🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*GIDAN MIJINA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
(kalubale gareku iyayen miji)☀FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION☀
F.C.W.A
☀home of qualities and trusted of the nation☀
*MUMMYN SEEYAMA*
*the first class writers of* *the 2019*the author of
*kuncin rayuwa*
*Zaman takewa and*
*now GIDAN MIJINA*~i dedicated this page to my sis Mummy jidda baiwar allah ina matukar alfahari da hot comment naki~ 💞💞💞💞💕💕💕💕🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
*Page* *~5&6~*
Sun gama yawansu da tambaya amma sun kasa samun gidan saboda basu sam mai ake gayawa hafsat ba sunsha wahala sosai haka suka dawo basu samu nasarar samun gidan ba
Ammi taji haushi sosai da rashin gano gidan amma sun kudiri aniya sai sun gano gidan zara taji dadi sosai da basu samu gidan bac
Zara ta lallaba taje ta sanarwa bro dinsu cikin mamaki mai ammi xasuyi da gidan su farhat wannam wani irin kiyayya ammi take yiwa talaka
Zara tace wallahi nima bro abin yana bani mamaki sosai don ko film muke kallo in dai na talakawa ne xatace sai mun cire suna xaune suna tattauna matsalar sai ga sabeer da shaheed sun shigo suka ce yauwa bro a nuna mana antin namu muganta mana kafin ta shigo
Cikin wasa khaleel yace anki a nuna muku wato baxa ku tayani rokon ammi ba
Sabeer yace ai aykin gama ya gama tunda an riga am baka saura musha biki ammi ma insha allahu xata amince
Khaleel yaji dadin maganar sosai nam ya dauko wayarsa ya dinga nuna musu pic din farhat duk tayi kyau duk da a kunshe take a ciiin hijab su shaheed sai gwada kyanta suke yi
Haka rayuwa taci gaba amma soyayyarsu sai kara habaka take amma harcyanxu ammi tana kan bakanta na baxai aureta ba
*Bayan wata biyar*
Yanxu soyayya tayi nisa tsakanin khaleel da farhat komai ya kam kama saura sati daya akai kayan aure asha biki
Amma ammi har yanxu tayi uwa tai makar biya akan baxa ayi aure ba abin ya jawo musu rikici sosai da daddy har tana cewa akan khaleel ya aure farhat gwara ta bar gidan mahaifinsa
Khaleel ya tsorata sosai yacewa mahaifinsa daddy nikam na hakura da auren farhat xan nemi wata daddy yace wallahi baxai yiwu ba karma ka fara aure kamar anyi angama in ta ga dama ta fita mana gari da yawa ai maye maxai ci kansa ba
Ammi dama burga tayi dan baxa ta iya tafiya ba tadhe to shike nam wallahi khaleel inhar kayi auren nam ni dai bada yawu na ba daddy yace tadhi kaje ubana aure kamar anyi an gama
Khaleel ya mike jiki a sanyaye
Daddy ya khaleel ammi yace balkisu bansam mai yasa kika sauya ba wallahi mai makon ki karbaba masa gwaiwa amma ke kike hanashi haba balki karki manta da mai kudi da talaka duk allah ne ya hallicce mu nan dai yayi ta mata nasiha ammi kamar ta dauka amma daddy yana fita ta bishi da harara tana cewa ayi dai mu gani wallahi in ma anyi da kabarta xata fita ta bar mana gidan
Washe gari kanwar ammi jamila ta xo gidan ammi ta gayawa jamila komai akan saura sati daya akai kaya
Jamila tace haba yaya balki yanxu kina nufin shikenam khaleel baxai auri suhaima ba
Ammi tace kar ki damu insha allah sai mun hada ya ranmu aure
Jamil tace ko dayake ki bari akai kayan kinga ta nanne xamu samu damar ganin gidan sai mujr mu shuka musu radhin mutunci yadda xasuce an fasa aure