A zaune a parlour Baba Babba Maryam ce tare da Baba Babba. Soyayyiyar gyaďa suke ci yayin da Maryam ke yi mishi hira, rabi da kwatan hirar duk shirme ne. Shi dai saurarenta kawai yake yi idan ta faďi abin dariya yayi murmushi.
Zuwa can ya kalleta yace "Ya Allah ka raya mini Maryamu ka albarkaci rayuwarta ka azurtata da zuri'a na gari kasa ta kasancewa mijinta uwar iyali".
Ko kaďan hankalin Maryam baya kan Baba Babba don tun bayan da suka gama cin gyaďa ta fito da duwatsunta tana 'yar carafke, 'yar hirar da take yi mishi ma dainawa tayi.
Aliyu ne yayi sallama a kofar parlour. Sai bayan Baba Babba ya amsa yayi mishi izinin shigowa sannan ya shigo. Zama yayi a kasa kusa da Baba Babba sannan ya gaishe shi, bayan sun gama gaisawa ne yace "na shigo ďazu Inna tace mini kana bacci, dama zan gaya maka batun tafiyata Abuja gobe ne akan maganar visa".
Baba Babba ya gyara zamanshi sannan yace "Masha Allahu tafiyar ta iso ashe, to da wanne lokaci zaka tafi?" Aliyu yace "In Sha Allahu ana fitowa daga sallar asuba don inaso na isa da wuri", yace "hakane, to Allah ya kiyaye hanya yasa kaje lafiya ka dawo lafiya yasa a dace da abinda za'a je nema". Aliyu yace "amin Baba nagode" yana mai russunawa.
Duk abin nan da ake yi Maryam na zaune tana wasa da duwatsun 'yar carafkenta ko ďagowa bata yi ta kallesu ba tun shigowar Aliyu. Murmushi Baba Babba yayi yace "Maryamu kenan, banji kin gaida yayanki ba fa". Turo baki tayi ta hade fuska tamkar mai shirin yin kuka tace "nifa Baba na daina kulashi tunda dai ya tsaneni kullum sai ya doke ni to nima babu ruwana dashi, shi yasa ma na daina gaisheshi".
Harararta Aliyu yayi jin abinda tace sannan yayi tsaki ya dauke kai cikin ranshi kuwa cewa yake yi "yarinya baki yi karya ba don kuwa sosai na tsaneki ko sha'awar ganinki ba nayi".
Tuni Baba Babba ya bata rai yace "Subhanallahi, me Maryamu take faďa haka, kar na kara jin irin wannan maganar ta fito daga bakinki, wato kin fiso a kyaleki kina iya shege ba tare da an tsawatar miki ba. Maza tun muna shaida juna ni dake ki gaida yayanki".
Ganin babu alamar wasa a fuskar Baba Babba ne ya saka babu musu ta durkusa ta gaida Aliyu sannan ta fice daga parlour don ko gaisuwar bata bari ya amsa mata ba ta fita.
Ajiyar zuciya Baba Babba ya sauke ya kalli Aliyu yace " har kullum ina gaya maka cewa shi yaro ba'a cewa za'a tankwara shi ta karfi. Tsanani da azabtarwa ba shine tarbiyya ba. Nasiha da faďakarwa cikin lumana shi zai sa ta fahimci duk abinda kake so ta fahimta duk da dai ni ban ga wani aibu a cikin halayyar Maryamu ba da har yake damunku. Yarinta ce kowa da irin tashi, nan gaba idan aka ce tayi tsokana ko neman faďa ba zata yi ba. Amma kaga yadda kake tafiyar da al'amuranta ďinnan babu abinda zai jawo sai rashin jituwa a tsakaninku tunda kana jin abinda take faďa bata kallon tsananin da kake yi mata a matsayin gyara sai dai takura ko rashin so. Bazan so ta taso da tunanin cewa baka kaunarta ba, bana son abinda zai kawo rabewar kai a cikin zuri'ata don haka ka kiyaye".
Cikin kaskantar da kai yace "kayi hakuri Baba In Sha Allahu hakan ba zai kara faruwa ba". Hira suka ci gaba dayi wanda rabin hirar duk nasiha ce Baba Babba yake yiwa Aliyu akan zaman duniya.
Ga Maryam kuwa tana fitowa daga parlour Baba Babba bata zame ko ina ba sai gidan Baba Karami, duk da dai ma bata cika yawan zuwa gidan ba don kuwa shi bai cika sakar mata fuska ba kamar Baba Babba daga shi har matanshi, har gara ma Hajiya Goggo wasu lokutan tana sakar mata sai idan taga alamar rashin kunyarta zata motsa nan da nan sai ta canja fuska ta hade rai tamkar bata taba dariya ba. To da Maryam taga haka zata shiga taitayinta.
Yanzu ma da ta shigo gidan ďakin Hajiya Goggo ta shige, ai kuwa tana shiga ta tarar da warmers ďin abinci a ajiye a gefe. Sai a sannan ta tuna cewa yau ko abinci bata ci ba ta fito daga gida kuma ko da ta shiga gidan Baba Babba bata nemi abinci ba.
Kitchen taje ta ďauko plate da spoon ta dawo ďakin ta buďe warmers ďin taga shinkafa ce fara da miya sai haďin salad da akayi wrapping dinshi da foil paper.
Shinkafar ta ďiba kaďan ta saka miya sai dai kuma ta kwashe duka naman dake cikin miyar. Haka ma ta buďe salad ďin ta tsince kwan dake ciki tas sannan ta rufe ta koma gefe tana cin abincinta, sai da ta kusa gama cin abincin ne sannan Hajiya Goggo ta shigo ďakin.
Kallon Maryam tayi sannan ta maida kallonta kan plate ďin hannunta tace "ke kuma yaushe kika shigo?" Bakinta fal da shinkafa tace "ban daďe da shigowa ba dama kuma ina jin yunwa shine naga abinci anan na ďiba inaci".
Salati Hajiya Goggo ta saka tana tafa hannayenta. Warmers ďin ta buďe, ta shinkafar dai ta gani kaďan ta ďiba a ta miyar ne taga aikin da Maryam tayi don bata ga alamar akwai sauran nama a cikin miyar nan ba. Buďe plate ďin salad ďin tayi taga Maryam duk ta tsince kwan dake ciki.
Takaici ne ya kama Hajiya Goggo na irin wannan aiki da Maryam tayi mata. Juyowa tayi taga Maryam har ta gama cin abincinta tana wasa da digital tasbahan Hajiya Goggo dake ajiye a kan bedside drawer.
Haushi ne ya kara kamata da har bata san lokacin da ta kaiwa kan Maryam rankwashi ba, ta kama mata kunnenta tana cewa "ashe ban hanaki taba abinda ba'a baki ba eh. Wato ke kunnenki na kashi ne ko da ba kya jin magana kwata-kwata. Idan abincin kike so me ya hana kije kitchen ki ďiba shine kika zo nan kika kwashe naman miyar tas, to zaki gamu da Ali don kuwa abincin shi ne kika ďiba kin kuwa san halinshi ba kyaleki zai yi ba".
Tana samu Hajiya Goggo ta cika mata kunne tayi wuf ta fice daga ďakin tana sauri ta bar gidan kada Yaya Aliyu ya shigo ya iske ta don ko bi ta kan Hajiya Goggo dake kwala mata kira bata yi ba. Da ta san abincin shi ne ma da babu abinda zai saka ta taba mishi.
A bakin gate kuwa ta haďu dashi zai shiga gidan, sauri tayi ta matsa ta bashi hanya ya wuce sannan ta kwasa a guje zuwa gida don gani take yi tamkar yasan abinda ta aikata.
Kindly vote, comment & share, thank you.
UMMASGHAR.
DU LIEST GERADE
MARYAMU
RomantikHarararta Aliyu yayi jin abinda tace sannan yayi tsaki ya dauke kai, cikin ranshi kuwa cewa yakeyi yarinya bakiyi karya ba don kuwa sosai na tsaneki ko sha'awar ganinki banayi.