EPISODE 1

4.1K 139 6
                                    

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY* (Firdausi S Ahmad)
Wattpad  *@jannahjay8*

© 2019
بسم الله الرحمن الرحيم

*Asssalamu alaikum, wannan littafi mai suna asama k'agaggen labarine wanda ya k'unshi illar zazzafan kishi dayakan jefa wasu ga zargin abokan zamansu wanda ak'arshe baya haifar da komi sai rashin zaman lafiya da nadama.Duk da kasancewar manzon (S. A. W) yace"duk wanda baya kishin iyalinsa bazai ji k'amshin aljannaba" Hakan bai bamu damar mudinga zafafa al'amuraba, wannan abun yazama ruwan dare awannan zamani daga bangaren kowane jinsi ma'ana maza da mata, ina fatan da d'an karamin fad'akarwar da zanyi wasu su amfana.Don Allah wanda yaga kuskure ko shawara k'ofa abud'e take asanarmin, pls adinga comment. Nagode*😘

01

*KHAIR* ce tsaye suna magana itada *Ibrahim* wanda ya kasance immediate elder brother na friend d'inta *khadija mu'az* suna tsaka da magana basu san hawa ba basu san saukaba kawai *Ibrahim* yaji an rufeshi da naushi, sai da aka kaimasa naushi karo na uku gaba d'aya suka ji muryar *YA ADAM* yana jefa mata tambaya lokaci d'aya yana k'ara kaimasa duka yace " uban waye wannan? " Tuni hantar cikin *KHAIR* ta kad'a bata iya bashi amsaba sai hawaye daya fara zubowa a idonta, tana d'an karkarwa take bashi hak'uri akan yasaki wuyar rigar *Ibrahim* don tuni ya cakumeshi har idonsa yayi ja duk da ta alak'anta hakan ne da b'acin rai

Yanzu ya sakeshi sai dai bai daina jifansu da wani irin kalloba, take *Ibrahim* ya wuce batare da ya tankawa *Adam* ba wanda darajartane ya hanashi amma batun bacin rai ba'a magana don yaji ba dad'i

Ganin haka yasa *Khair* binshi tana "don Allah *ya Ib* kayi hak'uri, nasan..  " gani tayi ya k'ara hanzari tada motarshi

Hak'urin da *Khair* ta bawa *Ibrahim* shiya k'ara tunzura *Adam* take ya fizgota ya d'ora mata mari, dafe kuncinta tayi ta fashe da kuka kuma adaidai lokacinne *Hajiya Hassu* ta fito daga gida zata je unguwa, akan idonta akayi marin watsamasa kallo tayi na warning

Take jikin *Adam* yayi sanyi don yasan tsaf zata sab'a masa, nuni tayi masu da su biyota cikin gida, basuyi k'asa agwuiwaba suka bi bayanta, itakam *Khair* har lokacin tana hawaye suna zubowa tana sharesu da yatsunta

   Tsugunne suke gaba d'ayansu kowa ransa ab'ace, baya ita *Khair* da bama marinne ya dametaba illa cin mutumcin *Ibrahim* da yayi, anasa bangaren kuwa kishi ke nuk'urk'usarshi ya za'ayi ta tsaya tana b'arewa wani baki suna hira har tana dariya. Cikin dakakkiyar murya *Hajiya Hassu* ta fara magana " *Adam* wannan shirmen naka ya fara  yawa koda baku fad'amin meya faruba nasan bai wuce kaganta da wani ba, ba damar kaganta na uzuri da wasu sai ka tsiri tada mata hankali, gaskiya yakamata ayiwa tufkar nan hanci gara azo ayi auren nan kowa ya huta, ke kanki kya sarara *Khairi*, idan yaga yasameki kinzama tasa ai ya san ba'a auran maza biyu daga ranar sai ka kwantar da hankalinka, kasan cewa takace kai kad'ai" jin k'iran sallar da tayine yasa tace "tashi kaje masallaci kuma kadinga yiwa kanka Addu'ar sauk'i" mik'ewa yayi koda yazo fita sai da yaso ya had'a ido da *Khair* ita kuwa tuni ta d'auke kanta don yau kam *Ya Adam* bak'aramin b'atamata rai yayiba, ji take inama *Ya Habib* ta zab'a da tuni ta huta da masifar *KISHINSA*

Bayan fitarshi *Hajiya Hassu* ta umarceta da tayi sallah, ta tashi ta shiga toilet dan d'aura alwala,  ita kuma *Hajiya Hassu* (Mama) ta kira *Safiyya* ta kawowa *Khair* abinci

Bayan *Safiyya* ta kawo mata Abinci, kasa ci tayi don har lokacin bak'aramin damuwa ta shigaba, sau tari takan shiga tunani akan yanayin rayuwar da zatayi da *Ya Adam* bai iya controlling *Kishinsa* ko kad'an, sauk'i d'aya da takeji shine mutane dayawa sukance mata da zarar yaga tazama mallakinsa zai daina damun kansa.Ganin *Khair* tana ta juya spoon batare da tana cin abincin ba yasa *Safiyya* ta sauko daga kan couch d'in da take ta koma kusa da *Khair* ta dafa kafad'arta tace "Sis har yanzu damuwa kike akan abunda *Ya Adam* yayi? Hmnn baikamata ace kin ajiyeshi arankiba har yakai da ya hanaki sukuni, karki manta bayau ya faraba idan da sabo yaci ace yanzu kin saba" tabbas *Khair* tasan da hakan inda sabo yaci ace tayi amman dizgin yayi yawa, tamkar an zugo hawayen da suke idontane su zubo, bata damu da ta shareba ta kalli *Safiyya* tace "Bazaki gane yanda abun nan ya bani haushiba ace wai d'an uwan *Khadija* akayiwa haka, inaga yaci ace *Ya Adam* yadaina irin haka har marina yayi fa" lallashinta *Safiyya* tacigaba dayi, itakam *Khair* ji tayi batason cigaba da maida zancen, jin shigowarshi cikin gidan yasa ta mik'e ta ce "Bari na k'arasa gida inason k'arasa wani Assignment" kallonta tayi ta jijjiga kai tace " kedai kawai kice kinji ya dawo bari ki tafi saboda baki huceba" basarwa *Khair* tayi tace "Nidai in Mama tafito kice mata sai da safe na tafi" daidai lokacin *Adam* ya bud'e curtain d'in d'akin zai shigo kuma tsaf yaji sallamar da take akunnanshi, hakan ya tabbatar masa bata huce ba, bata damu ba da ganin sa atsaye yana kallonta saima sunkuyar da kanta da tayi don bata son kallon fuskarshi sosai idonsa zai mata illa wajan tursasata ga hucewa, cikin hanzari ta nufi k'ofar ta takura jikinta dan ta wuceshi, shikuma yana sane yak'i matsawa daga wajan, tagane nufinsa amman saita d'aure fuskarta tana fita daga d'akin yace "Hmm dagaske fushin kike da har yakai ki fara gaba dani" cikin hanzari ta wuce don karma tak'ara jin wani furuci daga gareshi, bin bayanta yayi da kallo tare da sakin ajiyar zuciya.

*khair* na shiga gida ta hangi mahaifiyarta na aiki a kitchen, batason tasan me yafaru tayi sauri ta shiga cikin falo da sand'a ta shige d'akinta ta shiga wanka. Ita kuwa *Hajiya Aisha* tasan daga inda *Khair* ta dawo shiyasa bata damu da taganta ba, sai dai taga tana sand'a tanason sanin dalilin hakan

  ....... *Khair* na fitowa daga wanka tasa kayan baccinta red gowan ne har k'asa cotton ta shafa perfumes tare da zira hula net fara k'al, ta janyo wayarta domin kiran *Ibrahim* saida tayi mashi 2 miss calls sannan ta ajiye wayar tare da rafka tagumi tashiga uku yau *Ya Adam* yanaso ya b'ata masu zumuncinsu da su *Khadija*  tajima tana tunane tunane tunowa tayi da randa ya Adam yaje har islamiyyar da take alokacin ya tsinkawa malaminsu mari akanta, da aka tambayeshi sai cewa yayi ai yaga kullum sai ya biyo bayanta idan aka tashi daga makaranta k'arshe saida aka cireta daga islamiyyar, yasa aka dinga gulmarta amakarantar kuma daga ranar ko gaida malamin tayi sai ya d'auke kansa, sai daga  baya ya huce dayaji labarin halin *Adam* donshi da ya d'auka sharrin mata tayi mashi tasa akayi masa hakan

Sai da akayi isha'i  sannan *Adam*  ya dinga kiran *Khair*   ita kuma tak'i dauka, duk da yunwar dayake ji yakasa cin abinci sai jan tsaki yake *Khair* matsala gareta bata ganin son dayake matane yasa yake irin haka, dafe kansa yayi yaja tsuka mata matsala garesu wallahi ya furta afili

  *Khair* kam sai 9 tafito tasan lokacin Ummi tana part d'in mahaifinta, zuwa tayi kitchen ta duba taga akwai ragowar fura ta d'auko ta nufi d'akinta taci sa'a bakowa ayaran gidansu balle sujata da magana. Tana shiga d'akin taga miss calls daga *Ya Ib* bayan na mutumin nata ajiyar zuciya tayi don taji dad'in haka don haka batayi k'asa agwuiwaba tayi call back,  bayan yad'auka ta bashi hak'uri yace karta damu ko k'iran da tamishi bai kusane yasa bai d'aukaba bawai don fushiba ai ya dad'e da sanin *KISHIN* *Adam*
   Bangaren *Adam* baiyi zuciyaba ya cigaba da k'iranta sai yaji busy lokacin tana waya da *Ibrahim* sai yaji wani irin k'unci ya kamashi yaji kamar ya tashi yayi hauka... Kwana yayi yana juye juye sai b'arawon baccine ya d'aukeshi

BY JANNAH JAY

NAMIJIN KISHIWhere stories live. Discover now