CHAPTER ONE

143 8 0
                                    

🌎 *ACIKIN RAYUWA*🌎

*By :Zeety A-Z*💞

Wattpad@Zeety-AZ

_Da sunan Allah me rahma me jin kai_

_Allah kabani ikon fad'an abunda ya dace ka kuma d'auka ka rubutu na yaje inda banje ba kuma yaje inda banyi tunani ba_

*wannan labarin ba kirkirarre bane true life story ne, bakomai yasa muke rubuta shi ba saidon mutane su dauki daradin dake cikin shi, Allah yasa mudace*

*Base on true life story !*

*CHAPTER ONE*


Kuka takeyi sosai ,mamanta da take zaune a gefe ta tsura Mata ido tausayin er tata yana kara ratsa  zuciyarta, gwaron ajiyan zuciya ta sauke, tace

“ ladi kiyi hakuri haka kibar kukan nan,kowa Yasan mutuwan aure ba dad'i saidai kuma idan yafaru babu yadda mutun zaiyi face ya d'auki kaddara”

Hawayen ta ta goge, tare da cewa

“wallahi mama ni ba mutuwan aure na nakeyiwa kuka illa makomar rayuwar Beena da ya kwace ta, kwata kwata fa shekaran ta biyu ne,kuma mama kinsan yadda rayuwar gidan yake ko kashi da kyar asamu me wanke Mata, ta yaya yarinya er shekara biyu zata iya kula da kanta”
Cikin matsananci kuka takarashe maganan…

gefenta mama tazo ta zauna kafad'anta ta dafa sannan tace

“ladi Allahn  da ya halicce mu yafimu sanin halin da zata shiga kuma yafimu sonta, Allah ya kan iya d'auke uwa yaraya d'a balle ma dukan ku kuna raye saiki godewa Allah…

haka maman ta tayita Mata nasiha tare da lallashi har saida taga zuciyan ta yayi sanyi sannan suka tashi domin yin Sallan azahar…

Haka ladi taci gaba da rayuwa a gidan su tare da maman ta, da dad'i ba dad'i suna rayuwar su cikin godiyar ubangiji, duk da tafara samun kwanciyar hankali amma hankalin ta nakan Beena don makwaftan su suna bata labarin halin da take ciki na maraici acikin gidan dukda lokuta da dama mama tana hanasu gaya Mata, don duk randa taji labarin Beena ko abinci bata iyaci, sai mama tayi da gaske.

Acikin wanna satin ladi tagama iddanta kuma cikin ikon Allah tasamu wani bazawari police, mama ce tabata shawara data aureshi, domin aure shine kad'ai rufin asirin mace..

hakan kuwa akayi bayan wata daya aka daura Mata aure da Musa police, ta tare a gidanta dake police Barack.

Duk yadda ladi take tunanin samun farin ciki da kwanciyar hankali abun ya gagara, saboda sam musa ba mutumin kirki bane, baya bata abinci ga kuma shan biya badama ta mishi magana akan halin shi sai ya rufeta da duka gashi sai lokacin taji ashe auri saki ne dashi, tayi tunanin sanar da mama amma tafasa don tasan hakuri zata bata,don haka tadanne ranta tasama ranta salama…

ranan ta tashi batada ko Sisi kuma bata da abinci, hakan yasa tayi tunanin zuwa gida ko zata samu wani abu.

Kallo d'aya mama ta Mata tagane tana cikin tashin hankali, bayan sun gaisane ta tambayeta ko lafiya ?
Ce mata tai jari takeso ko omo ne tana sayarwa, take mama tagane matsalar erta, wucewa tayi inda take ajiya, ta d'auko dubu d'aya da d'ari biyar tabata tace” wannan zai isheki ki saro biredi na dubu daya saiki hada da akamu na dari biyar,nasan zaki sayar kisamu riba kuma kema kici aciki,  kici gaba da hakuri kinji..

Ta mika mata, karba tai tareda yiwa mama godiya sannan takoma gidan ta...

Ba laifi tadan samu sauyi don ko bakomai  tanasamun abunda zataci, shi kuma musa kwata kwata ma yadaina ciyar da ita.

Da gudu er makwaftan su ta shigo tana cewa maman ladi kizo ki gani Beena zata mutu… a rud'e mama ta d'auki gyalenta suka fita basu tsaya a ko ina ba sai gidan su Beena wato tsohon gidan da ladi ta fito.

*ZEETY DELIGHT*

ACIKIN RAYUWAWhere stories live. Discover now