NI DA ABOKIN BABANA

3.8K 84 17
                                    


NI DA ABOKIN BABA NA....!!*
              ©JeedderhLawals

                      01

A nutse nayi sallama dakin Daddy na, dakin a shimfide yake da tattausan carpet sakar hannu kirar kasar India, ruwan hanta ne kamar yadda jeren kayan dakin suke.  A hankali na zauna a kusa dashi ina kallon yadda yake sarrafa laptop dake hannunshi cikin kwarewa, ganin bashi da niyar dawo da hankalinshi gare ni, dama dai nasan halin baba in dai yana aiki baya maida hankalinshi ga kowa har ni er gaban goshin shi kuwa har sai ya gama. Remote na dauka na canza channel daga sports zuwa Zee World. Na ma manta ranar suna shirin da nake nacin kallo, Love Look Like What You Made Me Do.  Dan Murmushi nayi nace woah, ni na ma manta da shirin nan. Daddy ya dan yi glancing din wajen da nake zaune ya kafin ya maida hankalinshi ga laptop dinshi. A takaice har aka gama shirin suka fara tallace-tallace Daddy bai gama abinda yake yi ba. Ba a jima ba naji na fara hamma, remote na dauka na mayar mishi da tashar da yake kallo na mike, daidai lokacin daya rufe laptop din nashi ya kalle ni cike da kulawa. "Uwata, ya aka yi ne?" sunan mahaifiyar shi gare ni shi yasa yake kirana da Uwata, su Mommy kam Ummi suke ce min. Baki na turo cikin dan jin haushi nace "ni barci nake ji..... Sai da safe!" er dariya yayi ya kamo hannuna ya rike ya janyo ni na koma kusa dashi na zauna ina kara tura baki na. Kumatu na ya dan ja, "ohhh m soooo sorry princess, na tsaida ki koh? Akwai muhimman bayanai dana tura ne yanzun shi yasa, ayi hakuri. Gobe zamu je mu sha ice cream ni da princess dina, are we good now?" kaina na kawar daga kallonshi, yasa hannu ya juyo da fuskata zuwa gare shi, "hey, m trying to pay for what I did, aren't we good yet?" bansan lokacin dana yi er dariya ba ganin yadda yayi da fuskarshi, Ina son babana fiye da tunaninku saboda yana sona sosai, kaunar da yake min ko mahaifiyar data haife ni bata nuna min kwatankwacinta. Ban sani ba ko don hakan yana da nasaba da cewa ni Kadai ce diyar su??. Kai na girgiza ina dan murmushi, "naji na hakura, but we will also go for shopping, agree??" ya gyada kai, yes. Tashi tsaye nayi nace to sai da safe Daddy. Murmushi yayi, ki tashi lafiya Uwata.

A main parlour naci karo da Mummy, da alamun turaka zata tafi ganin yadda taci kwalliya, ba wai ta fuska ba, ta jiki sai tashin kamshi take. Murmushi nayi naje na rungumeta, "Mommy sai da safe!" bayana ta dan shafa, "OK, sweet dreams baby" ta sake ni ni na wuce dakina ita kuma ta tsaya tana kashe wutar falon.

        Ina shiga dakina wuta na kunna na shiga zare kayan jikina daya bayan daya, towel na zara na daura a jikina na fada toilet din dake manne a dakina. Cikin bathtub na shiga na zauna bayan na tara ruwa mai dumi, ban jima a ciki ba na fito. A cikin toilet nayi shafe shafen da zanyi, na fito. Kayan barci na saka marasa nauyi, kayan dana bari a tsakar daki na tsince na watsa cikin kwandon da nake tara kayan datti don nasan idan na bari Mommy ta gani gobe sai raina ya baci. Mommy mace ce mai tsabta da bata jurar kazanta ko ta anini. Kan katoton gadona nayi tsalle na haye kamar wata karamar yarinya, wayana na cire daga jikin socket na kunna data, social media na shiga na fara chat da friends dina. Ban samu barci ya dauke ni ba sai wajen karfe goma sha biyu na dare. Ban jima da fara barci ba naji numfashi ya fara min wahalar shaka, rigar jikina na fara adjusting daga jikina, ji nake kamar ita ta shake min wuya na kasa numfashi. Daga karshe tashi nayi gabadaya na cire rigar na jefar kasan gado na koma na kwanta. Dama don dole nake saka riga idan zan kwanta saboda fadan Mommy, ban cika kwanciya da riga a jikina ba saboda a yawancin lokuta na kan ji kamar rigar na shake ni ne, ban sani ba hakan sabo ne ko kuwa hali ne ko cuta? Ban sani ba, n I don't give a damn akan lallai sai na sani.

                    *☆☆☆☆☆*

Kiran sallar asubahi a cikin kunnena da yake masallacin unguwar mu a jikin gidanmu yake. Na saki gurnani a hankali saboda barcin daya cika min ido, da kyar na samu na iya bude idanuna suna komawa suna rufewa, na dauki kusan mintuna biyar kafin na iya tashi zaune, gashin kaina daya tattare ya barbaje min a fuska na tattara na maida shi baya, a hankali iska ya shiga kada sassan jikina hakan ya ankarar dani yanayin da nake ciki na babu riga, da sauri na dira daga kan gadon na dauki rigata na saka. Daidai lokacin Mommy ta leko, ganina a tsaye yasa ta maida kofar ta rufe ba tare da ta min magana ba. Sighing na danyi softly cike da jindadin bata kama ni ba. Bandaki na fada direct na dauro alwala, nazo nayi sallah na zauna Ina lazumi har sai da gari ya danyi haske, tashi nayi na fita daga dakina. Sai dana je na gaida Daddy sannan na shiga kicin inda na samu Mommy da Mama Sauda wadda take taya ta en aikace-aikace suna ta kokarin hada break fast, a nutse na gaida su sannan nima naje na kama musu.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 19, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NI DA ABOKIN BABANA COMPLETE BOOK 1Where stories live. Discover now