na taho miki dasu".

      Nuwaira da mamaki ya ishe ta dan ganin abunda bai tab'a faruwa ba yau da kyar ta iya mata murmushi tace "toh na gode Anty Allah ya saka", "a'a ke kuma ya haka ai k'anwata ce ke ko?" Murmushi Nuwaira tayi tare da gyada mata kai ta d'auke ledar a kasa.

      Fadila na fita waje a hankali take cewa "mahaukaciya kawai sai nayi maganin ki ai", ta shige d'aki.

       Duk da mamakin da Nuwaira tayi gami da Fadila, bata kawo komai ranta ba haka ta yanyanka dukka fruits in ta ajiye na Yusuf ta d'auko wasu ta fita zuwa parlour.

      Hajiya ta tarar zaune a parlour ta k'araso ta ajiye plate na hannun ta a kan stool na gaban ta tare da cewa "Hajiya ga fruits", bud'an bakin ta tace "ce miki nayi ina bukatar su?" Kai kawai Nuwaira ta g'yada, sai tace "toh d'auke su.

     Sunkuyawa tayi zata d'auke sukaji yo muryan Fadila na fitowa cikin fara'a tace "a'a haba Hajiya ya zaki fad'i haka, Nuwaira ajiye ki zauna zata ci mana", Hajiya kallon 'yar nata take kawai dan tasan tabbas wannan fara'ar ba a banza take yinsa ba da biyu.

       Saida Nuwaira ta samu waje ta zauna, Fadila ta sa musu wani movie a Tv suna kallo, sai hira da dariya suke gwanin sha'a wa in ka kalle su kaman ba su da suke gaba ba.

      Time na zuwan Yusuf ne yayi, yayi sallama ya shigo suka amsa mar a tare, ba k'aramin mamaki da dad'i yaji ba dan ganin su a tare suna tad'i, gaisa wa sukayi dukkan su nan Nuwaira ta mik'e ta karb'e jakar sa suka wuce ciki. Fadila kuwa harara ta bisu dashi basu gani ba.

      Da daddare Nuwaira na shimfid'in gado Fadila tayi sallama ta shigo d'akin, murmushi Nuwaira tayi ta amsa ta.
     Wayar ta Fadila ta hanga akan drawern gado.

     Bayan Nuwaira ta mata iso cikin d'akin, zuwa tayi ta zauna akan drawern tare da d'auke wayar tana cewa "sorry pls nazo damun ki a daren nan, application na azkar nake son ki turo mun wanda naga kina yawan karanta shi".

     Nuwaira tace "Ok babu komai ki tura", "oops da password ashe" cewar Fadila da bata ji dad'in hakan ba. "Oh!" zuwa zatayi ta karb'i wayar ta bude sai ta tura mata kenan tayi tuntub'e ta bugi k'afar ta a edge na gado har saida babbar yatsar ta ya fame jini ya fara fita.

       K'ara Nuwaira ta sakar na rad'ad'in zafin ciwon da taji ta sunkuya tare da kama k'afar ta soma hawaye, "Subhanallahi meya sa meki", cewar Fadila da tayi saurin k'araso wa wajen ta. Nuwaira ta daure tayi kok'arin tashi tana cewa "babu naji ciwo ne Anty ki zauna bari na wanke jinin a toilet".

     "Ok sannu yi maza ki wanke pls", "oh toh ai zaki iya turawa kafin na fito, password d'in...... " ta gaya mata kafin ta shiga toilet d'in, hamdala sosai Fadila tayi aranta sannan ta shiga contacts na Nuwaira don tayi checking number'r Safiya, bata wani b'ata lokaci ba dan da sunan ta tayi saving so tana gani tasan ita ce, da sauri tayi loading insa wayar ta ta koma tura azkar app da ta fake shi tazo nema.

       Tana gama tura wa Nuwaira ta fito, Fadila ta mata murmushi tare da cewa "sannu Allah ya tsare gaba", daidai wannan lokacin Yusuf yayi Sallama yashigo suka amsa. Yace "meya sa meki naji ana Allah ya tsare?" Sai da Nuwaira ta masa sannu da zuwa sannan tace "ciwo naji a k'afa ta yanzu" tana nuna masa k'afar, "kai garin yaya?" ya ajiye ledar dake hannun sa ya kamota zuwa gado suka zauna yana duba kafar.

     Mik'ewa Fadila tayi ta ajiye mata wayar a bakin gado tace "na tura godia nake", "a'a babu komai Anty" cewar Nuwaira. "Sai da safen mu" tace kafin ta fice. Spirit Yusuf ya d'auko ganin wajen na jini har yanzu, da kyar ya lallab'a ta ya shafa a wajen sannan suka kwanta bacci.

      Fadila na zuwa d'akin ta tayi maza tayi dialing number'r duk da dare yayi hakan bai hana ta kira ba, tafi so ayita ta kare hankalin ta zaifi kwanciya.

      Safiya na kwance tana baccin ta har da mishari taji call ya shigo wayar ta, bakin ciki ne ya lullub'e ta tuna kashe wayar da batayi ba kafin ta kwanta gashi an katse mata baccin ta, hannu tasa ta ciro wayar karkashin pillow taga new number ne, tsaki taja tayi switching off gaba d'aya ta wullar da wayar ta gyara kwanciyar ta.

       Ganin anyi rejecting call d'in Fadila ta sake dialing nan taji switched off, tsaki ita ma tayi tana tunanin girman kai irin na Safiya dukda ba komai garesu ba amma sai girman kan tsiya "yarinyar nan in ban bita a hankali ba inaga sai raina ya b'aci ban samu abunda nake so ba", da haushin Safiya aranta haka ta kwana.



Urs Fannah😘

Abadan Dani Dake Zamu ZaunaWhere stories live. Discover now