page 6

2.7K 199 2
                                    

🌑 🌑 *B🅰K'IN D🅰RE*🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑

     *Written by*
💅💅 *Sadnaf*💅💅

  
*A heart touching story*

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    _ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş_

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*WANAN SHAFIN NAKU NE MASOYANA NA ASALI MASU KAUNATA TUN KAFIN SU SAMU CONTACT D'INA MASU K'AUNATA BADAN RUBUTUNA BA*

*FRESH KHADY*
*HALEEMA LEEMA*
*AISHA YAR ALJANA KAUNARKU HAR ARAINA WLH ALLAH YA BARMU TARE*💜💜💛💙💜💛💙💚❤💔💔💔💔


*My Salmab rigimamiya ina gaisuwa*


*Page 6*

Batare da b'ata lokaci ba yaje ya nemo wani boka dayake cewa kansa Mallami akan ya ringa musu aiki kafin su fita operation sabida yanayin aikin nasu akwai Hatsari

Mai gida ake cewa Mallamin inda yayi fice sosai akan tsubuce tsubuce ba iya b'arayi yake yiwa aiki ba harda matsafa da kidnappers

Kafin su  fita operation sai sun fara zuwa wajensa ya duba musu akwai sa'a afitar tasu ko babu kamar kuwa mai gani amadubi dan duka yanda operation d'in nasu zai kasance Mai gida sai ya gaya musu har wani zobe ya bawa Alhaji Bala akan yasa A tsakiyar yatsan shi na hagu indai da akwai danger a duk inda suke ko kuma ana nemansu zaiji zoben hannunsa  na mishi zafi

Da wanan d'aurin gindin da Alhaji Bala ya samu awajen Maigida yasa ya rufe ido yake farautar dukiyoyin jama'a da rayakansu babu d'igon imani ko kad'an a zuciyarsa tamkar yanda zaka kashe Sauro kana daga cikin d'aki haka yake kashe mutumin da ya nemi ya mishi gardama ko kuma ya hana shi kud'i ga fyad'e da bai d'auke shi a bakin komai ba dan in dai zai fita operation indai yayi tozali da mace wala  mai Aure ko  buduruwa to fa sai ya mata fyad'e dan yana cikin sharad'un mai gida ya ringa yiwa mata fyad'e


Tuni Alhaji Bala ya zama kungurmin dan fashi Dan yanzu ba iya matafiya yake tarewa ba har manyan gidaje yake zuwa fashi idan kuwa yaje fashi  tsautsayi yasa babu kud'i a gidan to fa aranar sunanku gawa Dan bazai fito batare da ya d'auki rai ba

Ad'aya b'angaren kuwa Mahaukatan kud'i kawai yake Samu Dan bai fiye sakarwa su lion kudi ba sosai he is very selfish ga wayon masifa duk abinda su lion zasuyi idonsa na Kansu dan bayaso suyi betraying d'inshi kamar yanda yayi betraying d'in Oganshi Chris


Acikin kanensa babu Wanda bai Mallakawa gida ba banda Mahaifiyarsa da ya tamfatsawa wani katon gida da masu aiki

Albarka Saude kawai ke sa mishi Dan duk a tunaninta aikin da Alhaji Bala keyi ne Allah yasa mishi Albarka

Yan cikin garin kuwa irin kud'in da suka ga Alhaji Bala na samu ne cikin kankanin lokaci  yasa suka fara tunanin ko dai yana yankan kai ne


Abinka da Kauye tuni kananan maganganun da yan garin ke yi ya koma kunen Mahaifiyar Alhaji Bala data tashi daga mai dan wanke zuwa Hajiya Saude sabida duk shekara Sai Alhaji Bala ya biya mata Umara da Hajji

Hankalinta ne ya tashi data ji abinda yan kauyen ke cewa inda ta nemi Alhaji Bala da yazo da gaggawa tana so taganshi aikuwa babu b'ata lokaci yaje ya sameta


Murmushi yayi a lokacin da Hajiya Saude ta gaya mishi zargin da ake mishi agari inda ya musanta zargin da ake mishi yace aikin mai yake yi kuma kowa yasan aikin mai na kawo kud'i

BAKIN DAREWhere stories live. Discover now