Kwan kwasa kofar farid ke da wuya farida tatashi da sauri ta bude kofar ayayin da yashigo gidan cikin karamin lokaci ko ina yacika da kamshin turensa da yasaba sawa koda yaushe tun kafin aurensu,ayayin da kamshin turaren farid ya doki hancin farida batasan lokacin data rungumeshiba,sun dauki tsawon minti guda a rungume da junansu saboda shaukin ganin junansu.farid yakasance ma aikaci akarkashin hukumar kidaya a jihar Kano.Farid da farida sun daukin tsawon wata biyu basu ga junansuba bayan aurensu saboda fostin din da akaiwa farid zuwa garin Borno domin daukar adadin mutanen da suka rasa rayukansu ayayin da hargitsin boko haram ya yawaita ayankin.Domin kuwa auren farid da farida bai wuce wata uku ba aka turashi Borno idan aka hada da wata biyun da yayi suna da wata biyar da yin aurensu kenan sai dai abinda farid bai saniba tsawon wannan lokacin shine farida tana da cikin da yakai wata hudu,shine ma dalilin da yasa lokacin dayake a gombe a duk lokacin da suke waya sai ta gaya masa cewar tanajin kasala ko kuma tana marmarin wani abu daban ba abinda yasan tasaba ciba,amma abinda da sabon yankan rake baigane abinda take nuifiba.har sai da yayi kwana biyu da dawowarsa take gaya masa tana da juna biyu,farid yayi matukar jindadin wannan albishir din da farida tayi masa domin kuwa yasan bada dadewaba zai Zama uba shima.Haka abubuwa suka ci gaba da wanzuwa tsakaninsu domin kuwa akoda yaushe suna tare saboda yanayin aikin nashi yanzu agida yake.
Wata tara farid yadawo sai yayi yunkurin bude gida sai yaji kofar gida akulle wanda yake nuni da babu kowa agidan.yayi matukar mamakin hakan saboda irin hakan bata taba faruwa dashiba.
Farid yayi sauri ya ciro waya agaban aljihunsa ya danna ya lalubo lambar wayar farida wacce yayi sabin din lambar da QALBEE danna lambar keda wuya yaji anace masa, the number you are calling is currently switched off please try again later,ya kara kiran wayar amma dai abu daya wayar take gaya masa.Yana tsaye cikin rudani,tashin hankali da tunanin ko meyake faruwa sai ga Alh.Aminu yazo yana tambayarsa dafan masu juna biyu ansauka lafiya? Nasan haryanzu basu dawo daga asibitinba,duk wannan maganganun da Alh.Aminu keyi farid baice komiba,budar bakinsa ke da wuya sai yace wanne asibibin aka kaita? Sai yace eh to naji mai dakin tace AKTK,ma'ana Aminu Kano teaching hospital.Nan da nan ya shiga cikin motarsa ya kunna yatafi cikin sauri da fargaba.
Zuwansa asibitin ke da wuya ya wuce maternity section in da da zuwansa ya hango aunty Hafsa tana kokarin shiga cikin wani daki mai lamba ta goma (10C).farid da sauri yace aunty Hafsa Assalamu Alaikum,ashe harda ke,barka da kokari ya jikin farida fa? Ta amsa masa da cewar angon karni nasan yanzu arude kake ai ansamu 'ya mace zanka dediya kamar ita taikanta,son kowa kin wanda bazai samuba. Farid bakinsa yakasa rufuwa saboda matukar murna,nan da nan yace da ita don Allah tayi masa iso zuwa dakin,aunty Hafsa tace toh ai dama nima dakin zan koma,aunty hafsa tayi gaba farid na biye da ita abaya.Isarsu cikin dakin da farida take kwance ya hango inna Larai,yayin da agefe daya kanwarsa Ramlat ke rike da jaririyar da aka haifa masa.Kasa yayi da kansa domin kuwa yana matukar kunyar inna larai wacce take kanwar mahaifiyace agurin farida,ya durkusa hadi da tattare babbar riga,yace ina wuni, inna larai tace lafiya barka da zuwa kana tafe ashe,yace eh na dawo gidanne daga gurin aiki sai naga gidàn a kulle shine makocine ke sanar dani cewar ai kuna asibiti,surutun gaisuwar su inna larai da farid shine ya tashi farida daga baccin da takeyi mai nauyì domin bakaramar wahala tashaba wajen haihuwar nan,tabude idanuwanta ahankali wanda suke nuni da irin yanayin da take cikin,da sauri farid hankalinsa gaba da ya koma wajen farida yajuya yana maicewa ya jikin naki,dafatan kina cikin koshin lafiya?ya tambayeta ta amsa masa da motsa kanta cikin shagwaba irin wacce tasaba yimasa.Inna larai tafuskanci yanajin kunyarta matuka sai ta tashi ta fita waje,fitar inna larai keda wuya ya koma bakin gadon da farida ke kwance ya zauna yana taba Mata kunci da hannusa sai aunty hafsa tace kai mara kunya abin haryakai da ka daina jinkunyata ko!lallai kam ayi mugani idan tusa zata hura wuta.
Sallamar inna larai ce tasa ya tashi tsaye ya koma kusa da Ramlat yayin da hankalinsa ya koma kan yarinyar da aka haifa masa,Ramlat ce tayi masa nuni da ya dauki baby hakan yabashi damar rage kunyar da yakeji yadauketa yayi duba izuwa duka fuskarta yayin da ya ga rabin kamannin ta nasane rabi kuma na farida ne.
Sallamar nurse din da takarbi haihuwae farida ne yasa ya dauke kansa daga baby ya juyo ya kalli nusrse din yace barka da zuwa,ya aiki tace alhamdulillahi ya naku yace mungodewa Allah.Toh ai yanzu sai ku fara shirin tafiya gida tunda mai jego ta haihu tafiya kuma babu wani abinda yake damunta.