RAYUWAR SHAMSIYYARH
By salsabeelarrrh
Page1
Wani madaidai cin gida neh medauke da dakuna hudu kana shiga zaure zaka fara gani sai lungu ta hagu sai dakunan su
Wata kyakyawan mata nagani da yara hudu zaune tsakar gida daga gani kasan hira suke cikin farin ciki saboda murmushine dauke kan fuskan su
Sai naji matan nan da bazata wuce 35years ba tana kiran Shansiyyarh? Shamsiyyarh ??Wai kina ina neh???
Sai ga wata yarinta da baxata wuce 18-19 years ba ta fito daga daya daga cikin dakuna dake tsakar gidan tace Mamah gani Sallah nake yi
Tace Allah ya karba yi maza kije kisa girki ga rana yafara fitowa kuma kafin babanku ya dawo
Tace toh Mamah
Sai naji wannan yariyar da aka kira da Shamsiyyarh tace my Batool pls zo ki daka min Kayan miya
Sai Batool ta taso da gudu tayi hanya kitchen naji matan da aka kira da Mamah tana cewa wai Batool bana hanaki gudu bah Allah dai ya shirya ki
Shamsiyyarh tace wlhi Mamah nima kullum sai na mata fada akan gudu amma bataji
Batool dai sai dariya take kaman an mata albishiri da makkah lol
Suna kitchen suna hada jellof rice with dry fish naji Batool nacewa ya shamcee wai kinsan meyafaru kuwa tace sai kin fada
Batool tace dazu mama ta aike ni naga wannan mayan naki wai na gaida ki na ce toh wlh
ya shamcee haushi yake ban
Ita dai Shamsiyyarh batace mata komai ba saboda tun asali ita ba mai son surutu bane shiru ta mata har suka kusan kamalawa
Salama naji ina daga idona naga wani mutun mai kimani 55years
Batool ta tashi da gudu tayi wurin shi ta fada jikin shi tace babah welcome yace thank u my Batool bana ce ki daina gudu bah tace sorry Babah
Yace Allah ya mumu albarka a daina gudu pls tace toh Babah
YOU ARE READING
RAYUWAR SHAMSIYYARH
RomanceLabarin wata yariyace mai hakuri, kawaici da biyaya.....RAYUWAR SHAMSIYYARH😫💔😭