🏃🏻♀NA SHIGA BAN 'DAUKA BA🏃🏻♀
(Bata fidda Barawo)
Nah
Marubuciyar ZamaniNABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... NabeelertladyBismillahirrah Manirrahim.
1⃣➡️5️⃣
Ka taimaka mani *GAGARABADAU* kasan dai halin da nake ciki tunda ba yau muka fara tarayya da kai ba, tun farko sai da nace maka kada ka bari ayi auren nan amma kace na bar maka komai, gashinan tun ba'aje ko ina ba Yarinya tayi ciki, babban tashin hankalina ban tashi sanin cikin ba sai da ya girma, domin Alhaji ya d'auketa sukayi wata tafiya kusan wata biyar, suna dawowa sai dai naga ciki a gabanta ko yanzu zata iya haihuwa, nasan dai dama dashi ta tafi ban kula tana dashi ba.
Dariya Gagarabadau ya shek'e da ita yana fad'in haba *DEEJENBA* me kike ci na baka na zuba? Nine fa *GAGARABADAU*, d'aya nake tamkar da dubu, kowace irin matsala gareka matuk'ar kazo wajen Gagarabadau buk'atar ka ta biya, ban fara wannan sana'ar ba sai da nashirya, domin duk duniya babu abinda na tsana kamar a bani aiki yafi k'arfina, shiyasa sai da na kwashi shekaru ina koyon wannan sana'a kafin na bayyana kaina, aljanun da suke kaina sun wuce tunanin ki, suna mani biyayya kamar yanda nake masu, koda cikin Uwa nace su shiga su d'auko mani 'Danta suna aikata hakan, dan haka ki barni kamar yanda nace maki.
Gyara zama Deejenba tayi tana fad'in ina sauraronka Gagarabadau ya za'ayi? Kallonta yayi da jajayen idanuwansa yana fad'in kinsan ni ban cika tsauwalawa a harkar aure ba, shiyasa ki kaga aikina yana tafiya dai-dai, shiyasa da farko da ki kace a hana auren nace maki ki barsu suyi auren su domin shi aure ba'a masa shishshigi, sai dai bazan tab'a bari suyi farin ciki da auren ba, dalilin da yasa kika ga sun kai har haka suna farin ciki wannan laifin ki ne, domin kin b'ata mana rai, amma yanzu tunda kin dawo zan taimaka maki.
Risnawa tayi tana fad'in ayi hak'uri Gagarabadau wancan lokacin gani nayi bana cikin tsarki shiyasa na bijirema buk'atar ka, kuma da naji kace in tafi na d'auka ka fahimce ni ashe haushi kaji, shikenan baza'a sake ba, idan ma biyanka wancan bashin zanyi yanzu a shirye nake.
Washe baki yayi yana fad'in yanzu kam baki da matsala, ina mai tabbatar maki har abada kishiyarki bazata haihu agidan nan lafiya ba, kamar yanda kika sadaukar da mahaifarki ga aljanu na domin auren mijin ki, kuma kika sadaukar masu da jinin al'adarki domin samun yanda kike so a gidanki, ina mai tabbatar maki baza kiyi kuka ba, domin su kansu suna jinjina maki, shiyasa har yanzu kika ga mijinki yana maki soyayyar gaske, ko aurenshi na fad'a maki had'in Allah ne, kuma kin gani har yayi auren kina nan a matsayin ki.
Murmushi tayi tana fad'in nasan haka Gagarabadau, tunda har yanzu nice nake haskawa a wajensa da danginsa, rashin haihuwata betab'a damunsa ba, dukiya kuwa har yawa takemun, shiyasa nima bana kyashin na mallaka maka komai.
Gagarabadau yace yanzu kibar mani komai, zan saka ido zuwa lokacin haihuwarta nasan aikin da zanyi domin bazan bari kowa ya rakata asibiti ba ita kad'ai zata tafi, zansa aljanu suyi mata jagora ta yanda babu wanda zai fuskanci komai, sauran bayanin zaki zo kiyi mani godiya domin wannan karon zan maki aikin ban mamaki.
Dariya tayi tana fad'in shiyasa nake sonka, tashi mushiga daga ciki. Washe baki yayi ya mik'e yana gyaran gajeran wandonsa na gado.
**** ****
Wai *IZZATU* ba kiranki nake ba kinshige d'aki kamar bakya jina. Fitowa wadda aka kira da Izzatu tayi jiki a sanyaye tana fad'in gani *YADIKKO*.