Sallar wallaha

22 2 1
                                    

HUKUNCE HUKUNCE GUDA 15 NA SALLAR WALLAHA

Darasi na Farko

1-Minene Hukuncin Sallar Wallaha??

Ibn Baz Allah yayi masa Rahama yana cewa;
"Sallar wallaha sunnace mai karfi,Annabi s.a.w ya aikatata kuma ya kwadaitar akan yinta kuma yayi wasiyya da Shiryar da Sahabbai akan yinta".
@ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ‏( /11 396 ‏) .

2-Minene Falalar Sallar wallaha??

Sallar wallaha tana da lada da falala mai girma kuma mai yawa, ga wasu daga cikinsu:-

1-Hanyace ta Samun kariya daga Allah

(Wanda ya sallaci Raka'a guda hudu na wallaha yana samun Tsaro na musamman daga Allah har ya zuwa karshen yininsa).
@Sahihul Targheeb 671

2-Alamace ta Bayin Allah na kwarai.

(Babu mai kiyaye Sallar wallaha sai Bayin Allah na kwarai, domin Sallar bayan Allah ne Na kwarai).
@Sahihul Jami'I 7628

3-Tana cikin Wasiyyar Annabi s.a.w ga Sahabbai

(Annabi saw yayi daga cikin Sahabbansa wasiya akan kada ya sake ya bar aikata abubuwa guda ukku:
a. Sallar wallaha
b. Sallar Wutiri kafin ayi barci
c. Azumi uku a kowane wata)
@Sahihun Nasa'I 2403

4-Sauke hakkin sadaka da Allah ya dorawa dukkan gabbai a kowane yini

(Jikin Dan Adam yana da gabobi guda 360,kuma kowata gaba Allah ya dora mata aikin sadaka kowata rana.Amma wanda yayi Sallar wallaha raka'a guda biyu ya biya dukkan sadakar da aka dorawa gabbansa)
@Sahihu Abu Dauda 5242

5-Sunnace ta Annabi s.a.w

(Manzon Allah saw yana sallatar wallaha Raka'a hudu kuma yana karawa yadda Allah yaso)
@Sahihul Jami'I 4959

6-Hanyace ta samun gida a aljanna

(Wanda ya sallaci Sallar wallah raka'a hudu sannan yayi wata raka'a hudu. Ma'ana raka takwas ayi hudu a yi sallama sannan ayi hudu ayi sallama. Allah zai gina masa gida a aljanna).
@Sahihul Jami'I 6340

7-Samun ladar aikin Umara

(Wanda yayi tsarki na Salla sannan ya fita dan yin sallar wallaha. Babu abinda ya fito dashi sai Sallar wallaha. Ladansa kamar ladar mai aikin umarane awajan Allah).
@Sahihul Jami'i 6228

8-Samun Ladar aikin hajja da Umara ga wanda ya zauna yana ambaton Allah bayan sallar Assuba har rana ta fito sannan ya tashi yayi Sallar wallaha.

(Wanda ya sallaci sallar Assuba acikin jam'I sannan ya zauna yana ambatan Allah har sai da rana ta fito. Yayi sallar wallaha, to yana da ladar aikin hajji da umara cikakku.
@Sahihut Targheeb 469

3-Wani lokacine ake yin Sallar wallaha??

Ibn Baz Allah yayi masa Rahama yace:
"Lokacin Sallar wallaha yana farawa daga lokacin da rana ta fito kuma ta dan ďaga daida girma abin mashi daga nan har zuwa gab da Zawali wato gab da karkatawar rana daga tsakiya,amma mafi falalar lokacinta shine mutum yayita lokacin da rana ta fara zafi sosai"
@ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ‏( /11 396 ‏) .

~wato daga 11am zuwa 11:45am"

~Ana farawa alokacin da rana tafuto ta dan daga sama kamar misalin karfe 7:00am anan nigeria.

~Anan dainawa alokacin da rana ta fara karkatawa daga tsakiya.

Allah ne mafi sani.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 04, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SALLAR WALLAHAWhere stories live. Discover now