17

120 10 0
                                    

*°🔘°AMEENATU°🔘°*
         *1441H/2020M.*
               
    

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_

    '''🎐 G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE🏇🏼*•_




*NA MARUBUCIYA:-*
*REAL QUEEN ✍🏼*•
~INSTAGRAM~
~real_queen_abeedat~
~Wattpad~
~REAL QUEEN~



*SADAUKARWA GA DUKKAN MASOYA WANNAN LITTAFIN NA AMEENATU ALLAH YA BAR ƘAUNA•*

*MY KHADY (JIKAR HAJIYA) REALLY MISS YOU PLEASE COME BACK ❤❤.*

*MY IN LAW INA YINKI IRIN TOTALLY ƊIN NAN KE ƊIN TA MUSAMMAN CE TAWAN🌹🌹🌹.*




*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

*SHAFI NA 17📑*

*__________*📃"Shamsuddeen! Shamsuddeen!! Shamsuddeen!!!,wai wannan wanne irin baccine kake yi?, tun bayan sallar asuba daka koma har yanzu baka tashi ba, ka tashi ka je kayi wanka,Su Nuraddeen har sun gaji da jiran ka sun tafi".


     Da kyar ya iya tashi dan baccin dake kansa bai sake shi ba.

       "Shamsuddeen ka tashi?".

        "Eh na tashi, yanzu zan shiga wankan,a kawomin breakfast".

        "Ok tohm kayi sauri".

     "Uhnmmm". Gaba ɗaya jinsa yake kamar wanda aka yiwa duka, duk jikin sa a mace.

        Da kyar ya iya kai kansa cikin toilet,Yana shiga ya sakin ma kansa shower,gaba ɗaya sai ya tafi tunanin wannan mafarkin da yayi _(kenan duk abinda ya gani mafarki ne,kai *gaskiya* bai so ba,ina ma ace a gaske ne,dan *gaskiya* yana matuƙar son kasancewa tare da ƙanwar nan tasa,sai dai ba zai ji daɗi ba,saboda Nuraddeen yana matuƙar ƙaunar ta,inda ya godewa Allah da ya zama a mafarki ne Nuraddeen  yace ya sani yana sonta,kaiiii Wannan inda gaske ne da yaji kunya)._

      Haka yayi ta tunane-tunanensa har sha-ɗaya sannan ya fito daga wankan,yana duba agogon bangon ɗakin yayi saurin tashi,"kai *gaskiya* na daɗe a wankan,nasan ma an ɗaura auren bari nayi sauri kafin su Nuraddeen su dawo".yana magana yana shiryawa kafin ya gama shiryawa yaji ana kwankwasa kofar ɗakin,yayi tunanin Yaya Maryam ce,amma me yana buɗewa yaga Nuraddeen da alama yana cikin damuwa dan ga idon shi yayi ja.

       "Nuraddeen lafiya na ganka a haka?".

        "Shamsuddeen na rasa ta! na rasa ta!! na rasa ta!!!". Yana maganar idonshi na zubda kwallah.

      "Subhanallahi Nuraddeen kuka fa kake? Wacece ka rasa ɗin?".

         "Shamsuddeen Ameenatu tayi min nisan da har abada ba zan same taba".

        Duk wannan maganar da suke yi, suna baƙin kofar ɗakin basu shiga ciki ba.

       "Nuraddeen shigo daga ciki kayimin bayani dan wallahi na kasa gane me kake nufi".

      Kasa tafiya yayi,sai Shamsuddeen ne ya riƙo shi ya zaunar da shi a gefen gadonsa,ya tashi ya ɗauko masa ruwa mai sanyi a fridge,ya bashi amma ya kasa sha, sai Shamsuddeen ne ya bashi a baki ya sha.

AMEENATU.            Complete{04/2020.}Where stories live. Discover now