KOMAI DAIDAI NE...
"Malam Lawan ka ce ka ga fitowar Hamza a gidan mintuna uku da kashe Zainab ?" cewar barista Zulaihat, lauyar wanda ake zargi.
"Haka ne." Cike da karfin gwiwa malam Lawan din ya amsa wanda ke tsaye, kange a inda ake tsaida masu bayar da shaida.
"Hmmm! Ta ya aka yi ka san mintuna uku ne tazarar da ke tsakanin mutuwarta da kuma fitowar Hamza daga gidan?" Ta kuma tambayarsa a karo na biyu.
"Na kimanta lokacin fitowarsa 02:08pm ne da sakamakon lokacin mutuwarta 02:05pm da likitoci suka fitar ne." Ya ba ta amsa.
"Haka ne?"
"Haka ne."
"Ko za ka iya fadawa kotu kalar kayan da Hamza ke sanye da su a lokacin?"
"Ba zan iya ba."
Gungunin da jama'a suka barke da ita ne sanadiyyar amsar malam Lawan ta tilastawa alkali buga yar gudumarsa a kan teburi da gargadin a yi shiru.
"Da ranan!" Barista Zulaihat ta dora bayan kotun ta tsagaita da surutun.
"Eh. Ina da matsalar bambance launi, ina kallon komai a baki da fari ne."
"Aiya! You mean you are colour blind ?"
"Exactly."
"Amma ai kana iya bambanta fuska da shaida mutane ko? Misali matarka da kuma yarka."
"Kamar ya! "
"Ina da ja ya mai shari'a, kamar tambayoyin da lauyar wanda ake tuhuma ke yi sun kauce hanyar wannan shari'ar." cewar barista Malik lauyan masu shigar da kara.
"Barista ki kiyaye." inji alkali.
"Zan saukaka ma'anar tambayar ya mai shari'a." cewar barista Zulaihat cike da girmamawa kafin daga bisani ta juyo wa malam Lawan da wata tambayar.
"Ina nufin za ka iya fada mana ko wacece waccan sanye da koren hijabi daga sashen mata layi na biyu ? "
"Sosai ma. Hajiya Rabi'atu ce mahaifiyar Zainab."
"Da kyau ! Amma ta ya ka gane ita ce kai da ba ka tantance kala?"Ina zuwa...
YOU ARE READING
Komai Daidai Ne...
Mystery / ThrillerLabarin nadama da daukar fansa a kurarren lokaci. "A wannan rayuwar babu wani abu ba daidai ba, ya danganta da kusurwar da mutum ya kalli abun ne. Duk muni ko kyaun abu yana daga kallonka ne; idan ka kalla da soyayya, babu abun da za ka ji face shau...