🧕RAYUWAR AURENMU🧕 WRITTEN BY MAMAN RUFAIDA (Yar Aljanna) *🌈KAINU

79 1 0
                                    

🧕RAYUWAR AURENMU🧕



WRITTEN BY MAMAN RUFAIDA
   (Yar Aljanna)



*🌈KAINUWA WRITTEN ASSOCIATION🤝*





*Godiya ta tabbata ga Allah mai Girma Amince Allah ya tabbata da shugabanmu Annabi S.A.W*

*Gaisuwa mai tarin yawa zuwa ga yan uwana musulmai.jinjinar ban girma ga matan  kainuwa Allah ya barmu tare Ameen...*

*Edited:-By 💞Mrs💞Mansoor💞*




PAGE1⃣




Tsaye na ke ina  duban mai gidana ina sanye da wasu English wears,riga da wando wadanda suka matse min,suka fitar min da siffofin jiki na,shi kuwa gashin kaina na gyara shi,yayi kyau kwarai ga shekin da yakeyi tamkar yanzu na fito daga diraya ya zubo min har ga kafaduna.

Mijina yana zaune a kan dining table,ba abinda yake yi,sai aikin kallona tare da murmushi,ina rike da mudubinsa da hularsa da agogonsa a hannuna,a yayin da na sunkuyo na zauna,ina murmushi tare da yi masa(kiss) a kuncinsa.

Shi kuwa tun fitowata yake kallona yana murmushi,har na zauna,sai ya janyoni ya azani kan cinyarsa yana sunsunar kamshin jikina,ina murmushi nace "a'a my one ya akayi baka kirani ba?ka zauna zaman jira na?"yace "Haba my love,ya za'ayi in katseki daga abinda kike yi?dama na san kina can ki na tsala ado tamkar wacce zata je zabin sarauniyar kyau"

Sai na shagwab'e murya nace" kai my one akwaika da kod'a mutum."Haba my love wane irin kod'a mutum,ai ko kamshin turaran na ki kadai baya barin mutum ya lek'a koda bakin k'ofa ne."sai nayi murmushi, sannan na bud'e plate mai d'auke da soyayyar kaza da dankali da kwai da plantain da na tanada domin Break fast,na dauko fork na sanya a sama.

Na aje a gabansa,sannan na had'a masa tea na aje masa na zauna muka fara break kamar yadda muka saba,cikin walwala da nishad'i,bayan mun kammala ne my one ya jawoni jikin sa yana shafar gashin kaina,yace"my love kin ga abinda ke burgeni da ke,saboda yawa kulawar ki a gareni da kuma iyayyena,shi ke sa ina k'ara jin sonki da k'aunarki fiye da yadda kike zato,kuma shi ke sa ba na kallon ko wace 'ya mace in ba ke ba."

Watau my one yana wannan zance,gani na ke kamar nafi kowace mace dacen mijin na gari a duniya,don na kan ji dad'i,har in mance duniyar da nake ciki,sai in kasance cikin farin ciki,sai na ji ya tallabo fuskata,ya kama baki na yana min kiss.

Ni kuwa ina k'ara narkewa a cikin jikinsa,s cikin kisisina nuna sonsa na sa hannuna daya cikin sumar kansa,dayan  hannuna yana shafar k'irjinsa,da yake Allah yayi masa baiwa da gashin k'irje,ina fadar wasu kalmomin soyayya masu sanyaya zuciya.ina cewa.....hmm kijira don jin wad'annan kalamai😂😂😂😂



*By Maman Rufaida*
*🧕RAYUWAR AUREMU* 🧕

*WRITTEN BY MAMAN RUFAIDA*
   *(  YAR ALJANNA)*

🌈 *KAINUWA WRITTEN* *ASSOCIATION*🤝

*Edited by Ummy Ontop*


Page2⃣


"My love you and I will never stop loving you for ever!kuma bani kaunar abinda zai nisantani da kai har abada da kaunarka a gareni.
my love nafiso duk sakan daya inji dumika  a jikina,kuma kaunarka tana neman ta zautar dani.

Kaine wane sashe na rayuwata,kuma Kaine tushe inganta rayuwata har ka tafi da imani na da gangar jikina gaba daya,kaine d'a namijin da kowace mace take muradin ta mallaka a matsayin mijin aurenta,kuma Kaine uban 'ya'yana kuma ba zan taba daina yima addu'aba,sai ranar da raina yayi halinsa Kaine......sai kawai naji bakisa ciki nawa wanda yasa na kasa inda abinda zan furta na rasa duniyar da nake,

RAYUWAR AURE MUWhere stories live. Discover now