8

2.4K 192 30
                                    

*NAJEEB*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*MY LOVELY MUM*


                 *PAGE 8*





Granny barin falon tayi,bayan tace ma y'an matan su koma, ta nufi d'akin zarah inda ta iske ibtisam kwance tana baccin wahala,  cikin tausayin ibtisam tace sannu Allah sarki dole kiyi bacci, gocewan k'ashi akwai azaba, targad'e mutum yayi yasha azaba, balle ace k'ashi ya goce

Zarah ta shigo d'akin Tana fad'in Granny bacci take amma kina damunta da surutu.

Granny tace Hmmm, wlh tausayi taban, gocewan k'ashi akwai azaba, Allah sarki takwara, Allah ya baki lafiya, k'aran wayan ibtisam yasa Granny tace wayar Waye haka? Duba ki gani karya tasheta k'aran,  zarah d'auka tayi taga kabir, tace Granny kabir ne.

Granny tace Kabiru dan arziki d'auka kiban, dannawa Zarah tayi tare da mi'ka ma Granny, Granny tasa a kunne dai dai lokacin Kabir yana fad'in my ibti,  da sauri Granny ta cire wayar a kunne tana son fad'in abunda yace mi ibt, lokaci d'aya kuma ta maida wayar a kunnenta tare da fad'in Kai Kabiru grandi ce.

Gaidata yayi tare da fad'in ya Abuja?

Granny tace habuja lafiya, kasan takwaran tawa ta samu gocewan k'ashi koh? Yanzu haka bacci takeyi

Yace Subhanallah, wlh ban sani ba, yaushe hakan ya faru? Dazu nazo na ganta fah?

Granny tace Kabiru a Ina ka ganta ita da take habuja, yace Granny Nima ai nazo Abuja din

Granny tace ah lallai soyayya, toh sai kazo ka dubata inta farka, yanzu dai tana bacci, yace insha Allah Zanzo inganta tare da kashe wayan, yana tunani, wani abokinshi dake kusa Mai suna Tahir yace kabir lafiya kuwa?

Yace Wlh ibti nace ta samu gocewan k'ashi, kuma dazu mun had'u, kai Wlh banji dad'i ba, ko kad'an ban son in ganta cikin damuwa, ina sonta da yawa

Tahir yayi murmushi tare da fad'in ina matsayin amininka, komai naka kana fad'amin amma shine baka fad'amin wannan ba, Allah ya bata lafiya

Kabir ya amsa da Ameen, tare da fad'in sorry Tahir naso sai Abu ya kankama Kafin in fad'a maka, domin kasan dagaske nake

Tahir yace Toh wannan wace yarinya ce haka da Abokina ya mutu a kanta? Gaskiya ko wacece tayi sa'a, toh amma irin halin da kake son mace dashi ita tana dashi?

Kabir yace Sosai kuwa, wannan shine dalilin da yasa na K'ara Sonta, sai dai abunda yake damuna, tana da burin tayi karatu, toh ni banda matsala, infact ma Ina son iyalina suyi karatu Mai zurfi, but matsalan shine ita ta'ki yarda muyi aure wai saita kammala karatu nan da shekara hud'u, ni kuma gashi an matsa min akan ya kamata in ajiye iyali, gashi wacce nake so tace sai nan da shekara hud'u, so ni Abun ma duk ya jagula min lissafi, gashi nace mata na amince data gama karatun, kuma gaskiya ban tunanin family d'ina zasu yarda Wlh.

Tahir dariya yayi sannan yace mutumi na an fad'a love, Niko in zaka dubiya tare zamu inje inga wannan yarinyar data tafi da Abokina, Toh amma Indai har Tana Sonka zata yarda kuyi auran, ai wannan ba hujja bace mace tace saita kammala karatu Kafin tayi aure, hakan bai kamata ba, aure ai baya hana karatu, sannan tace ka jirata shekara hud'u ai yayi yawa, sai kayi ta zama haka? Ni gashi inada yaro d'aya gana cikin na biyu amma kai har yanzu kuma Nima iyalin nawa na karatu, ya kamata ka mata bayani Sosai in Tana Sonka zata yarda.

NAJEEBWhere stories live. Discover now