ZAWARCI MAI TSADA

113 4 0
                                    

*ZAWARCI MAI TSADA*

*DAGA ALK'ALAMIN*
      *Meesherh lurv*

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

_Follow me on wattpad@meeshalurv_

_DEDICATED TO_
*SADIYA ABDULLAHI SHEHU*
( _Stylish bch_).

5⃣9⃣

Nan ta tattara magungunan ta ajiye su a durowar gefen gadonta sannan ta shiga wanka. Ta fito sanye da doguwar riga Hijab 'yar k'aramar himar daidai k'irjinta inda ta sa mukulli ta bud'e motarta k'irar Kia picanto ta yo ficewarta yawon shak'atawa....

    Bata tsaya a ko ina ba sai  _milliniun park_, inda ta tsayar da motarta ta yi fakin a inda aka tanadar don fakin d'in motoci. Ta d'auko _Sans cream soda drinks_ daga cikin wata 'yar k'aramar _cooler_ dake cikin motarta inda ta nufi cikin harabar _park_ d'in.

Samari ne da 'yan Mata masu ji da kansu ke shak'atawa a cikin wannan _park_. Duk Wanda ka gani a wurin fuskarsa cike take da fara'a.

  A can wani gefe guda kuma _birthday party_ ne ake yi na yara k'anana. Wani b'angaren kuma wasu iyalai ne suke ta faman d'aukar hoto.

  Tayi murmushi sannan ta d'anyi magana da zuciyarta inda take cewa " _Duniya kenan. Wasu na murna, wasu kuwa yanzu haka suna cike da bak'in ciki_."
  
  Can ta nemi wani d'an dutse ta zauna akai inda take kallon tafkin da aka tanadar don nishad'antar da jama'a a wajen. Ta d'auki lokaci tana kallon inda ruwa yake faman malalowa a cikin wannan tafki gwanin ban sha'awa. A tak'aice dai anyi tafkin kamar wani _water falls_ na gaske.

    Can sai ta hango wani matashi kyakkyawan gaske yana zaune a gefe guda rik'e da _laptop computer_ akan cinyarsa yana faman dannawa.

Ta d'auki lokaci tana kallon wannan matashin wanda a cikin d'an k'ank'anin lokaci taji ya matuk'ar birgeta. Nan take ta yanke shawarar zuwa tayi masa magana. Ta tashi ta nufi inda yake zaune. Tana isa tayi masa sallama. Ga mamakinta, sai taji yayi shiru bai amsa mata ba. Ta sake yi Masa sallama amma taji shiru. Can sai ta d'an tooareshi sai taga ya firgita ya ce "Lafiya?"

   Ta yi murmushi ta ce "Ina ta faman yi maka sallama amma kuma baka amsa min ba, shiyasa na d'an tokareka. _I'm sorry for that_."

Saurayin yayi murmushi ya ce " _It's okey_. Ba komai." Ta kalleshi na d'an wani lokaci inda taga ya maida hankalinsa ga _Computer_ d'insa. Nan sai ta zauna kusa da shi ta ce " _Browsing_ kake yi?"

Ya ce "Eh." Ba tare da ya d'aga ido ya kalleta ba.
Ta sake murmusawa ta ce " _I can see that you are busy_, _well_ bari in k'yaleka ka ci gaba da abin da kake yi."

Saurayin ya yi murmushi ya ce "A'a yaya zaki tafi kuma? Kawai _chatting_ nake yi da _friends_ d'ina na _facebook_, amma in kina da wani muhimmin zance ai sai inyi _logging out_ in saurareki...."

Ya juyo ya kalli fuskarta yana mai yi mata murmushi mai satar imani....

   Tana ganin wannan murmushin nasa sai ta ji tsikar jikinta ya tashi. Lallai wannan gayen da kwarjini yake kallo d'aya kawai da yayi Mata ya d'auke imaninta? To meye sirrinsa? Ya Zama wajibi ta binciko sirrin wannan kwarjini nasa.
    Ya kalleta har cikin ido inda yayi mata wani irin murmushi ya ce "Sunana Muhammad, amma ana kirana da Amman."
  Ta yi kamar zata fad'a Masa
Gaskiyar sunanta, sai wata zuciyar ta ce ta b'oye masa asalinta tukunna. Don haka sai ta yi murmushi ta ce "Nabila, sunana."
  Ya yi murmushi ya ce " _Wow Nabeelah, what a nice name_."
Yadda ya kira Nabeelah ya k'ara sata cikin wani irin hali na rud'ani. Duk sai taji jikinta ya mace tana son ta kwanta a jikinsa, amma kuma sai ta d'aure ta ce "Well, Amman, _what are you doing for a living_?"
    Ya ce " _I'am a corper_. Bautar k'asa nake yi a nan Abuja."
Ta ce " _Wow_! Bautar k'asa? Lallai ya yi kyau. A ina kake _serving_ d'in kenan?"
"Ina nan ofishin _visafone_. Dasu nake _serb'ing_."
Ta gyad'a kai ta ce " _Thats good_. Kai d'an ina ne? Da ga wani gari kake?"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 31, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ZAWARCI MAI TSADAWhere stories live. Discover now