31

1.1K 79 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

           3⃣1⃣

             A gidan su Zee zasu Kwana kasan cewar mai lallen a unguwar take kuma sai da safe za'a masu bakin kunshin,

       A can gidan su Ama kuwa mutane sun hallara an fara cika, su kawu kuwa daman kwanan su biyu da zuwa su da iyalansu yasa aka bude masu gidan kusa dasu  sosai sukayi mamakin irin arzikin su Abubakar

         Karfe sha biyu suka nufo gida daga gidan su Zainab kasan cewar sun gama lallen da wuri, tin da sukayi parkn Abdul ya gano su ta window,

      Numfashin sa ne ya fara barazanar barin jikin sa sabida ganin yadda Marwiyya tayi masifar yi mashi kyau a ransa ya furta gwamma da aka hanashi haduwa da ita dan zai iyayin ba dai dai ba, har sai da suka shiga cikin gidan sannan ya saki labulen da kwanciya bisa gado lumshe idonsa yayi saboda jinsa a wani yanayi sai da ya kusa sec goma sannan ya Mike ya shiga wanka


          Karfe biyu mai kwaliyya tazo ta fara sansarawa masu kwaliyya gaba dayan su suna sanye cikin wani dakaken lace red an musu riga da zani dinkin buba kasan cewar kamu ne, head da komi da suka saka red ne, masha Allah abinda kowa ke fada kenan,

       Bayan an gama masu aka fara yiwa Zainab da Yasmeen kawar Amatullah da sukayi secondary school tare yar garin bauchi ce zuwan ta kenan ana yi masu kwaliyya, su Zainab suka shirya cikin atamfa fara mai ratsin blue suma dinki buba ne


         Karfe biyar aka gama masu komi gaba daya sukayi hotuna iri iri sannan suka fice suka shiga mota

         A bakin wani katon gida ne mai bakin gate mortar tayi parkn, mai gadi yayi saurin bude gate din suka Shiga, "masha Allah" abinda muka dinga mai maitawa ni da Mzz Daddy kenan saboda yadda wajen yayi masifar saruwa anyi decoratn da red an white kalar atamfar kawayen, wajen da aka tanada dan amare ma abin kallo ne kawayen su guda goma aka kira dan rako amare mazaunin su kasan cewar babu maza, a hankali suke taku har suka iso wajen zaman su nan aka dinga masu hotuna minti goma cikake dj ya ba wa mutane dan suyi hotuna, bayan sun gama hotuna aka bude taro da addu'a nan aka fara gudanar da program daya bayan daya cikin nutsuwa, an ci an sha kuma ansha rawa tsayawa fadar yadda kamun yayi kyau bata lokaci ne, karfe bakwai aka gama taro suka koma gida


        Zaune suke a tsakiyar dakin Marwiyya suna hira wayar Marwiyya tayi kara ganin Abdul ke kiranta yasa tayi dariya tace har ya gama fushin kenan a ranta

        Dauka tayi tare da karawa a kunnenta tace "Assalamu alaykum" ciki ciki ya amsa tace "anyini lpya" lpya ya fada a takaice, "ke baki san mutum na fishi ki bashi hakuri ba koh" dariya tayi, hade ransa yayi kamar tana ganin sa yace "au dariya ma na baki koh" girgiza kai tayi "am sorry sweat kasan ina busy ne kuma kasan in kana fishi hankali na baya taba kwanciya har sai na tabbata ka hakura amma kayi hakuri yanzu ka hau watsapp na turama pixs din yau" sosai yaji dadin furucinta ya yi mata sallama tare da kashe wayan ya kunna data, Marwiyya ta tura mashi hotunan ya dinga kallah har yayi bacci



             Zahradin ne kwance yana bacci, wayar sa tayi kara a hankali ya lalubo wayan lokacin ta kusa tsinkewa ya daga tare da karawa a kunnensa ya furta "Hello" a cikin Yan bacci, jin alamun bacci yake yasa Amatullah kara kufula saboda rabon da ya kirata tin shekaran jiya da daddare

        Jin anyi shiru ba ai magana ba yasa Zahradin furta waye dan ko duba sunan baiyi ba, kuka ne ya kufce mata yasa tayi saurin kashe wayan, jin kukan Amatullah yasa shi saurin mikewa lokaci guda bacci da yake tartare dashi ya gudu

        Ganin Amatullah na kuka yasa Marwiyya matsawa kusa da ita "sisto me aka miki kike kuka?" Cikin kukan tace "yaya ne yace wai bai gane ni ba" zaro ido Marwiyya tayi kafin tai magana wayar Amatullah tai kara ganin Deen ke kiranta yasa taki dagawa sai da ya kira kusan sau shida ba a daga ba daga karshe ta kashe wayan gaba daya

         Ganin Amatullah ta kashe wayan yasa shi kiran Marwiyya bugu uku da dauka "Ina Ama" ya tambaya "gata yaya na bata" eh bata" mikawa Ama wayar tayi tace "gashi inji yaya" hararta tayi "bazan karba ba din" karawa tayi kunnenta yaya kaji me tace "eh naji, plsss sisto ki bata hakuri wallahi bacci nake kawai na dau wayan kuma batai magana ba ni kuma bn duba sunan ba" toh yaya zan bata hakuri, nan sukayi sallama

       Duk yadda Marwiyya ta shawo kan Amatullah taki dole ta hakura, shi ko Zahradin juyi ya dinga yi da kyar ya samu bacci barawo ya sace sa


            Washe gari ya kama alhamis ranar za ayi party Wanda abokanan su na office suka shirya masu iya yan mata da samari ne babu matan aure babu yara

            Tin da Zahradin yayi sallar Asuba ya fara kiran Amatullah wayar avkashe hakan yasa ya nufi dakin Abdul nan suka danyi hira har ya tura masa pixs din kamun jiya, nan suka dinga yaba kyawun amaren nasu

          Karfe tara Mumy ta kawo masu break fast sukayi break fast sannan suka fice gaba daya Zahradin a takure yake dan bashi da burin da ya wuce Amatullah ta yafe mashi

        Karfe hudu na hango motoci kusan guda goma reras a kofar gidan su Marwiyya ana ta dibar yan matan amarya ana kaisu wajen partyn suna sanye cikin green din lace da red din head duk sunyi dogayen riguna da su,

       Dakin su Amatullah na leka nan na hango angama yiwa amare kwaliyya suna sanye cikin wani material golden head da komi da suka saka golden sun yi masifar yin kyau

       Kawar Mumy ce ta turo kofar tace ku fito angwaye sun zo suna jiran ku suna waje, tana fita suka mike su hudun sukayo waje



TEAM AISHAMS🤝

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now