Chapter 40-45

147 11 0
                                    

💝 *MAFARKI NA*💝
   💝                         💝

*_Written by F k  Ahmad_*

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's_*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
IG PML WRITERS
https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
http://maryamsbello.blogspot.

*In dedication to Mss Hafsy*👄
      ( *its me* )
*_The whole book is dedicated to you my dear._*

A short story from my night mare.

40 - 45

        Sauran da suka zo first in other categories d'in kuma  kowannen su aka basu kyautar naira dubu tamanin, su da basu ci ba kuma aka basu dubu goma goma dan kok'arin su.

    Farin ciki wajen d'aliban nan baya misaltuwa amma banda Hafsat da Imran da sukayi zaune kamar basu san abun da ake a gun ba, gaba d'aya Hafsat sai ta rasa abunda ya hana ta celebrating, ita da take d'okin zuwa na d'aya gashi ta samu amma kuma sai abun ya daina damun ta.

        Shiko Imran bak'in cikin zuwan sa na d'aya yake yafi son Hafsat ce kad'ai ta zo na d'aya. Shugaban wajen ne ya kira sunan wa 'yannan d'alibai d'aya bayan d'aya yake mik'a musu check nasu a hannu haka ma Hafsat aka bata mukullin motar ta, imran kuma ticket na Hajjin sa.

       Imran na karb'an ticket d'in direct wajen malamin sa ya nufa yaje ya durk'usa kansa a k'asa yake mik'a masa wannan ticket d'in, harara malamin nasa ya bisa dashi sannan ya amsa.

        Hafsat dake kallon su a nesa sai tayi mamakin kaiwa malamin su ticket d'in da Imran yayi bayan nasa ne shi aka baiwa. Godia sosai d'aliban suka yi har Saida Hafsat ma ta karb'i Mic ta musu nata godia ta musamman.

        Bayan an tashi daga wajen ne Hafsat take son yin magana da Imran amma bata gansa ba, Imran kuwa dan yasan Hafsat zata nemeshi ne ya b'uya dan abu ne mai wuta ya samu tsayawa da ita a nan wajen tunda akwai malaman su da suka sa masa ido.

        Haka aka zo tafiya dasu masaukin su Hafsat ta koma da bak'in cikin rashin ganin sa.

        Tunda Hafsat ta koma ta shiga cikin damuwa gashi gobe da safe zasu kama hanyar zuwa Maiduguri kuma motar su dabanne ya za ayi ta gansa acan.

        Tana zaune a k'asan carpet tana cin abinci amma kamar wacce aka sata dole a hankalin ta take ci dan tunanin da take. Wata room mate d'in ta ne ta shigo nan Hafsat ta d'ago da kanta ta kira sunan ta "Hannatu", "na'am" ta amsa ta, "nikam kinsan part d'in da maza suka sauka?" "Eh suna can gaba da mu ai, wani abun ne?"

       "Eh so nake naje wajen", " kai me zaki je yi? Mata fa basa zuwa wajen", take Hafsat ta had'e rai tace "toh ya zanyi yanzu wani nake nema fa", " wani kuma?" Cewar Hanne da ta juya ta kalle ta cikin fargaba, "eh wannan d'an garin namu Isma'il d'in nan ne nake sob magana dashi".

        "Au idan har shi kike nema ai na gansu da sauran mazan gindin wata bishiya can kusa da Gardner yanzu", " haba!" Cewar Hafsat da ta mik'e tsaye da jin hakan, "zan iya zuwa can d'in ko?" "Eh zaki iya", nan Hafsat ta ja hijabin ta da ke ayije ta saka ta nufi waje da sauri.

        Tana iso wa kusa da Gardner'n ta hango su zaune suna hira amma banda Imran dake gefe da gani hankalin sa baya wajen su. Tunanin ya za ayi ta tunkari zuwa wajen su take dan kar tayi abun kunya sai kuma ta dak'e ta nufi wajen su.

      Sallama tayi suka amsa mata nan tace "erm ya Imran nake son magana da", kowa juya wa yake dan neman sanin wanene Imran daga cikin su, shiko Imran ko daga kai bayyi ya kalle ta ba, da ta gane basu gane wanda ta tambaya ba shine ta gyara " Oh Isma'il dai nake nufi", daga nan ne ya juyo tare da cewa "Hafsat me kike nema kuma?"

      Murmushi ta masa tace "mu koma gefe mana", kaman wanda baya so haka ya mik'e yayi gefen ta bisa, aiko samarin nan sun samu abun magana kenan, magana suke k'asa k'asa yadda ba a jin su.

       " Ina jinki kuma kiyi sauri dan banyi tsammanin zuwan ki nan ba sannan za a iya fitowa neman mu ko da yaushe", cewar Isma'il. Murmushin har yanzu Hafsat keyi sannan tace "owk ya Imran so nake naji dalilin ka na bani damar zuwa na d'aya da kayi, idan aka maka tambaya na tabbatar da kasan amsar su amma baka amsa ta daidai sannan bakayi farin cikin zuwan mu na farko ba kuma ka gaisa malamin ka ticket d'inka kodai ajiye maka zaiyi?".

       Kai ya girgiza yace " ko d'aya ba haka bane nayi farin cikin zuwan ki na d'aya mana saide nine bana son na zo na farko", eyes wide opened Hafsat tace "ko meye dalilin ka?" Ajiyar zuciya Isma'il yayi sannan yace "Hafsat banga amfanin zuwana na d'aya ba domin babu abun da nake amfana dashi, ina fatan dai kinga lokacin da wancan malamina yazo yana mun magana sanda muke amsa tambayoyi?" Da sauri Hafsat ta gyad'a kai tare da cewa "yauwa eh naso nasan me ya gaya maka".

        Kai ha gyad'a sannan yaci gaba da cewa " kujerar Hajjin nan dai yazo nema, da wannan sau uku nake samun kujerar amma ban tab'a zuwa ba sai malamai na da suke karb'e ticket d'in shine yake ingiza ni da kar nabari kici gasar", baki ta bud'e tare da d'aura hannun ta akai tana cewa "toh me yasa hakan ne?" "Zalunci mana ai na gaya miki halayen su abaya".

       Kaman daga sama suka ji muryan wannan malamin Isma'il d'in yana cewa " ke me kike yi anan wajen? Maza kibar nan", ya k'arasa cikin tsawa, a tsora ce gaba d'ayan su suka juya ganin su, d'an k'aramin tsaki Hafsat taja, Isma'il yace "kinga ko abun da nake gudu", " ka kwantar da hankalin ka ya Imran insha Allahu Allah ya fisu kuma zan magance maka wannan matsalar", ganin wannan malamin yana doso inda suke yasa Hafsat saurin barin wajen.

       Malamin na k'araso wa yace "maza ku tashi ku shiga ciki", babu musu gaba d'ayan samarin suka mik'e, a hanyar tafiyar tasu ne d'aya daga cikin yake cewa " toh wannan yarinyar ko me tazo nema wajen Isma'il?" D'ayan kuma yace "ai koma menene Isma'il yayi babbar kamu gaskiya", Isma'il dake jinsu a baya ya juya yace dasu "kai bana son shiriri ta wannan fa kanwata ce Hafsat".



Urs Hannaf😘

MAFARKI NAWhere stories live. Discover now