Meyasa kaman haka?

59 1 2
                                    

🅿 3⃣-4⃣

Written by
M. HANNA

Story by
M. HANNA

Edited by
M. HANNA

Shigarsu gidan ba wuya, wata babbar mace dake zaune akan kujera wacce bazata wuce 39years ba fara ce sosai, tace ya kukayi ne dasu "MALIKA "matashiyar tayi murmushi kana ta zauna kusa da kanwarta "HANNA "tace uhmmm ayyi kinsan halin yan nepa yanda suke yace zai kawo mata sauran bills dinta, grandma dinsu ta zauna tana fadin wallahi haka sukeman lamarin nigeria yana damuna sosai wallahi, wacce tayiwa malika magana ba mamaki yar'ce gun granny tace uhmmm ayyi lamarin ne na nigeria sai hakuri, haka sukaci gaba da firansu dukansu

******MALIKA tana zaune tana charting awaya, taji grandma tace gashi baku gayaman zaku zo ba komai ban dafa ba, me zakuce ne? matar tace malika ta dafa taliya kaman zatafi sauki, sosai hakan ya bakantawa malika rai, cen kasan azuciyarta kuwa cewa tayi wannan yana daya daga cikin dalilin da yasa nakesan nayi aure banida shakat da walwala, nafa dafa abinci agida amma ba wanda yaci ayyi da sun sani sai muzo dashi nan mana, grandma ta katse mata tunanin ta da malika me zaa siyo? kaman batasan zancen da ake ba tace mezaa dafa kuma yanzu? grandma tace taliya ko zaki fira ne, kai tayi saurin girgizawa tace no ba inda zanje kawai tambaya nayi, ahaka dai ta saki ran nata, ta fada kitchen

******grandma ta daka mata kayan miyan ta kawo mata duk abunda zata bukata, malika ta hada komai, grandma tace amma gaskiya wannan ba rayuwa bace ayyi kamata yayi ace dake da HANNA zakuyi wannan aikin amma kinganta cen kwance sai waya take abunta, malika dai batace komai ba saboda inda sabo ta saba da hali irin wannan na HANNA, zama malika tayi tana jiran tafasan ruwan sanwar, grandma tace kiyi hakuri ayyi very soon zakiyi aure kije ki huta, malika tayi murmushi tace Allah yasa

*******haka malika ta karasa komai ta zubawa kowa ta kawo masa harda HANNA, amma cike da takaici HANNA tace banaci na koshi, malika tace okay, nan ta juya zuwa kitchen din, kana ta dawo ta zauna, mummy tace malika zo ki siyoman lacasera ba tare da gardama ba kuwa ta karbi kudin taje ta siyo ta dawo

*******suna cikin cin abincin malika ta kira childhood friend dinta dake aure a anguwar ta kawo mata samosa da donut  nan suka taba fira sukayi wasa da dariya kana tayi tafiyanta dama fita zatayi koda malika ta kirata, bayan tafiyarta malika ta soya samosa suka zauna sukaci abunsu

**********bayan sun  karasa komai da suke, ana zaune ana fira grandma ta mike ta shiga dakinta, bayan yan mintuna ta fito hannunta dauke da atamfa da kuma lace, bayan ta zauna tace maman malika kinga kayanda kanwar ki taman shekaran nan, atamfar nan babba ce 40k take, bakin mummy keda wuyar budewa tace menene 40k wannan atamfar? ina ita ina sayamaki atamfar 40k wacce ke neman abunda zasuci, ke malika nuna mata kasan atamfarki, duk fah irin atamfin nan ne irin na jikin malika 5k, grandma tace aaah wallahi wannan babba ce sosai, mummy kuwa sai fada take yiwa grandma kaman da ita da warinta, hakan ba karamin batawa malika rai yayi ba dan ko bakomai ayyi zaman uwa ce gun mummy bai dace ta mata haka ba

********cikin sanyin jiki grandma tayi murmushi tace bara na kirata, na tambeta kiji, mummy tace aaaah dan Allah kada kijaman bakin suna, nidai dauki kayan ki kawai, grandma tace aaah ayyi ba cewa zanyi ke kikace ba, mummy tace aaaah dan Allah banasan haka kada ki fara haka grandma ta dauki kayan ta ta fice yabar mummy da small talks(kananun maganganu)

***********malika ta nufi kitchen dan wanke hannunta, ta samu grandma tana fitowa daga dakinta, grandma tace kinji abunda mummy ki tace koh? malika tayi murmushi tace uhmmm, grandma tace ayyi koda 5 naira take yakamata ta yaba, dan  ita komai bataman shekaran  nan ba, kinga kudin  wutar nan dana bayar bani ya dace na biyasu ba mummynku amma kinga ta nuna halin ko in kula, dan Allah kigayawa mahaifinki ya aikoman koda da 10k ne, malika tace okay, bayan tafiyar grandma malika ta girgiza kai tace kai wannan wacce irin rayuwa ce cikin azumin nan fah daddy ta kawo mata fridge da kayan sallah, amma kuma common kudin nepa dinda ta biya so take ya biya indirectly kai jama'a wannan wacce iri rayuwa ce ta rashin godiyar Allah, ahaka dai tayi tafiyanta tana fadin wallahi wani zancen na daddy akanku duka gaskiya ne

********suna zaune misalin 6:30 brother din malika da hanna ya shigo, bakinsa dauke da sallama, shine karami cikin su, mummy tace malika tashi ki zubo masa abinci yaci sai mu wuce, ko alama malika bata muna damuwarta akan hakan ba, ta mike ta zubo masa abinci ta kawo masa, yaci ya koshi kana suka mike da sunan tafiya gida, grandma ta masu rakiya har gun motarsu, kana ta zagayo gun malika tace kada kimanta, malika tace okay, amma aranta ta rubuta akan bazata gayawa mahaifin ta ba, ayyi itama tana tausayinsa, haka suka fice har zuwa anguwar su dake sama road

Share
Comment
Likes
Vote

M. HANNA 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 17, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MEYASA KAMAN HAKA? Where stories live. Discover now