[9/4, 11:53 PM] ATTABI IBRAHIM: 〰〰〰〰〰〰
*HINDU*_writing by zeeabusafana_
_Mrs'Salihu Bamalli_*dedicated to my fans afuwan kunji cigaban bakar mace da kukan noor shiru nayi losing din komai nawah ne amma in akwai mai su daga farko har zuwa inda na tsaya ya turomin zan karasa muku ngd*
*Ya Malikul mulku zuljalalu wal'ikram ya Allah*
🔳1
Da karfi ta banko kofar tashigo dakin a kan kafet ta jefar da side bag dinta kai tsaye mirror ta nufa duban kanta tashiga yi tana jero tsoki haulat na kwance tana karatu bin Hindu tayi da ido tadai san dagani ta tsuniyar gizo bata wuceta koki!
Hindu ta dafe kai mtseew wallahi talauci da talakan mutum suna ban mamaki dan Allah haulat a ina nai kama da matar kananun mutane ne ni kuwa a rayuwa meh yasa talakawa ke bibiyana ne ni kuwa meh suke gani wanda yakai class dinsu a jikina why? Inban da rigimar tsiya irinta mutane!
To mene ne ya faru kuma yanzu? Mtseew just forget idan na tuna am felling angry wani mutum ne ya biyo ni yana saman mashin ina a mota amma baiji kunyar furtamin kalmar soba saboda tsabar rain in wayo,
Hmm Hindu kenan manya kekam Allah ya nunamin mijin ki a duniya saboda kina da aiki talauci dai da arziki dukna Allah ne kinsani kuma,,,,shiiiit you have to keep quiet is okay naji jikar Abubakar Gumi wa'azin ne ya motso toni kinga wuce wana kai tsaye ta fada bathroom girgiza kai haulat tayi tac'e Allah ya shirye ki Hindu Allah ya ganar dake gaskiya.
Sanye take da Riga da wando na roba wandon mai fadine kanta na daure da bakin gyale ta aza wata bakar Rigar sanyi a sama cikin black cover shoe ne a kafarta masu ratsin ashh! a kafarta ta ratayo black side bag dinta ta gaba zaune take akan kujerar falon tana kallo hannunta rike da cup tana shan hollandia yoghurt papa ne yashigo tare da wani matashin saurayi a bayan sa zama yayi kan kujera yana fadin Hindu kallo akeyi?
Yes papa your welcome barina kira mammy din! Nop barta na danna mata belt tun ina dakina nasan yanzu zata fito!
Risinar dakai tayi cikin girmamawa tace okay, sai a lokacin ta lura da matashin da yake tare da papan kallo daya ta masa taji tsanar sa da kiyayyar sa ta mamaye zuciyarta badan komai ba sai dan tsabar talaucin dake a tare dashi dan kana kallonsa zaka fahimci hakan, a bangaren matashin kuwa ya tsureta da ido yana yaba tsari da kyawun Surar da Allah yamata maganar ta ceta katse masa tunani kamar daga sama yaji tana fadin papa a ina kasamo wannan mai siffar wahala meh yazo yi anan gidan?
Hararta yayi kafin yace yazo neman aiki ne a gidan nan shine zan dauke muku shi a matsayin driver tunda kin kora wanchan, wannan papa zaka daukar mana mai siffar yunwa da kishin ruwa wanda da ganin sa tsiyah da talauci sun sama gindin zama a gurin sa saiya goga mana talauci!!!! tsawar da papa ya mata yasaka tayin shiru tare da zumburar baki tana dannawa saurayin harara mammy ceta sauko cikin fara'a ta sama gurita zauna cikin girmamawa saurayin ya gaisheta itama ta amsa mishi fuska a sake! papa yace mammyn yara ga sabon direba nan nakawo muku dan Allah a kula dashi, insha Allah papa ya sunan sa?Sunan sa Salees yaro ne mai nutsuw da hankali dan haka ka tashi kaje mai gadi zai nuna maka dakinka, godiya salees yayi sosai sannan ya tashi ya tafi duk yinin ranar ran Hindu a bace yake ranta bai kara baci ba sai ranar monday da zataje school kasancewar ta mai son jikin tsiyah da ganda yasaka ko driven tayi gajiyah takeyi dole sai dai akaita a daukota around 9am ta fito Riga da siket ne yan kanti na roba a jikinta ta yafo dan karamin gyale daga kanta zuwa kafada tayi yafin nan da yammata kecewa follow me kayan jikinta pinck ne sai black din gyale da flat shoe shima black hannunta daure da agogon Rolex kirar mata powder ne kawai a fuskarta sai pinck din janbaki data dan shafa a lips dinta sai kwalli data shafawa manyan idanunta bobble pop ne a bakinta tana sha ta ratayo side bag dinta a gaba fuskarta babu annuri ta fito takaici ya kara kamata tunawa da sabon driver da zai kaita tunowa da jin jiya papa ya kirasa da Salees ya sakata bude baki cikin fushi tace' Saleesu! dama yana shirin fitowa ne a hanzarce ya karaso yace dani kike?
Toda da dawah nake ji wani iskancin banza da wofi dallah muje ka kaimu school, a dai'dai lokacin haulat ta fito suka shige back sit get man ya wangale musu get suka danna hancin motar suka bar gidan a hankali haulat tace malan Salees barka da safiya an tashi lapiya? yayi mamakin jinta gaishe sa cikin walwala ya amsa da lapiya lau ranki ya dadeh, ya sabon guri ance kaine driver dinmu daga yau tom Allah yasa hakan shine alkairi! amen ya Allah,,,,,,, Hindu ce tace haulat bana son iskanci fa kindai san bana son surutu to danmeh zaki dame ni da shashancin banza kai kuma ka kula ba aikin dazako yiba kenan inace an dauko kane ka tukamu a mota ba'ace harda bakunan mu zaka tuka ba stupid driver kawai you have to be carefully
Afuwan ayi hakuri bazan sake ba ya fada tare da mayarda hankalin sa akan titin da suke bi yaci gaba da tukinsa haulat kuwa banza taimata domin sanin hali shi yafi komai wuya.