*🎈HAR ILA YAU NI CE TAKA!* 🎈
(The superheroes and romantic man)*MALLAKAR*:- Sadiya A shehu (stylish bch)
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*
(CLIQUE)Wattapad @zeelishbch
*IN DEDICATION TO*:-
*Zainab D'ahiru Yabour*
*(Zee Yabour)*Page 33......
Itama Aymana karasawa gurinsu tayi sai kale-kale take musamman take kallon Omar dake d'an nesa dasu yana jiran karasawar Faisal shi kuma ya kurawa Haulat idanuwa wadda ba tasan yanayi ba dan ko kallo bai isheta ba duk kuwa da tana son ganin nasa.
''Mutuniyar yaushe kika zo?''
Faisal ya tambaya yana kallan Aymana da ta karasa wajan da suke, tayi murmushi ganin yadda yake sakar mata fuska gashi ya kirata da mutuniyarsa tace dashi.
''Jiya.''
''Masha Allah ashe da rabon zamu had'e, da yau zan koma zaria but na fasa sai gobe.''
Dariya Haulat tayi sannan tace yaje idan ya huta sai yazo suyi hira.
Da sauri ya karasa wajan Omar yana fad'ad'a murmushinsa, tafawa suka yi tare da shiga cikin parlourn inda Faisal yake cewa.
''Kai mutumin ashe nayi farar tafiya.'' Cikin rashin fahimtar maganar Omar yace.
''Ta me kuma?''
''Naga kayana anan gidan naka, kai kaji farin cikin da nake ji dana sameta anan gidan.''
Tsaki Omar yayi domin bai fahimci inda maganar Faisal take dosa ba, baya son irin wannan maganar kawai ayi masa abu kai tsaye sai a tsaya wani kwana-kwana.
''Kai dalla can abinda nake nufi naga baby na anan gidan, kasan fa ni sonta nake yi da gaske wallahi kuma da aure dan haka nasa uwar gidan ka ta dinga kular min da ita, ashe tazo jiya ne.?''
Dam gaban Omar Farooq yayi wata irin bugawa cikin ransa yake ayyana. 'Kardai wannan da yake gani itace wadda Faisal yake so? Innalillahi ta yaya akai har Faisal ya rigasa hango wannan kyakyawar yarinyar shi aka barsa da barambaram gashi ta kasa wayewa har yanzu.'
Shifa Omar duk ya rud'e a tunaninsa Aymana itace Haulatu har yanzu musamman da yanzu Faisal yake bashi tabbacin wannan din budurwarsa ce, ya shiga uku gashi yaji kamar yana jin wani abun a kanta ga Faisal yana sanar dashi yadda yake kaunarta.
''Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.''
Ya fad'a a bayyane ba tare da yasan a fili yayi ba cikin sauri Faisal ya juyo ganin Omar rike da kansa wanda ke tsananin sara masa yace.
''Lafiya bloody? Are u alright?'' Faisal ya jefa masa tambayar lokaci d'aya tare da rike hannun Omar d'in.
Murmushin dole Omar ya k'ak'alo tare da janye hannunsa ya dafa kafad'ar Faisal yace.
''Yaah am okay karka damu just a little headache ne kuma idan nasha magani shikenan insha Allahu.''
''Okay bloody Allah kawo maka sauki.''
''Ameen.'' Omar ya fad'a tare da sake yin wani murmushin.
Tare suka zauna a cikin parlourn kasancewar Omar ya fasa fita saboda zuwan d'an uwan nasa, ga kuma yadda yaji kansa na yi masa mugun ciwo, ga wani irin abu da yake ji a cikin zuciyarsa kamar zata fito fili ya rasa abinda ke mishi dad'i tun lokacin da yaji Faisal yace ga wadda yake so.
A parlour Omar ya bar Faisal, shi kuma ya k'arasa cikin bedroom d'in sa wayoyin hannunsa ya cilla kan sofa d'in dake gefen window tare da cire agogon azurfarsa dake sak'ale a hannunsa, wata iska mai zafi ya furzar tare da yin wata nannauyar ajiyar zuciya.
BẠN ĐANG ĐỌC
HAR ILA YAU NICE TAKA.......
Lãng mạnTunda muka fara ku6ewa da d'an Haruharu a k'ofar gidan nurse Hajara da ko ita ba ta sani ba ya fara jan ra'ayi na har na fara jin zan iya zama tare da shi duk kuwa da cewar ban san mai aure yake nufi ba, amma nasan dole dama wata rana zanyi kuma dol...