MAZAN KO MATAN
Na Shuraih Usman
Gajeran labari
Part 1
Tangamemen Gida ne iRin na zamani
Wanda ya kawatu ainun, domin kuwa a gaba dayan fadin unguwar gidanne gida na farko da a ka sana'anta da Bene
Gidan wani dan majalisa ne mai ci
.
Ina tsaye a bakin gate din gidan hannuna na dama rike da makulli ,yayin da hannun haguna yake boye cikin Aljihu,
Lokaci lokaci nakan yi wasa da makullin hannuna ta hanyar jujjuyasa
.
Wani yaro na gani ya fito daga cikin gidan zai karisa bakin titi, da guduna na tsaida shi ta hanyar kwala mai kira , yaron ya tsaya yana dubana tamkar wanda yaga wani Aljani ,
"Dun Allah yayarka Safiya tana gida kuwa"
Na tabayi yaron
"Eh tana gida" yabani amsa
"Dun Allah kai mani wata Alfarma man"
"Ina jin ka"
"So nake ka kiramin ita"
"Hmm " kawai ya fada sannan ya juya ya nufi cikin gidan
.
Duk da dai nasan abunda zai biyo baya hakan bai sa naji ko darr a zuciyata ba,
Bayan dan gajeran lokaci sai ga yaron ya fito
Haryanzu irin kallon dayai mani waccan karon itane dauke a idanunsa ,
Bayau na saba zuwa zance wajen safiyya ba don kuwa nakai wajen wata biyu, ina zuwa wajenta dai dai da rana daya ban taba fashi ba
.
Duk abun da nake yi komenene, koya wannan abu yakai ga muhimmanci muddin karfe takwas din Dare yayi, toh take zan saki abunnan na nufi hanyar gidan su safiyya
,
Wani tarin abun takaici kuwa shine Tunda nake zuwa wajen safiyya dai dai da rana daya bata taba yimin kallon mutunci ba,
Ko tafito ma sai de ta gaggasa mani magana tai tafiyarta, wani sa'in ma a gabana samarita masu hannu da shuni suke zuwa sui awon gaba da ita, cikin dankareren motoncinsu
,
Bazan taba mantawa ba akwai wata rana da na zo , naci sa'a ta fito, ranan ina sanye da kayan aikinane na bakanike. Ko tsayawa canzaasu ban ba, kuru kuru safiyya ta fadamani wai wari nake
Muna tsaye da ita a wajen sai faman bata baki nake ina furta mata lufuzan soyayya masu sanya zuciya tai taushi,
Wata dankareriyar motace kirar range rover ta faka wani mutum sanye da manyan kaya ya fito daga cikin motan.
Koda safiyya ta kyallara ido taga waNnan mutumin sai ta nufeshi tana mai murmushi
,
Ni kuwa nai tsayuwata a kofan gidan cikin zaman jira lokacin data zo shigan gida
.
Sam bana damuwa da irin tarin wulakancin da safiyya take nuna mani, duk da bata fito fili tace bata sona ba,
Nasan abu daya ne ya shiga tsakanina da ita
Kuma shine ya darsa rashin kaunata a zuciyar safiyya
Wannan abu kuwa shine NAIRA
,
Bakaniken mota ne ni,cikin kanikawan ma yaron aiki nake,
Aduk lokacin dana dan samu kudi sai na tafi kasuwa na sayomata yan man shafawa, da sabulai na iya karfina na kawo mata, amma ko godiya bata taba min ba sai de ta amshe tai su ta kara gaba wajen masu zuwa da dankara dan karan motoci
.
Wannan abu ya dade yana cimin tuwo a kwarya
Su kansu Abokaina ma tsiya suke min sai kaji suna kirana da dan wahala ,
,
Wannan yasa na yanke shawarar canja salon takuna tunda na fito a gaskiyana abu yaki aiki toh bazan jarraba dayan ko zaiyi aiki
.
Wannan nema yasa naje na samu wani dan unguwanmu ana kiransa Abba Yelo, na naimi daya taimakamin da Aron Motarsa na Dare daya kacal,
Daga nan na garzaya wajen Abokina MJ na nemi ARon kayan kanti sababbi a wajensa
,
Nai wanka na feshe jikina da turaren Daki na ci kwalliya sa'annan na dau makullin motar dana ara nai ficewata daga gida,
Koda na fito kofan gida mutane da dama basu gane ni ba, don kuwa sun saba gani na cikin tsummokaran Over size dina
To yau gani sai kace wani hamshakin mai dala ne
.
Na shiga cikin motan nai hanyar Gangaren Aboki
Fakawa nayi a kofan gidan su DANGADO na nemi daya bani aron wayarsa infinix finger print, da kyar da sidin goshi ya bani, yayin daya cikani da gargadi
*****
"Wai tana zuwa" yaron ya fada
Cikin isa na zura hannu cikin Aljihuna na dauko naira hamsin na ba ma yaron, sosai yayi godiya sannan ya kara wuta
,
Bayan dan wani lokaci sai kofan gidan ya bude safiyya ce ta fito tana sanye da riga da siket wayanda sukai matukar yi mata kyau, hasken fuskarta wanda akullum karuwa yake,
Tun daga nesa naga tana mini kallon daga ina
Wannan yatabbatar mani da cewa bata gane ni ba
"Assalam" tai sallama
Na amsa sallamar cikin kausasa murya yanda na amsa sallaman zai tuna maka da marigayi IBRO Allah ya jikansa
,
"Malam waye kai sannan daga ina kake" ta jero min wayannan tambayoyi bayan data jingina a jikin motan Aro na
Nai murmushi sannan na Cire bakin tabarau din daya ke kan fuskata
Cikin dan razana ta washe baki "shuraih!"
Na gyada mata kai
Munyi hira sosai yayin da yawancin hiranma safiyya ne ke zancenta , don ni hankalina yana cikin wayar hannuna wanda tun da muka fara hira na fiDdo,
Ni kaina nayi mamakin yadda safiyya ta zage muna hira yau tamkar ba itace safiyyan da ke cemin ina Wari ba,
Na tattakure na shiga shirga mata karya ba kakkautawa
Don kuwa ce mata nai ai Dangote kanin babana ne Uwa daya Uba daya
Sun rabu ne tun suna yara kananu
Koda ta nemi sanin abunda ya rabasu sai na sake shirga mata wani karyan inda nace mata
Ai tun lokacinnan babana suna zaune a kano wata rana sun fita yawo shi da dangote shine barayin mutane suka sata shi, tun daga ranan basu sake haduwa sai jiya, da dangote yazo wucewa ta nan garin sai Allah ya hadasu
,
Ta sake tambayana yadda akayi suka shaida Juna
Nai murmushi nace mata ai naka nakane babu ta yadda zaka mance da dan uwanka, hatsari dangote yayi a hanyan KARAN SHANU shi kuwa mahaifina yai kokari ya taimakeshi ya futo da shi daga cikin motan to ta haka ne har dangote yaga wata sarka a wuyan mahaifina , wannan sarka itace shedan gidanmu don nima ina da ita,"
Safiyya ta kalleni cikin mamakin zancena
,
Na basar da kallon datai mani
Ta budi baki da niyyar sake jefomin wani tambayan nai sauri na katseta da fadin
"Yanzu haka ma dangoten yana nan a gidanmu, shin kina bukatar ganin sa ne?"
Nai kasake ina shirin jin amsar daza ta bani, ni kaina na san nayi gangancin fadin wannan zance,
,
"Ai kuwa zanso na gansa ,kash sai de yanzu babana yana gida amma gobe kam dolenka ka kaini kodan ma muyi hoto"
Tafadi cikin zumudi
murmushi nayi mai nuna cewar na tsira daga wannan takin,
,
Munyi hira sosai daga nan na sallemeta inda na zaro last cash dina Dubu daya na bata, ita kanta dubu dayan sai da nayi kwanaki bakwai ina tarata , na bude motan aro na na kara gaba,
Zuciyata fal da farin ciki domin kuwa ji nake tamkar nafi kowa a duniya
,
Ina kan hanyata ta komawa gida sai na Tuna da abun da ya kusan sanyani hatsari,
Hankalina ya tashi, idanuwana suka zazzaro
Gabana yakama faduwa
"Wayan DANGADO"
A fili na fada yayin danake lalube aljihuna
Nai saurin faka motan a gefen titi
Babu inda ban bin cika a cikin motar ba amma ban ga wayan ba
Na tuna irin tarin gargadi da kashedin da runga kwarara mani kafin ya bani wayan
.
Fans dafatan kuna biye da Alkalamin 99%
YOU ARE READING
MAZAN KO MATAN
Short StoryMAZAN KO MATAN Na Shuraih Usman Gajeran labari . soyayya takan ginu akan turba dabam dabam, Masoya da dama suna gina soyayyarsu akan tafarkin gaskiya ce, yayinda kadan daga cikinsu masu zalama da son abun duniya ke gina ta su bisa tafarkin Karya,yau...