👝👝👝👝👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝👝
👠👠👠
👝👝
👠💄💅 *DAN MINISTER* 💅💄
🦚🦚Written by *Husba'ahfama*
*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*
15-16
Ido suka hau mustsikawa suna dada kallan juna
nabil yace ko dai mafarki nakene ban saniba
Shatuwa itama wajan Amina takoma da sauri tace anty Yaya nabil ne wannan Naga Babu shigar da yakeyi ajikinshi ko sarkar Babu
Dariya dukansu suke musu Amina tace nabil ne shatuwa Kinga yacanja ko
Tace eh anty
Rada akunne Amina takewa shatuwa kardai kimanta da du abinda nagaya Miki kifaja ajinki kafin ki saki jiki dashi Amma Naga ke kanki rawa yake niyar ba da kanki kikeyi ke ko Ina se kin nuna wautarki ta ke rikwan kakace
Kafin shatuwa tayi mgn
Nabil yakaraso wajan shatuwa yasa hannu yatabata yaji dagaske itace ba mafarki yakeba hannu yabude almar tazo shatuwa Amina takalla taga Amina na harararta ai shatuwa Bata da mu da gargadin da Amina take mata da Ido na taja ajinta taje da sauri tafada jikinshi suka rungume juna suna dariyaNabil yace Aisha ina Kika shiga nake ta nemanki meyasa Kika gujeni kinsan wuyar da nasha akanki kinsan halin da nake ciki saboda rashinki Ina kikaje du tsawan wannan lokacin nake ta nemanki waye yasaceki
Shatuwa tace ba anty Amina bace ta daukeni ta gudu Dani america baffah da mommy ne suka sata ta gudu Dani Wai Dan muna fada Ni da kai yanzuma se da taga nayi fishi da ita na dameta da kuka sannan tadawo Dani har cemata nayi yanzu mungirma mundena fada Ni da Kai Amma anty Amina Bata yardaba har da yimin fada tafashe da kuka
Amina hanu tadora aka tazamo daga Kan kujera ta zauna akasa tace shikenan angudu ba a tsiraba goyan Kaka Kenan akwai wauta daga temako se yazama lefi
Nabil ransa yabaci kallan su amina yafara Yana rungume da shatuwa Yana rarrashinta yace yanzu Ashe Daman du rokwan da nake Tai muku kunsan Inda matata take kukaki ku temakeni ku dawo min da ita se da itama ta dameku tukunna kuka dawo da ita anty Amina meyasa kikai Mana Haka kinsan halin da Dan uwanki yashiga akan hakan da kikayi baffah har da Kai mommy kema haka wlh daga yau Kar Wanda yakara dauke min Mata ba da saniba Allah bazan yardaba yishuru aishata gidanmu zamu tafi yanzu rabu dasu daga yau Kar wanda yakuma zuwa yace kizo kuje wani wajan ba da saninaba karki Kuma yarda kibi kowa kinji
Tace to Kuma ai kace katsani Mata baka sansu Kuma Nima kace baka Sona Ni bazan bika gidan kaba bayan baka Sona Kuma bakasan Mata Ni awajan mommy Zan zauna ko anty Amina ko nabi iya mutafi mazagai tare
Muryar nabil narawa yace haba Aisha kuskurene ko Ada da nake fada rashin sanine Amma yanzu nagane gaskiya wlh yanzu nasan darajar Mata Kuma Ina girmamasu ako Ina suke ta dalilinki nasan darajar Mata aduniya nasan Kuma wacece mace kema wlh Ina sanki Aisha Ina kaunarki bazan iya rayuwa in Babu keba kin Zama wani bangare na jikina karki min Haka Dan Allah ki temakeni kiyarda mu tafi gida yanzu karkisa su baffah suyi Mana dariya daddy da iya kusa Baki ku tayani bawa Aisha bawa
Shatuwa tace Babu ruwansu wannan tsakaninmune Suma ai shedane agabansu kasha fada baka San Mata ba sau dayaba ba sau biyuba
Kwacewa tayi daga jikinshi ta haura sama da gudu tana kuka aminace tabi bayanta da sauri nabil shima binsu zeyi
YOU ARE READING
DAN MINISTER
Short StoryKubiyoni Dan ganin sabon novel Dina karkubari abaku lbr lbr neme fadakarwa nisha Dan tarwa dakuma ilimantarwa