ZAB'IN RAI NA....Complete

1.2K 33 6
                                    

💕💕💕

*ZA'BIN RAI NA*

             💕💕💕

_*WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍*_


_*DEVOTED TO HAUWA A USMAN*_
              {JIDDAH}

_*BESTOWED TO  MY FAN'S❤*_

_Sak'on gaisuwata agareku masoya a duk inda kuka kasance, ina godiya sosai da soyayyar da kuke nuna min, ina alfahari da ku_
    💓
_*Ina ji da ku sosai Intelligent writer's Allah yak'are had'e kawunan mu*_
❤❤

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®📚*
{On Ward Together}

🔚🔚🔚🔚
*LAST PAGE*
🔚🔚🔚🔚

*PAGE 6⃣2⃣*

Kamar yadda ko su kakus suka yanke hukunci haka kuwa akayi shiryawa sukayi sukaje gidansu Zeey suka ba iyayenta hak'uri nan Kb yarok'e su gafara suka yafe mashi albarkacin su kakus sannan Suka nemi suka Zeey nan Dad yace masu tayi aure, Malam Zubairu ne yarok'i Dad yabashi Address d'in gidan Zeey dan Kb yaje yanemi gafararta Dad yace zai basu ammah sai ya nemi izinin mijinta.

Koda yayi ma Anwar magana cewa yayi bakomai ya amince yaje,.
Ranar wata alhamis Kb yashirya shikad'ai yaje gidan dan Kakus cewa tayi bazatajeba dan bata iya had'a ido da Zeey.

Koda yaje Anwar ya tarbeshi hannu bibiyu har cikin main parlour yakaishi yazauna yasa Azeema takawo mashi ruwa da abinci sannan Anwar yatashi yanufi part d'in Zeey yasanar da ita ammah fafur tace bazata fitoba.

Anwar matsa mata yayi nan tasa mashi kuka tace wlh bazata jeba dan ta tsani Kb bata k'aunar tak'ara had'a ido dashi a rayuwarta.
Jikin Anwar duk yayi sanyi nan yarungumeta yana lallashinta sannan yafara lalla6ata akan tayafe mashi.

Murmushin k'arfin hali tayi tace Ya Anwar duk abinda yafaru laifi nane ba nakowa ba bana fata incigaba da rik'eshi a cikin rai na bayan a yanzu ina tare da *ZA'BIN RAI NA* kaje kawai kace mashi yatafi ni na yafe mashi ammah kar yak'ara tunawa da ya ta6a sanina a rayuwarshi, ni banga ma dalilin da yasa kakawo mana shi a gidaba.

Ganin yadda tad'au zafi yasa Anwar yayi murmushi yace hakan ma mungode 'yanmata, d'aukar sultan yayi yafita nan yake shaida ma Kb akan Zeey ta ce tayafe mashi har cikin ran Kb ya ji dad'i saidai yaso yaganta yabata hak'uri ammah babu yadda ya iya godiya yayi ma Anwar yatashi zai tafi Anwar tausayinsa yaji nan yace kar kadamu Kb nasan halin Zeey sosai tana da sauk'i tunda tace ta yafe toh dagaske ta yafe.
Cikin sanyin jiki yace bakomai Barrister nagode sosai Allah yasaka da alkhairi.
Ameen, dubu goma Anwar yabashi yace yahau abin hawa.
Godiya yayi mashi sosai sannan yatafi.

Bayan tafiyarshi Anwar yakoma yacigaba da lallashin Zeey har saida tasafko daga fushin da take.

Cikin Azeema yana cika wata tara lokacin tafara laulayi, Zeey da anwar sosai suke nuna mata kulawa sannan Dr Sainah tana yawan zuwa taduba lafiyarta da abinda yake cikin cikinta duk abinda tace tanaso shi akeyi mata Zeey bata barinta takauda koda kara, kome saidai tasa ayi ko ita tayi, danginta ma suna k'ok'ari dan suna zuwa sosai sudubata sannan sutaimaka mata da wani abun intana buk'ata koda sunsan Zeey ba k'aramin k'ok'ari takeyi akantaba.

Saida cikinta yashiga cikin wata na goma sannan tahaifo d'iyarta mace mekyau tana kama da ita saidai farin Anwar ne tad'auko, anyi shagali sosai, Zeey ita kanta ta taka rawar gani a sunan dan duk yawanci siyayyar baby ita tayi su haka zata ajiye sultan tad'auki babyn Azeema dan tanason yarinyar sosai.

Ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Azeema watau Aisha ammah suna kiranta da Afrah, lokacin sultan yana da wata takwas dan ma yana da girman jiki kamar ya yi wata goma saboda a lokacin yana rarrafe sosai kyaunshi yak'ara fitowa yakoma Daddynshi sak.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 19, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ZAB'IN RAI NAWhere stories live. Discover now