🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*
© 201924
Sai da tagama surutan rok'onta sannan yace mata "A'a ba nayi fushi bane kawai ki kwanta Allah ya sawak'e" saida taga yana murmushi sannan hankalinta ya kwanta
Cikin rashin kuzari take had'a breakfast d'in, duk wanda yasanta ya kalleta zaisan tana cikin damuwa, rashin zaman lafiyarsu da Adam baya mata dad'i ga yanayin laulayi. Yana zaune yana cin abinci sai sak'e-sak'e yake aransa, shifa tunda yaji hankalinsa bai kwanta da mutane biyunnan ba baya k'aunar yaga taje asibitin nan, dan baya son iyayensa suji maganar da tuni yasa ta ajiye aikin, jan tsaki yayi ta d'ago ta kalleshi ko tantama batayi tsakin yana da nasaba da ita, haka kurum taji abu yazo ya tsaya mata arai sai hawaye ya b'alle mata kamar wasa sai gashi ta kasa shanyesu sai sheshheka take, a tsanake yake k'are mata kallo tabbas ta fad'a ta rame "Babyluv meye yake damunki kike kuka kuma?" cije lip d'inta tayi ta jijjiga kanta alaman bakomai "Ya zakice haka? Babu komai kawai zakike kuka kinga ki fad'amin ko wani abu ke damunki" bazata iya cewa komiba sai k'ok'arin share hawayenta da takeyi, bata tab'a manta nasihun da iyayenta suka mata akan dannewa da rik'e sirrin aure, kuma gashi tanayi domin har yau bawanda yasan tana samun sab'ani dashi, shiyasa abun ke cinta arai bata tab'a fada, kuma iya bin diddigi da sa'idonka bazaka gane ga yanayin da take cikiba, lallashinta yazo yakeyi yana cewa "Tayi hak'uri haka ciki yagada amma ta samu ta kwanta ta huta, in yaso anjima zai kaita gida" taji haushin maganar da yayi, ya za'ai yace wani ciki ai yasan kalar matsalar da suke ciki, amma bakomai taji dad'i dayace zasu gida ko bakomai zata wataya acan, dama kwana biyu basu jeba...
Matane ak'alla zasu kai shida acikin k'aramin tsakar gidan, kowacce da yaranta inka d'auke Jamila da shafa'atu, kasancewar week-end ne sunzo kitso wasu kuma sun kawo yaransu amusu, hira suke kaman yanda gidan kitso ya gada, d'aya acikin matan ta dubi fatsima mai kitso tace "kinji labarin abunda ya samu shafa'atu ai ko" tallafar kumatu tagefensu tayi itace shafan, kallon ta Fatsima tace " Kwarai kuwa Barira nasani wai tsabar wulak'anci Nasiru kishiya zai mata akan haihuwa, maza sai abarsu" K'ululu cikin Jamila ya kada ta bi Shafa'atun da kallon tausayi, ita wallahi idan taji za'ayiwa wata kishiya har cikin ranta takejin abun Barira ta kalli Shafa'atu tace " Wallahi yar uwa ina ganin k'ok'arinki, da kika zuba masa ido yake yanda yakeso" Cikin mamaki Shafa'atu tace " To ya kike so nayi, ai tunda addini ya bashi dama dole ne na hak'ura don namiji yayi niyyar k'ara aure haukan mace baya hanashi saima ki cikawa kwabarki ruwa karshe ya baki Visa" heyy matan gefensu suka saka shewa nan fa kowacce ta shiga cika baki akan abunda zataiwa mijinta in yace zai k'ara aure, hauka kadai itama Jamila duk da bata fiya surutu a gidan kitsoba sannan bata saba dasu Shafa ba tace " Tab amma yar uwa gaskiya na jinjinawa k'okarinki, wallahi kishiya ko wani za'ayiwa haushi nakeji balleni, amma dubeki kalau kaman abun bai dameki ba" murmushi yak'e Shafa tayi tace " To ya na iya da kaddarata sai dai fatan kawai ta zamo tagari" nan Barira ta karbe zancen tace " A kishiya ina ake tagari, matar da zata shiga da niyyar rabaki da farin cikin ki, kinga ko wannan 'yar fata na nake mata Allah kar ya nuna mata kishiya arayuwarta" ta kama diyarta wadda bata k'arasa shekara hud'u ba, matan wajan suka saka dariya suna lallai Maman Huda ashirye kike, ta kalli Huda ta shafa gashinta tace" Ko kina son kishiya?" Yarinya kuwa da batasan kan komiba ta kwantar da kanta jikin uwar tace " A'a banacon ta Mama" nan suka fasa shewa yiii yarinya 'yar gari, dole Jamila ta dara ita da Fatsima don abun yabasu dariya, rabin hirar akan kishiyane da irin juyawa mata baya da wasu mazan kan yi in sunyi amarya, da irin reasons da kansa maza k'ara Aure bayama rashin haihuwa, daga masu cewa uwar miji kan zuga ayi ko abokai, iyakar tashin hankali Jamila ta shiga, ana gama mata kitso kuwa da tashiga gida fad'awa tayi kan kujera ta rushe da ihu " Allah mai nai maka ka hana ni haihuwa? Ya Allah kaji k'aina kabani haihuwar nan" haka tagama sumbatun haihuwarta kafin ta mik'e ta d'ora girki, taso ta makara Allah yasota Ahmad yaje Gumel d'aurin Aure
YOU ARE READING
NAMIJIN KISHI
רומנטיקהKhair gara nak'ara maimaita maki bake ba Aikin nan ke bari na tak'aita maki wallahi wallahi ban yarda dake da Dr Umar ba.... Cikin Kuka tace " Zargina kake? "Hawaye yana zuba a idonta... "Wallahi Ahmad sai kayi nadamar abunda kayi yau, zan tabbat...