🕳🕳🕳🕳🕳
*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳
*Maman Abd Shakur*
8⃣ - 9⃣
Sallama yayi Abba yabashi izinin shigowa hakan yasa ya shiga yana shan malt din dake hanunshi ya maida kofar yarufe yakaraso nan kusa da Abba a kasan carpet ya zauna yace "sannu da hutawa Abba" alamu Abba yamai dakai na yauwa dan ranshi abace yake har yanzu Mum bata sake kiraba, ajiye malt din hanunshi gefe yayi yace "Abba I've been calling Mum yafi sau uku she's not answering, gaskiya Abba tadawo this girl need her mana, she looks lonely gatanan duk kalan tausayi tausayi, yanda zatai feeling taji tamanta da matsalolinta a jikin Mum bahaka zataji a wurin muba, please Abba Mum should come back kace tadawo." "and kana tunanin bance mata tadawon bane?" Abba yay maganan yana raising ma Ya Muhsin voice ranshi abace, yanda Ya Muhsin ya tsaya kallonshi da mamaki ne dan da wuya kaga Abba yay fushi hakan yasa ya dafa kanshi nayan sakannni kafin ya shafa fuskarshi ya sassauta muryanshi yace "Muhsin lemme advice akan wani abu, inhar lokacin auren ka yatashi karka sake ka yarda da any conditions da wacce zaka aura zata kawoma na zata dinga tafiye tafiye tana business, Mum dinku ko hmm" sai kuma yay shiru kawai batare daya kara wata maganan ba, ganin yanda Abba is so pained ne yasa shima yaji ranshi dukya baci, haba mana Mum kullum tana wanan garin tana wanchan garin sabida Abba na sonta and he's too soft towards her saisa take abinda taga dama, maganan Abba ne ya katse mai tunani yace "kaga Son i have meeting daya kamata naje, gobe ne meeting din a japan amma dole nafasa tafiyan zamu barkune ba baba ba Mama?" girgixa mai kai Muhsin yayi yace "kayakuri Abba" "is okay, i know what to do, yaya kukayi da kaje asibitin?" yatsine fuskarshi yayi yace "bansami HOD dinsu ba, so i will be going their tommorow i need her permission ne sabida nai gaining access to their CCTV footage, dudda nasan thousands of people suna shiga da fita daga asibiti daily but i want to take my time and watch it, dan inhar Nadeera tace taga boyayyen mutum taganshi ne, inhar am able to see him that shows that she's innocent kaga koda wani abu eventually happen to d patient baza ai holding dinta responsible ba in anyway" gyadakai Abba yayi alamun gamsuwa da maganan da Ya Muhsin yayi, ahankali yace "to ubangiji Allah ya fitar da ita, ya maganar mu Son? Sabida banason takura muku saisa ka banzantar da ita ko? Wlh fa zan maka auren nan babu abinda ya shafan koma wacece saidai nahada ka da ita" lumshe ido yayi ahankali yace "my heart, soul, system and my nerves only belong to her Abba" "mekace banajinka" bude ido yayi ya kalli Abba yana murmushi yace "Abba in sha Allah very soon zan fito da mata, ka karamin lokacin kadan" gyadakai Abba yayi yace "is okay take your time amma banason ka wuce dis year kaga kana 29 yanzu at least by 30 ko yaron kirki?" maltinan shi ya dauka yasha sanan yace "yes Abbana" zama ya gyara suna kallon news din tare, ba'a wani dadeba Ya Ahmad ma yashigo suna hira kasa kasa suna labarai sai wuraren eleven na dare suka baro dakin Abba koda zasu tafi su kwanta saida suka bude kofar dakinta amma hartai bacci ta lulluba da bargo, hakan yasa suka kashe mata wutan dakin suka rufo kofan sukai part dinsu.
Da Asuba Abba ya shigo yatada ta saida ya tabbatar ta tashi sanan ya fice, saukowa tai daga kan gadon ahankali ta shiga bayi, bata wani jimaba ta fito daure da alwala, rakatanil fajiri tafara yi, sanan tai sallan asuba tana gamawa tai azkar sanan tajawo Al Qur'ani tafara karatu da qira'anta mai dadin gaske saida gari yasoma haske ta rufe Qur'anin ta ijiye ta linke dadduma ta ijiye sanan ta wuce kitchen ruwan tea tadafa takai shashin su Ya Ahmad babu ma kowa falon alamun basu dawoba hakan yasa ta wuce part dinsu tray ta dauka takai part din Abba, sanan tafito tai dakinta tattare dakin tayi sanan ta wuce ta shiga wanka bata wani dadeba tafito daure da pink towel gaban wardrobe taje ta dauko wasu gogaggun uniform dinta ta shirya tsaf, gaban mirror ta tsaya tadan shafa hoda tasaka kwalli bakaramin kyau tayiba dudda idanunta da dan ragowan kumburin jiya na kuka, addu'a tayi Allah yasa kar amata komi a practical yau, ajiye hijabin tayi akan gado ta zira silifas ta fita, kitchen taje tahada tea tai soya egg tafito dining ta zauna tana ci, Ya Muhsin ne ya shigo sanye da black suit sai kamshi yake, kallo daya yamata ya dauke kai hadiye egg din bakinta tayi tace "ina kwana Yaya" corridor yayi dan zuwa ciki ya gaida Abba batare daya kalleta ba yace "kin tashi lpy", agurguje ta shanye tea tadau komi takai kitchen sanan tafito tai corridorn itama ta shiga dakinta, black cover shoe dinta ta dauko ta saka sanan tadau hijabin tasaka shima, tadau jakarta ta goya ta rike hadadden after dress dinta a hannu tafita daga dakin sai kamshin turaren ta twilly takeyi tafice tai dakin Abba sallama tayi ta shiga Abba da Ya Muhsin ke zaune kusa dashi suna wani abu da system ta kalla tace "good morning Abba" "morning princess, zakije anya ba matsala kuwa?" yay maganan yana kallon fuskar Ya Muhsin, jingina yay da jikin kujeran yace "no taje Abba anjima i will go to the hospital anjima" gyada kai Abba yayi yace "okay to shikenan, Allah bada sa'a" Ameen tace tana murmushi yaciro dubu uku ya mikamata karba tayi tace "thank you Abbana bye, bye Ya Muhsin" batare daya dago kai daga abinda yakeyiba yace "bye" fita tayi da sauri ta wuce waje da Ya Ahmad sukaci karo kunenta ya rike ta hijabi yace "ke kin gaisheni dis morning" kaman zatai kuka tace "tona shigo side dinku lokacin baku dawo daga mosque ba, good morning ya Ahmad" "morning princess kinsan wani abu?" yay maganan yana mika mata red necktie din dake hanunshi, karba tayi ta ijiye after dress dinta akan kujera tace "saika fada" tai magana tana dage kafa dan ta sakamai necktie din dan yafita tsawo, duko da kanshi yayi hakan yasa ta hau dauramai yace "tommorow ki shirya zamuje amusement park, zaki rakani tadi wurin My Deejay, a park din zamu hadu" dan dariya tayi saikuma ta harareshi tace "wlh in nine Khadeeja bazan bari kana cemin My Deejay ba chabdi" tai maganan daidai tagama dauramai tie din, hakan yasa ya dungure mata kai yace "sunanta dai yafi naki dadi black belly" "wlh karyane ni white belly ce, kuma ni kabani kudin break" hararan ta yayi yana son ya wuce yace "sabida kina tayani zuwa banki muna aikin tareko" hanunshi tarike tai kaman zatai kuka tace "ai wlh saika bani, accountant kun cika mako, naira daya dazaku bama mutum kun gwammace kuyi tunanin yanda zaku juyata ta koma miliyan, wlh saika bani ni" tai maganan harda bubbuga kafa akasa, tsaki yayi ya ciro wallet dinshi daga aljihu yabude gayan dubu daidai sai ya zaro wata naira dari biyu sabuwa ya mika mata yace "gashi beggy beggy" turo baki tayi dake kara mata kyau tace "eh naji dai inaso" sakin shi tayi ta mika hannu zata karbi kudin ya daga hanun sama, bin hanun tayi da kallo hakan yasa tai tsalle zata karba yakara dage hannun sama sosai, buga kafa tai akasa tace "kaga kabani kudina" "kai kajimin yarinya kudinki ko kudina? Oya gashinan ai yi tsalle ki karba, ai duk beggy beggy haka ake musu" hararan hanunshi tayi tasake yin tsalle zata chapko kudin yay dage kudin yay sama sosai juyawa tayi tadau after dress dinta kaman zatai kuka tace "banaso" tai hanyar fita da sauri yariketa yana dariya sosai yace "haba emmatan Mum, oya gashi" make kafada tayi taki juyowa tace "banaso" "yakuri to ga dubu daya" da sauri ta juyo tana murmushi, dubu dayan ya ciro daga wallet ya mika mata da sauri ta fizge dan azatonta zai kara kaiwa sama ne dariya yayi sosai yace "beggy beggy gashinan dai kinyi latti" dariya tayi tajuya tafita daga dakin da gudu ta shiga mota Adamu yaja suka tafi.