SUHAILAT

8.3K 162 4
                                    

🧕🏻SUHAILAT🧕🏻

1to5

NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA

Da fatan anyi sallah lafiya Allah ya amshi ibadun mu yasa muna daya daka cikin wa inda aka yanta amen

Da sunan Allah mai rahma mai jin qai wanda ya sake bani daman rubuta wannan littafi mai suna suhailat yanda na fara lafiya Allah ka bani ikon kammalawa lafiya dan alfarman annabi (s a w)

Yau an tashi garin da sanyi kasancewan anyi ruwa jiya da daddare a garin gombe kasancewan lokacin zafi ne, duk wanda zaka gani yana cikin nishadi domin sanyin da akeyi, garin gombe ya tara mutane kala2 musamman manoma, baya ga haka garin Sun rike kasuwanci bada wasa ba, yayin da zaka ga koda karamin yaro ne ko yarinya zaka ganta da tallah akai tana yawo, yayin da wasu suke zaune waje daya suna saidawa,. A gefe wata yarinya na gani da tire a gabanta ta zauna ta zabga uban tagumi Kana ganinta Kasan tana cikin damuwa, wani na hango kusa da ita yana fadin suwale lafiya kuwa inata magana shuru? Ko abincin bana saidawa bane,? Cikin sauri tace yakuri ban jika bane na nawa zan baka? Ya bita da kallo yana hadiyan yawu, yace bani na hamsin,cikin sauri ta dauko ta mika mishi shinkafa da wake da mai da yaji, da yake abincin a jere yake ansa ko wanne a roba an rufe da bakar leda, yana ci yana kallonta tare da hadiyan yawu, yace suwale yaushe za'a kawo min ziyara ne? Cikin rashin fahimtan kalman take kallonshi ganin yanda yake kallonta yasa tayi saurin kasa dakai , ganin haka ya washe baki dan yana ganin zai samu nasara, wani daka gefe yace oga ya kamata mu tafi fa kasan yau akwai fita? Muje mu gama shiri, lokaci daya ya mike tare da ciro kudi ya mika ma suwale yace gashi gobe zanzo sai mu karasa magana, dan zaro ido tayi tace uban daba bani da canji, yace ki rike, nabar miki canjin ta amsa tare dayi mishi godiya, sannan ya wuce, bata wani dade ba aka siye abincin wanda duk yawanci yaran uban daban suka siye domin inda mai gidansu yake cin abinci suma anan suke ci .

Bayan ta karasa gida cike da murna domin Tasan yau babu duka, dan ta siyar duka, ba kwana biyu da suka wuce ba wanda take yin kwantai domin uban daba baya gari, Sun tafi wani aiki cikin garin gombe, da sallama ta shiga cikin gidan, ba amsa sallama sai uban harara da yayi mata maraba da zuwa, ta dan tsugunna a gefe tare da fadin Inna na siyar duka, cikin washe hakora tace ko kefa, miko min kudin,tayi sauri ta kwance zani ta bata ciki harda canjin da uban daba ya bata, duka ta hada mata, cikin washe hakora inna tace, yau kuma waya miki juye? Tace ba juye akai min ba, dalla yimin shuru ubanki aka miki inba juye aka miki ba,ya akai kudin yayi yawa? Cikin sarkewan murya tace uban daba yabarmin canjin nace bani da canji yace in rike, ta kuma washe baki jin an ambaci uban daba, domin kaf matasan bambam babu mai kudin uban daba, inna ta miko mata wani gutsirarran biredi gashi kici nayi baki na basu kasonki, cikin sauri suwale ta amsa tana ci kaman tana cin nama haka ta cinye, wanda inda za'a ce ta koshi amsar a'a zata bayar domin tana jin uwar yunwa rabonta ta abinci tun jiya da rana, saboda horan yunwa da inna ta mata yasa kwata2 bata cin abinci da yawa daka taci kadan sai taji ta koshi, wani lokacin ma in tana ci saita dinga yun kurin amai, wani zubin kuma sai taji kaman ana daure mata zuciya ko ana muntsilin zuciyar wannan kenan.

WACECE SUWALE

Gida ne na kasa Kana ganin gidan kasan talauci ya musu katutu, bawai su kade bane talakawa a garin ba, a'a zan iya cewa kaman sunfi kowa talauci a garin, sai dai duk da talauci irin na malam musa, yana tsaye a gidansa wajan basu tarbiya, kasan cewan ya samu Mace ta gari inna laure, sai yasa baya samun matsala musamman wajan yanda Take bama yayanta tarbiya kasan cewan mata Allah ya bata, sunyi aure da malam musa tun saurayi da budurwa saida suka shekara uku da aure Allah yaba inna laure ciki,lokacin da ta gano tana da ciki tana ta jin kunya kun san Fulani lolz ,suna ta rainon cikin har Allah yasa yakai watan haiyuwa cikin daren monday inna laure ta tashi dana kuda kasancewan garin babu asibiti domin duk wanda yasan bambam yasan kauye ne domin ko wutan lantarki babu a garin, haka tai ta fama da azaba har wajan biyun dare inda ta haifi yarta mace, malam musa yayi murna sosai, ran suna taci sunan hadiza, inna suke kiranta da dije,

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 07, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SUHAILAT Where stories live. Discover now