Autar mata

6.1K 208 16
                                    

Na Heendert .A. Baffa
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un abinda take ta maimai tawa kenan a yayin da take durqushe a tsakar dakin ta Wanda yasha ledar tsakar daki , tun tana daurewa har ta kai ga ta kasa ihu kawai take tsalawa yayin da naqudar ta turniqeta , Laure wadda ta kasance kishiyar ta tana cikin nata dakin ta jiyo ihun abokiyar xaman tata ta qara gyara kwanciyar ta. Kamar ranta xai fita haka take ihu amma ta rasa mai kawo mata dauki har ta haifi xankadediyar yarta mai kama da ita kamar tayi kaki ta tofar , tana cikin axabar ciwon amma hakan Bai hana ta rarrafa ta dauko yarta wadda ke ta tsala ihun shigowar ta wannan gida mai cike da qalubale irin irin kala kala wato (duniya). Qaunar yarinyar ta cika ranta amma tana tunanin yadda take cikin wannan hali da wuya tayi rai,a take jini ya balle mata ta fara daukar jini male male take kwance cikin jini rai a hannun Allah sai ga qaninta Wanda ya kasance dan uwanta na jini riqe da hannun sauran yaran wato Isma'il da Ruqayyah wani wawan ihu Ruqayyah tayi ganin mahaifiyarta kwance male male a qasa bata ko motsi take ta rungume ta tana fadin Umma ! Umma ki tashi ..........Abdallah ya qaraso gurin cike da rudani ya daga hannunta sharaf hannun ya koma hankalin sa ya tashi da sauri ya nufi waje wurin wata makwafciyarsu a gigice ta fito koda taje rai yayi halin sa. Akaxo aka shiryata aka Kaita gidan ta na gaskiya Yayin da ta tafi tabar yaranta guda 3 wato Isma'il, Ruqayyah da kuma jariri yar ta da a halin Yanzu ko suna ba a rada mata ba.
Abdallah ne xaune a daki shi kadai yake tunanin anya ba'a shiga haqqin matar nan ba kuwa an kashe mijin ta itama kuma ba'a barta ba an biyo ta an kashe ta.
ASALIN LABARI
Malam sani Wanda yake a garin qauyen madaci Wanda yake cikin qaramar hukumar rano yana da matansa biyu Laure ita ce uwar gida bata taba haihuwa ba.Malam sani ya kasance a gidan sa na gado wanda iyayen sa suka bar masa gado gidan kara ne duk ya rube ya lalace, a lokacin da ya hadu da matar sa ta biyu wato binta yana mutuqar sonta ta amince ta aureshi duk da bai da wani abin hannun sa kuma ya fada mata a qauye xasu xauna bayan ita din yar rano ce . bayan an daura auren su ba da dadewa ba ya samu aiki a wata qaramar primary a rano wanda albashin sa bai haura naira #20,000 ba ya fara aiki yana Tara kudin sa har ya samu ya Gina wani dan madai daicin gida. Sai ya yanke shawarar ya fara mai da amarya can kafin ya Gina wani sai uwar gida ta koma, koda ya xowa da amarya maganar nasiha ta fara mishi da cewa bai kamata uwar gida na nan ita a fara dauketa ba amma ina yace Sam shi ba Laure yama gini ba ita yama a haka dai harta yarda tace xata koma ko washe gari bayan sun gaisa da Laure take fada mata ta fara shiirya kayan ta gobe xasu koma sabon gida laure baki yaqi rufuwa ko washe gari malam sani ya turo mota domin a kwashe kayan binta aka cika mota da kaya laure ta hau gaban mota tama Binta sallama ta tafi su laure aka tare a sabon gida koda dare yayi malam sani yaxo ganin sabon dakin amaryar sa amma abin mamaki wa xai gani..........

Autar mata ban ma fara ba ku biyo ni masoya na

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 24, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Autar MataWhere stories live. Discover now