Shekarun en mata

47 3 0
                                    

Hindatu er Shekara goma Wacce ta tashi A gida tare da en uwanta da iyayyen ta A garin Gwarzo dake Jihar kano.
Aisha Asalin sunan babar hindatu wacce suke kiranta da yakumbo, Abubakar sunan mahaifinsu.
Baban su hindatu matansa Uku, Asabe wacce suke kiran ta da iya ,sai Fatsima wacce suke kiran ta da yadikko.
A dakin su hindatu Tanada yayye uku duk maza yaya Yusha'u, yaya Idris da kuma yaya yusif.Sai iya na da yara biyu mata wanda sun kasance kannan Hindatu ne Jamila da Halima sai kuma yadikko nada yara Bintu da Asma'u.

"Hindatu" baba yayi kira da karfi a tsakar gida.
"Mallan" ai hindu na daki tana Aikin nan nata wato bacci"cewar yakumbo mahaifiyar hindatu.
"Daman nazo wucewa ne sai naga Abinda hindu ke so wato  Guava na siyo mata, Amma tunda bacci take bari na bawa kannan ta, ita ba rabon ta bace" 
"Jamila da halima kuzo ku karba", sukayi gudu suka nufi baban nasu dan karbar tsaraba.
Yakumbo rai bai so ba, ta shiga cikin daki inda ta tarar da hindu tana ta sharar bacci.
Tas!Tas kake ji karar duka da yakumbo takaiwa hindu a cinya, tace" tashi me baccin Asara kawai, gashi nan Garin irin shegen baccin Nan mallan yabayar da Abinda yakawo miki"
Tai maza ta tashi tace "me ya kawo yakumbo?
" ba a Saniba"Cewar yakumbo tayi shigewar ta tabar ta nan.
Ni dai Hindu nashiga uku da wannan bacci komai sai yayita shige a garin bacci, toh bari na tashi nayi sallah in roki  Allah ya ragemin baccin nan kar wata rana babban rabo ya wuce ni.
"Ke kika sani" yakumbo tace.
Hindatu ta tashi tayi Sallar la'asar tayi shirin islamiya.tace "yakumbo na tafi makaranta" .yakumbo tace "Allah ya bada Sa a kuma a rage bacci a ko ina ma",  toh Yakumbo insha Allahu.

A islamiya Mallan Mubarak na ta kira'ar kur'ani wanda hakan ke nufin yana wa Daliban Karin kur'ani ne.
" hindatu Abubakar! Mallan ya kira sunan ta", "naam" hindu ta Amsa, Mallan yace "tashi tsaye",  hindu ba musu ta tashi.Ita tasan me tayi shiyasa Abin baiba ta mamaki ba. Mallan ya cigaba da karatu har sai da yagama sannan yace ta zauna.
Bayan Antashi daga Islamiya Suna tafe da Jamila da halima kannenta.Tace Wallhi yau a gajiye nake, Sukace " Anty mekikayi  yau din" Tace "Ubanku nayi" Daman kamar tana jira, dayake sun san hali Abun ko Damunsu baiyi ba.Sukayi Shiru har aka isa gida.
Da isar su gida suka tarar da kowa da kowa a tsakar gida Ana ta hira cikin raha, Sai yaran kowa ya koma Dakin su ya cire uniform suka fito.
Baba yace"yawwa yara na maza kuzo kuyi shara"Hindu da saurin ta tace baba dan Allah su halima suyi ni wallah Agajiye nake"Uban mekika yi dakika gaji daman fa ke er rainin Wayo ce"cewar Iya.
"Kyalleta dai dayake su, su haliman basu san ciwon jikin su ba ko" Cewar Yadikko."ai ni narasa Aikin datayi har ta ce tagaji, kuna kallo in banda bacci bawani Aiki datake yi". "Nifa wallahi yau danaje islamiya A tsaye na wuni fa" cikin kuka cewar hindu."aike kika ja, hala aikin dakika saba shi kikayi shiyasa mallan ya ladabtar dake, maza dauki tsintsiya ki fara, ni Aisha Bansan Ya zakiyi ba idan bama tare, nima fama nake balle Wata"inji Yakumbo.Mallan dayaga Duk sunyi Wa er tasa haka Sai yafice yabar su a nan.Haka Rayuwa tacigaba A gidan su Hindu, wadda kullum yakumbo da baba na iyakar kokarin su wajen Tarbiyar ta da sauran Yaran.
Mallan Abu Sunan Mahaifin hindu Wanda haiffafen dan Gwarzo ne, ya taso a Zamanan ce shida En Uwan sa Hudu, biyu mata biyu maza.Sunyi karatun boko da islama, A inda Mallan Abu ya tsaya A iyakar Diploma a boko sai yayi sauka A islamiya.Baban mallan Abu cikakken da Kasuwa ne wanda yake Sana'ar Saida Kayan Awo Acikin Kasuwa.Yakasance indai yaransa suka Girma Dole sai kayi Sana'a sannan ka cigaba da rike kanka.Haka baban Su hindu Yafara irin sana'ar baban sa , Har ya bunkasa A kasuwar yadda, Akasan shi a kasuwar sosai saboda rike Amana da Koma Rashin Algus.Yayan Mallan Abu wato mallan Abdurahman yakoma cikin kano da Zama, inda ya kafa runfar sa A kasuwar rimi yana Sana'ar saida kayan Awo.

Haka rayuwa tacigaba, inda Su mallan Abu ke sada Zumuncin su, har yakan je kanon yayi sari ya sauka wuron mallan Abdurrahman.Ana haka mallan Abdurrahman kecewa mallan habu me zai hana ka dawo nan kano, ka kuma bude shago can kuma sai yusha'u yazauna.Mallan Abu yayi na am da shawarar, sai dai yace"Amma gida da iyali na fa", Mallan Abdurahman yace sai ka dawo da biyu nan can kuma Sai kabar Aisha da yaranta.Mallan yayi godiya da shawarar sai yakoma gida yatara iyalinsa.yake gaya musu Abinda zai aiwatar.Kowa yana Murna har ita yakumbo Wadda daman tafison zaman  Gwarzo tunda nan ne mahaifarta ga en uwanta a gari gashi tana Sana'arta Sosai.Hindatu ita kadaice bata murna Saboda ance Anan babarta zata Zauna kuma, gashi gaskiya ita tana son Zuwa kano saboda taji me En kano keji da kanon nan.
"Baba" hindu tayi kira yadda dakaga fuskar kasan babu walwala."mene? Hindatu gwarzo"baba yafada yana er dariya."nafi Gaskiya bazan Zauna a Gwarzo ba"Hindu tafada, "meyasa" inji baba yana er dariya saboda yasan Za'a rina, Nifa Wallahi Daman yadda yakumbo kemin banaso kuma dan tana ganin a Gabanka ne.Gwara na bika nazauna agun iya, tafada tana kallo iya."babu komai hindatu aike ma y'a tace"inji iya.Hindatu ta rungume iya tace Shiyasa nafi sonki Ai.Yakumbo dai ba Abinda tace sabodabata son tayi magana Mallan yace daman Bata son su iya.
Haka dai Lamari ya faru,Mallan habu yakoma Kano dazama, Inda gidan shi yake Sharada.
Su Hindatu an shiga Makaranta, Inda yanzu tana JSS3 Komai na rayuwa yafara Chanzawa,Tun daga jikin ta tasan Abubuwa fa sun chanza, tafara Girma kuma ga Shekaru sunkaru Ga Iya tagaji da halinta, Saboda haka baba ya bata Daki ita da kannen ta.Yanzu Dai encin kanta takeci a gidan, Bamai kula da ita Abincimata, ,  Ana bata Sai babu kulawa irin ta Uwa a tattare da ita.Dun haka Yanzu tafara tashen ballagar ta ga babanta baida lokacinta, Sai ta tashi Asakaka babu Shawara dakowa sai kawaye inda Allah yataimake ta kawayen na gari ne.
Hindatu ta cigaba da rayuwa a cikin gidansu inda bamai matsa mata, Matan baban babu ruwan su da ita, ba abinda suke mata, Takanyi waya da yakumbo A lokaci lokaci Amma irin wayar nan ta gaisawa kawai, babu tambayar Ko tana wani hali, har hindu tasaba da Zurfin ciki.kafin kasan Halin da take ciki zaka dade.
Watarana yadikko ta Aiki Hindu Shago siyo mata tiara.Hindu na tafiya taji Ana baiwar Allah Jimana, Hindu ta tsaya yace"Dan Allah inda ake saida kankara nake nema"tace "layin mune Amma bari naje Aike sai na dawo nafada maka" yace "Bari kawai na rakaki kar naje ki gudu" tace "toh" suka tafi.
A hanyar su ta dawo wa yace"ke kamar ana siyarwa a can layin zoki rakani tunda nima na rakaki, kuma ko bama haka zakiga Gurin ki dinga zuwa"Toh hindu tace, ta bishi yakaita wani layi a kango inda babu mutane yaso ya lallata ta,Ita kuma bata gane ba Har yakusa Shawo kanta, Allah ya taimaketa, ta gudu.Ta dawo gida ba wanda ta fadawa da akace meyasa ta dade sai tace babu ne saida tayi tanema.
Shekaru suna ta tafiya, lokaci nata Gudu Ga Hindu a SS2 Inda ta koma wata Makaranta wadda ta shahara da masu kokari da kuma Masu ji da kai.
Hindu ita dai a tsakiya take Baza'a ce mata me kokari kuma baza'ace dakikiya ba.Hindu tayi kawaye Sosai, Sabida ita ganin ta sune en Uwanta.Yanzu dai hindu Shekarar ta Sha shida, Wato shekaru masu rudi a Shekarun y'a mace,Shekarun da kowa yana ganin kafara Girma, Shekarun dakomai akace kayi zakayi batare da musu ba, Shekarun da bakowa ya san ciwon kansa ba, Shekarun nada dadi shiyasa suke cewa "Sweet Sixteen'.
Hindu takai Shekara Sha shida A duniya.Inda yanzu dai hindu na kan karatun ta, idan akayi hutu takanje Wajen yakumbo tayi sati.idan zata dawo Takan dawo da tsaraba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 12, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Shekarun En mataWhere stories live. Discover now