chapter four

35 2 0
                                    

🌎 *ACIKIN RAYUWA*🌎


*By :Zeety A-Z*💞


Wattpad@Zeety-AZ



*CHAPTER FOUR*

Haidar sabon ango kullum cikin dirzan angonci yake, ita kuwa Beena ta d'aukarma kanta alk'awarin bazai tab'a neman abu tahanashi ba, tunda shima babu abunda ya ragan mata…

haka rayuwa taci gaba komai yana tafiya musu daidai.

Beena tasamu ciki har ya girma batada wani damuwa a rayuwar don tarairayan da take samu wajen haidar ba’a magana.

Bayan shekara d'aya Allah ya azurta su da yaro na miji sun sa mishi suna Ubaid, a wannan lokacin beena  tana kokarin gama NCE… 

matsala d'aya take fuskanta a rayuwar ta shine *dangin miji*, sun samata ido kuma ba’a wata basuzo ba, zuwan su ma bashine laifi ba kamar yadda  kullum sukazo sai sun bita da sharri, takanas maman shi take turo kannen shi idan kuwa suka zo babu maganan arziki tsakaninsu da Beena sai bakar magana haka zasuyi ta takura mata harsai sun tafi, sai yanzu tagane meyake rabashi da matanshi da ya aura… shi bashida matsala ko kad'an saidai dangin shi, duk matar daya aura ganin suke arziki tazo ci.

Ana cikin haka wani rana yasamu invitation daga wani company daya taba aiki dasu a UK  zasu bud'e branch a Nigeria a Rivers kuma shi sukeson su baiwa managing director (MD) na wajen, saboda yataba aiki dasu kuma sunsan halin shi.

Anyi komai angama har anbud'e company saura su tattara su koma potakol, a wannan lokacin kuma Beena ta kammala NCE ta.

Sun koma Rivers arziki ya ninka nada zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan su ba a magana.

dangin mijinta kuma ganin sun kara nisa hankalin su yakara tashi… don haka yanzu idan aka turo mutun sai tayi ko yayi kamar wata biyu kafun ya tafi… Beena kullum dannewa takeyi bata tab'a nuna mishi dangin shi na mata abu, shima da yake yasan halin enwanshi kullum cikin bata hakuri yakeyi akansu.

Beena ta kara aihuwa tasamu baby girl *NUSRA* wannan lokacin tafara tunanin komawa makaranta domin yin degree kuma tasamu goyon baya agun abban su Ubaid, shi yayi mata processing komai  tasamu admission a ABU.

Dagajin wannan labarin maman shi tace sai a d'auko mata yaran shi tunda matan shi makaranta zata tafi batada lokacin zama a gida ta kula mata da jikoki… ananne matsalar su tafara tsanani saboda dama haka sukeyiwa matan shi daga mata ta aihu sai a kyautar da yaron a dangi itace ma akabarta da yaranta sai yanzu aka kawo musu hari.

Basu tashi d'aukan yaran ba saida suka bari ta tafi makaranta akazo aka d'aukesu… shima haidar bayaso saidai babu yadda zaiyi da mahaifiyar shi..

haka ta dawo daga makaranta ta tarar da yaranta basa nan sannan kuma har an aura mishi cousin dinshi wai don duk takoma makaranta.

Don haka Beena batabi takan kowa ba tashirya ta tafi garin su haidar kuma cikin nasara tasamu tasato yaranta, tana fitowa a gurguje ta tari mota a hanya tashiga suna isa wani kauye tasauka takara shiga wani motan haka take ta tafiyan tana canjin mota saboda tasan zasu iya biyo bayanta.

Maman haidar dawowa tai daga makofta dama tabar su ubaid da me aikin tane ita kuma tashiga ban d'aki kenan Allah ya baiwa Beena nasaran d'aukan su.. koda tashigo taji shuru gyalenta take ajiyewa tareda cewa yanzu haka yaran nan bacci sukayi, sakalallun banza babu abunda uwarsu ta koya musu sai bacci da shegen turanci kamar yaran arna, d'aki tawuce don dubasu amma fayau ba kowa, duka d'akunan gidan ta duba basa nan… kira tafara kwallawa me aikin ta wanda yasa ta kwara ruwa ba shiri ra fito a kidime don dagajin kiran tasan ba lafiya ba, a kid'ime Anna tace mata ke lami ina yaran nan? Cikin rawar murya tace suna d'aki lokacin dana shiga wanka…cikin tsawa tace d'akinwa nace miki d'akin waye? Tunda nashigo nake dubasu bangansu ba babu d'akin daban duba ba…

yau nashiga uku ni Anna waye yazo har gida yau d'auki yaran nan… cikin tsawa tacewa lami maza ki d'auko hijabin ki muje nemansu kin tsaya kallo na bayan duk laifin ki ne..

Waje suka fita suna ta rarraba ido wani shagon anguwan suka nufa, gaisawa sukai da me shagon sannan  Anna tace dan Allah Isah bakaga yara biyu sun fito daga gidana ba?

Eh nagansu tareda maman su.... cikin hanzari Anna tace waye maman su? Isah yace matar Haidar naki (dayake dama tana zuwa shiyasa ma yaganeta).. cikin kad'uwa Anna tace shikenan tasace su wallahi.. gida suka wuce cikin sauri suka bar Isah da mamaki mata da yaranta ace wai tasacesu baki ya tabe yace Allah ya kyauta.


Suna shiga waya tad'auka takira wani d'anta dayake zama a garin tace maza yazo, yana isowa ta shaida mishi abunda yake faruwa tace kuma yayi hanzari yaje tasha yasanar musu duk wanda yaganta a kamata yaran mutane tasace.

Sunje duka wajen shiga motan gari sun bada cikiya, amma shuru har yamma ba’a sameta ba.

Anna ce takira haidar tashaida mishi abunda yafaru.. yasha mamakin jin abunda Beena ta aikata wato tana nufin mahaifiyar shi batada iko da yaranshi kenan, dahar zataje ta sace su, wani zuciyan kuma ce mishi yai amma ai ba‘a kyauta mata saboda babu wanda yagaya mata, jingina yayi da kujera yana tunanin yaushe ne Anna zata daina shiga hurumin gidan shi, meyasa duk auren dazaiyi saitayi sanadin mutuwan shi.. ajiyan zuciya yai sannan yace ai yanzu kam na auri wacce takeso yakamata su sakanmin mara haka, sarai yasan Beena bazata wuce kafancan ba amma yaki gaya musu don bayason su takura mata akan yaranta.

Ita kuwa koda ta tashi bata tsaya ko ina ba sai gidan su, kannen ta sunji dadin ganinta duk sun girma ko maryam ma yanzu tana secondary su Ayuba da ibrahim sun kwana biyu da gama secondary haidar yasama musu makarantun gaba da secondary kuma suna sana’a domin sun saba da kula dakansu tun maman su tanada rai ma basu tab'a ganin baban su ya musu komai ba balle yanzu da bata nan.

Bayan sun gama farin ciki da kannen ta, take shaida musu abunda yake faruwa dukansu jikin su yayi sanyi, maryam ce tace toh anty yanzu in sukazo fa? Beena tace shiyasa bazan zauna anan ba, gidan mama(kakarsu) zanje inbud'e d'akinta in zauna anan in sungama ribibin nema na zan kira abban su Nusra in sanar dashi, nidai yaranane bazan iya bar musu a rabasu a kauye kamar marayu ba.

Da maryam suka tafi gidan mama, ita ta tayata share share sannan  suka shiga…

Anna duk ta gigice har anyi sati shuru.... danta yakawo mata shawaran ko zasuje garin su Beena ne su duba ko can tayi? cikin hanzari tace yauwa amma yaron nan kafini tunani ai ni nasan ma bazata yuce can ba, gobe da asuba kazo mukama hanya .

Washegari Anna da yaranta uku suka tafi garin su Beena mace daya da maza biyu… dayake sunzo daurin auren su Beena shiyasa gidan bai b'ace musu ba, saidai basuyi nasara ba don basu sameta ba, su maryam kuma sun sheda musu sam Beena batazo ba, saidai hankalin su Anna bai d'auka ba …

don haka tsayawa sukai a waje suna tunanin abunyi, wata yarinya ce en mata zata wuce su Anna suka tsaida ita ko tasan inda Beena take, daga farko cewa tai bata sani ba amma da Anna taciro dubu daya take yarinyan tafara washe baki tana cewa kuzo muje ranan naga maryam tafito da yaran Beena daga gidan maman ladi…

*ZEETY DELIGHT*💗

ACIKIN RAYUWAWhere stories live. Discover now