💥AHALAM💥
Love story
written by khairat upF.O.W
11
Duk suna zaune ne a cikin garin kano inda kowa gidan shi daban. kanwar su AMINA ita ke aure a gombe da mijin ta barrister ne.yaran ta uku duk maza MUHAMMAD, SAIFULAHI, YUSUF.
alh.muhd ya rasu sanadiyan wani ciwo da ya kwanta wanda be tashi ba harkokin shi sai umar abbu yake kula dasu bayan sun yi shawara da yan'uwan su tunda shi ne babba garuruwa biyu na sane da zaman family din alhaji muhamad umar kumo.
ahalam ta taso cikin gata da so a gun iyayyen ta saboda sunan hajjar su da ta ci dan a gun hajjar ta taso wata iriyar gata da sangarta hajjar ta dora wata wanda ya sa ta ke da tsiwa ga rashin kunya amma akwai ilimi.
ahalam ta dawo gun abbun ta ne bayan rasuwar hajja ahalam ta sha kuka kamar me
ba wanda ya isa ya taba ahalam nan da nan su abbu zasu nuna bacin ransu shi sa ma take abunda take so.
''ahalam ta hadu da ahamad ne a gombe taje gidan mama amina hutu ranan sun fita unguwa da saifullahi a wajan shan ice cream ya mata magana cikin ikon Allah ta amsa masa hakan nan ya kwanta mata a rai taji ya yi mata gashi dan gayu me tsafta ma'abocin kamshi. exchanging num suka yi lokacin tana ss2.''
'' ahalam wato ni naji ina son ki kuma kin kwanta min a rai tunda na dawo nake tunanin ki har gizo ki ke mun wallahi.
murmusawa tayi tace nima ka kwanta min a rai fatana mu fahimci juna.kar ki damu ni bada wasa nazo ba na miki rikon gaske dan har na fadawa mum dita dazu ta mun murna sede ni zan yi kewar ki ba dan gombe ba ne mazaunin kano ne nazo bikin abokina ne kuma gobe zan koma amma na fasa se na zo mun sake ganin juna tukuna nida ke!''
'' ai nima ba nan garin nake ba ni ma yar kano ce ka kwantar da hankalin ka sede gani na ze ma wuya sede wayar dan ko ba a bari na kula samari se na kammala sec sch.''
'la'ilaha illalahu kina nufin sede muyi ta waya?''
'eh wlh, shikenan kina wat'saap ko instagram? aa duk bama yi doka ce ,shi kenan fada min sunan ki murmushi ta kuma yi tace masa AHALAM wow ni kuma AHAMAD,sunan ka da dadi kar ki zage ni ai be kai naki ba amma zabar min suna yanzu ta kulle ido tace masa my only ni kuma zan na kiran ki my lady! ta kulle idanun ta tana dariya 😄.
sai da safe naji mama na kira na kar taji ina waya zan na ma flashing seka kira amma kar ka kira tukuna shi kenan my lady an gama seda safe zan yi kewar ki nima haka.
wai ahalam me ki ke tun dazu a bandaki kusan 30min?uhm kawai na ji ciki na ya murda mun ne wallahi
a kawo miki magani? no zan kwanta zan samu relif,ok seda safe kiyi addu'a fa kamin ki kwanta ok? to gudnyt same2u.
tun daga lokacin ahalam da ahmad ke soyayya a boye ba wanda ya sani har wattsapp seda ya sa ta bude ya sa ta bude insta ba wanda ya sani a nan suke hira amma wata num daban take using a chart din.
ta tura masa pics din ta shima haka suyi vedio call su raba dare suna waya.
tana kammala ss3 ne ta fadawa umman ta a kan ahmad ita kuma ta fadawa abbu.
wannan shi ne mafarin soyayyar ahalam da ahamad wanda ahalam ke mugun so saboda ya koya mata hot love ashe shi din munafuki ne manemun mata ne dan iska ne ya yaudare ta ya boye mata kan sa ahamad u cheat me se kuma na nuna ma wacce ce ni!.
''kwana 2 tsakani ta gama shirin ta na tafiya skul su aysha suka dauko ta.
wannan semister din ma dr.adnan zai dauke su a aji
tayi mamakin yadda kamanin sa suka sauya ya yi kyau ya yi kiba har haske seda ya yi.
yana sanye da shadda fara ta sha aiki da bakin zare ya kafa hula
kafe shi tayi da ido sannan ta gaida shi amsawa yayi da fara'a ya ga ma ta rame tayi duhu kadan ba kaman da ba tayi kashin wuya ya kare mata kallo ya dauke kai ya ce auzubilahi
amarya ina angon naki ya barki ki ka fito?
yake ta masa tace ya adnan ashe kai din me kyau ne ko kuma antyn mu ce ta iya kiwo?
hah haka ma zaki ce? ai gaskiya ce naga da kai chocolate colour ne yanzu kuma ka fara rikidewa me sirrin?
murmushi yayi yace kwanciyar hankali da zumar kauna daga matata ke ai ahmad rago ne be iya kiwo ba a cikin hasken ki kin rage kin rame fada mun me damuwar ki?
suna tafe suke wannan hirar ana ta kallon su wasu na gulma ko ita ce matar sa? aa inji wata sam matar sa daban wanan kanwar sa ce.
ya adnan bani da damuwa seta kewar abbu na da umma idanun ta suka ciko ya ji wani irin abu ya tokare masa kirji besan dalili ba.
yau dai ga adnan ga ahalam na hira
masu karatu ku biyo ni dan jin sauran bayanin
juma'at mubarak
YOU ARE READING
AHALAM!!
Romancethis is a love story,a triangle story between 3 lover's, familiy courtship, love,betrayal i think you had like this story!