page 1-5

360 10 0
                                    

HAWAYEN_ANISAH
Written by
seemaluv
Page (1_5)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
ANISAH yarinyace kyakkyawa wacce kowane da namiji ya jinjinawa kyanta, bugu da kari har mata baso sukeyi su hada kai da ANISAH ba. ANISAH ta tashi ne cikin gata cikin kudi, kasancewar ta yar babban gida. Mahaifin ANISAH Alhj_Murtala_Bature babban mutum ne a garin gombe' Asalinsu yan Maiduguri ne zama yakawo su Gombe, Mahaifiyar ANISAH Hajia Suhailat ta dade da rasuwa tun wajen haihuwar ANISAH Allah yayi mata cikawa. Hakan yasa Alhaji Murtala daukar alwashin ba zai sakeyin wani aure ba shi zai kula da little ANISAN shi, yan aiki babu wacce bai kawo ba saboda kula da ANISAH kasancewar shi yana tafiya office bashida enough time.
A yanzu haka dai ANISA tanada shekaru goma Sha bakwai(17) kuma tana a final year a makaranta her hobby is to become a Nursekuma Alhamdulillah mafarkinta ya kusa kasan cewa gaskiya tareda gudun mawar da mahaifinta yake bata.
Kwance take kan gadonta faffada tana bacci jitayi anai mata waiwayi a kafanta, cikin yanayi na bacci ta bude idonta a hankali Nanny Marwa tagani zaune a bakin gado ta zuro mata ido,
"Haba Nanny ina cikin bacci na kinzo kin tasheni miye haka. Cikin shagwaba ANISA ta karashe maganar ta,
"To ke inbanda abunki makarantar fa, kuma inajin alarm dinki yanata kara tun 6:30 amma kika ki tashi.
Ko kafin Nanny Marwa ta karashe maganar har ANISAH taja blanket ta koma bacci. Mamakine yacika Nanny Marwa,
"Ohhh baccin kika koma ko to bari naje na fadawa Daddynki aibai tafi office ba.
Da sauri ANISAH ta riko hannunta," No Nanny karki fada mishi zai iyayin fushi, kuma maganar school na riga na makara koda naje baza'a barni in shiga ba.Tabe baki Nanny Marwa tayi,"baki zauzau kamar radio naji shikenan tunda bakiyi niyya ba.
Tashi tayi zata bar mata dakin kamar ance ta juyo sai ganin ANISAH tayi ta rufe ido sai gwalo takeyi."Au sannu ANISAH,
Kunya ce ta kamata yasa tayi saurin rufe fuskarta da blanket, "Sorry Nanny am just having fun.
Cigaba tayi da baccinta ita kuma Nanny Marwa tafiyarta tayi ta cigaba da aikin dake gabanta.
Bacci sosai ANISAH takeyi saboda ta dade rabonda ta samu isasshen barci, ANISAH jitayi ana shafa saman gashin kanta a hankali' gyara kwanciya tayi saboda tasan babu maiyi mata hakan sai Daddynta, " Daddy baka tafi office ba.
"Yes my little ANISAH ban tafi ba saina ganki tukunna,
"Ohh Daddy nace maka banason wannan little din da kake cemin.
Murmushi yayi," haka nan zaki hakura da sunan saboda dashina saba    "Alright shikenan na hakura ka tafi office haka nan.
Kiss yayi mata a goshi sannan ya fita.
Tashi ANISAH tayi ta shiga bathroom don yin wanka minti biyar tayi sannan ta fito, gaban madubi ta wuce don gyara jikinta. Kwalliya tayi mai kyau sannan ta sanya kaya, tayi kyau sosai wayarta ta hango a site drawer dinta ta dauka ta kira kawarta KAUSAR, " hello KAUSAR ki fito da motarki kizo gidanmu mutafi yawo.
"ANISAH kamar kinsan iqabunda yake raina kenan, am own my way.
Kashe wayar ANISAH tayi sannan ta kama hanyar zuwa parlor don ta yiwa Nanny Marwa magana.
ANISAH!! TO BE CONTINUE...
Dedicated__to__readers
Written__by__seemaluv

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 03, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HAWAYEN ANISAH Complete Where stories live. Discover now