3

153 9 2
                                    

RAYUWAR SHAMSIYYARH

BY Salsabeelarrrh

Page 3

Follow Salsabeelarrrh❣️😘
Kuyi voting and comment pls dan samun cikaken labarin akai akai
                 And kuma pls ur comments are really needed dan karfafamin  gwiwa🙏🏼
                 Wanna taurarun ⭐️ kawai zaku dangwala dan yin voting🥰
                  THANK YOU 🙏🏼😊😘

Alh Muktar ibrahim dan jihar Niger state neh ita kuma hajiya Hadiza Ahmad yar jihar Kano ce
      Mahaifin Hadiza dan jihar Kano da Niger state neh wato mamanshi yar kano ce mahaifin shi kuma daga Niger state minna ya fito
           Rabuwa neh ya shiga tsakanin mahaifan nata shine uban ya kwaso su ita da kaninta zuwa Minna
       Ana haka kuma Allah ya bashi wata mata ya aura
            Bayan ya dauko su daga Kano sun dawo nan minna
        Ya saka su makaranta suka fara

           Wata rana Hadiza da kanita Aliyu sun taso daga makaranta suna tafiya suna hira
       Shima Muktar ya taso daga wurin aiki a kafa yana tafiya
       Ya hango hadiza ta kanita suna tafiya suna hira ya samata ido har sukazo suka wuce shi
       Tun daga wannan rana Allah ya daura mashi sonta
          Kawai kwasam yaga cutan kansa zai yi idan har bai fito fili da lamarin bah
         Sun taso kenan suna tafiya sun hira as usual ...
         Sai yace Sannu ku yan mata suka  hada baki ita da kanita wurin cewa ina wuni yace lafiya lau ya makaranta sukace Lfy lau
       Yace toh madalla
          Ya dauko naira goma ya bama kaninta yama shi godiya
          Kusan lokacin kudi na da daraja
             Suka kama hanyar gida suna cikin tafiya sai Aliyu yace ya hadiza amma wanna mutumin yana da kirki kin ga fa harda goma ya bamu ita dai murmushi ta mishi saboda ta girmeshi da shekaru kusan 7 ta bashi bama shi ke bimata bah akwai wata Ummi amma Allah ya mata rasuwa Allah ya jikanta da rahma (Ameen)
          Suna isa gida suka tarar da Baffan su
               Suka gaida shi ya musu sannu da dawowa
        Aliyu ya nuna mishi  kudin da wannan mutumin ya basu 
          Kuma suka fada mishi yadda suka yi da shi
            Yace toh madalla an gode aje a huta
         Baffah ya wuce kofar gida saboda sallama ake da shi a kofar gida
           Abokinshi ya gani kofar gidan suka gaisa suka dawo cikin zaure suka zauna
           Su baffah na wurin sunata hira har akayi sallahn la'asar suka tashi sukayi Sallah
         Bayan sun fito daga masalaci neh
            Suka tafi wani gaisuwan rasuwan wani abokin su sun dan jima sai kusan margin suka baro wurin
       Suna isowa kofar gidan baffah aka kira Sallah suka yi alola suka shiga masalaci don yin Sallah
          Suna fitowa abokin baffah Alh sale yace zai wuce yace a'a Alh dole muje muci tuwon dare sai kawuce
       Alh sale yayi dariya yace toh madalla
           Suna shiga daga zaure suka shinfida tabarma Alh sale ya zauna
          Shikuma baffah ya shiga ciki don dauko musu abincin
          Bayan ya dauko abincin Aliyu ya biyo shi da ruwa a kwanun sha
          Aliyu na ajiye ruwan ya sake gaida Alh sale
         Yace Aliyu ya makaranta yace Lfy lau Toh ka gaida Inna ku da hadizatu
         Yace toh
           Su ka zauna cin abincin
                 Bayan sun kamala baffah ya kira Aliyu don kwashe kwanukan
          Baffah ya tashi kenah zai raka Alh sale sukaji ana salama
       Suka hada baki wurin amsawa
                Suna karasa fitowa sai muktar ya tsugunna yace barka da dare
        Sukace Yawwa sannun ka yaro
          Wa kake nema????
         Yana daga tsugune yace dama wurin ka na zo yana magana kanshi na kasa
        Sai Alh sale yace bari ya tafi sukayi salama da baffah
           Baffah yacewa Muktar bisimilla
               Suka shiga daga zauren baffah yace ya zauna
            Suna zama ya sake gaida baffah a mutunce
    Baffah ya amsa cikin karamci
                      Baffah yace meke tafe da kai dan nan
              Muktar kan shi na kasa cikin ladabi ya gayama baffah komai na son auren hadixa
         Baffah yayi jim yace toh yaro ba wai naki taka bah kuma ba wai banaso nabaka auren hadizattu bah a'a
          Kaga yaro makaranta hadizatu takeyi amma kafin nan ma itace ta turoka wajena? yayi saurin girgiza kansa yace a'a baffah
     aiki da abinda addini ya tanadar nayi neman izini wajen mahaifin yarinya ayi hakuri
       Baffah yace toh madalla Allah ya muku albarka
            Yace zan tuntunbe ta akan maganar ka dawo nan da kwana biyu inshaa Allah kadawo sai muyi magana
        Yace toh baffah nagode Allah ya kara girma
                   Yace Ameen
      Baffah ya tashi ya shiga daga ciki duk yangan su tsakar gida suna hira
            Shima ya zauna  danyi hira da ilyalanshi sai kusan goma da rabi yace ma hadizatu ta tashi taje ta kwanta shi dama Aliyu tuntuni ya dade da yi bacci
                Ta tashi ta shige dakin inna saboda nan take kwana
             Baffah ya tashi ya shige dakin shi inna kuma sai da kuma gyara ko ina sanna ta shiga dakinta ta duba hadiza sanna ta fito ta shige dakin baffah
             Tun daga wanna rana da Muktar ya zo baffah ya fara bincike a kanshi
             Baffah bai yi na'am da yaron bah kwatakwata baya son yaron ko kadan yaron bai kwanta mashi a rai bah
              Bayan kwana biyu kuwa sai ga Muktar yadawo kamar yada Baffah yace mashi haka ya dawo
              Yasamu baffah a zaure bayan Sallah mangariba
            Suka gaisa cikin mutuci
      Baffah yayi gyran murya yace Muktar kayi hakuri da abin da zance ma shidai Muktar murmushin karfin hali yakeyi
          Baffah yasake cewa a gaskiya hadizatu makarnta nake da buri tayi saboda haka kayi hakuri dan Allah
          Muktar yayi shiru baice komai na dan wasu lokuta
           Yace to Baffah nagode Alh ya kara girma yace Ameen
          Kuma Allah ya baka wace tafi hadiza
      Shima yace Ameen
   Bayan kwana biyu da zuwan Muktar sai bai sake bi takan Hadiza ba
           Ya cigaba da zuwa aikin shi amma kullum da soyayan Hadiza ya ke kwana yake tashi
         Ashe ita kuma hadiza tana da wanda take so amma bawanda ya sani daga ita sai Aliyu kanita
             Wanna mutumin da Hadiza take so ba wani bane illa wani dan makwabcinsu Kabeeru
     Soyayah suke da kabeeru sosai
          Kwatsam wata rana hadiza sun tazo daga makarnta ita da Aliyu suna hanya dawowa Muktar ya tare su a hanya
         Yana tambayan su makarnta suna tafe yana magana amma bata kula shi Aliyu kawai ke bashi amsa har suka kusa karasowa gidan su sanna ya masu salama ya juya
       Abu kamar wasa Muktar ya nace ma Hadiza itakuma bata kulashi har kabeeru yafara ganewa ya tambayeta tace ita ba sonshi shi ya nace mata
             Kabeeru yace toh
     Wata rana kabeeru yatashi daga kasuwa kawai sai ya karasa makarnta su hadixa suka tako tare suna hira cikin mutuci da soyayah daidai inda Muktar ke tsyawa suka ga Muktar amma suka dauke ido kamar basu taba gani mai kama da shi bah
            Yana gani su karazo ya zo ya sha gaban hadiza yana mata magana bata kulashi ba amma shikuma yaci gaba sai da kabeeru ya mashi magana yace malam laifiya Muktar yama kabeeru kalan wulakaci yace lafiyan ce ya kawo haka yayi tsaki shi kuwa kabeeru yaga abin nashi harda iskanci ciki, yace wa hadiza zo mu wuce kawai ba sai  Muktar ya fara zagin kabeeru ba amma bai kulashi ba suka wuce
                    Tun daga wanna rana Muktar ya dau alwashin sai ya aure Hadiza koh ta halin ka'ka kuma ya dau Karan tsana ya dorawa kabeeru
      Haka kuwa akayi abu kamar wasa sai gashi hadiza tafara kulu Muktar soyayah suke ba kama hannu yaro
           Kabeeru yakasa gane kanta haryazo gane saboda Muktar take wulakatashi shi dai yana sonta tsakani da Allah haka yake ta binta amma bata kulashi kuma shima bai daina bah
            Abu kamar wasa har hadiza tazo ta fadawa inna itafa tasamu wanda take so kuma bakowa bane illa Muktar
        Inna tace toh bari Baffahn ku yadawo saina fada mashi
           Bayan Sallah mangariba sai gashi an aiko yaro wai ana sallama da hadiza
         Inna tace kaje  kace waye, hadiza tayi saurin cewa inna ai Muktar neh dama yace min zaizo anjima
        Hadiza tashiga daki ta dauko hijib ta fita tana murmushi
        Tana isa zaure ta ganshi tsaye takoma cikin gida ta dauko masu tabarma dan zama
      Suna cikin hira saiga Baffah ya shigo ya zare ido dan gani hadiza da yaron da kwatakwata baya kwana
      Suka gaida sa ya amsa yace ke hadizatu me kike a nan tace Baffah Muktar neh yazo wurina shi kuma Muktar munafuki kansa a kasa
        Baffah yace tashi kishiga ciki tatasshi ta shige tana waiwayan Muktar
        Tana shiga ciki Baffah yace daga min tabarma na tunda bana naka bane
        Yace yi hakuri Baffah wlhi sonata nake tsakani da Allah
       Baffah yace wlhi idan baka rufemin baki bah sai na mare ka dama Baffah baya daukan nonsenses yasin
           Baffah ya kuma cewa fitamin daga gida wawa mara tarbiya
         Baffah na shiga ciki ya hau inna da fada akan me tabar hadizatu ta fita ita dai inna sai hakuri take bashi
        Ya kwalawa Hadiza kira ya hau ta da fada tana kuka tace mashi ita Muktar take so
        Har sai da taja Baffah ya mare ta abunda Baffah bai taba yi kenah wato dukan yaranshi  yana sonsu kaman ranshi
          Daga karamin abu ya koma babba hadiza ta nace sai muktar
        Baffah kuma ya tsaya tsayen daka baxata aure shi bah
         Haka Hadiza wata rana an tura ta makarnta ita kadai saboda rana Aliyu bai ci dadi bah baje makaranta bah ta wuce gidan kakani ta domin kai karan Baffah ya
                Tana zuwa ta shige dakin kakanta wato wanda ya haifi Baffah ta
         Tafashe da kuka tana fadamashi duk abin da ya faru ran kakanta ya bace sosai yace ta share hawayenta ta shiga daga ciki
           Tana shiga ciki dakin kakanta tana kuka ta tambayeta meyafaru yanda ta fadawa kakanta haka ta fada mata
        Ita ma randa yabaci sosai saboda ai aure sunna neh don me zai hanaki wai sai kini karatu
           Kakanta ya aika aka mishi kiran Baffah ta
           Baffah na zuwa babanshi ya haushi da fada ta inda yake shiga bata ta nan yake fita  bah Baffah sai hakuri yake bashi kuma kakanta yace dole ayi mata aure
          Baffah yace toh yanda yace  haka za'ayi inshaa Allah
            Ya aika aka kira hadizatu su wuce gida ta shigowa dakin kakanta yace yace ta kwantar da hankali ta aure kamar anyi angama tace toh
        Suna fita suka kama hanyar gida har suka isa gida Baffah baice mata gobe bah
        Tundaga wanna rana Baffah bai kara shiga harkanta bah kuma ya hanata xuwa makarnta ita kuma bata damu ba suka cigaba da soyayan su ita da Muktar
         Haka rayuwa yace gaba da tafiya har aka saka rana aure amma Baffah yayi ransuwa ba zai mata Kayan daki bah kuma haka akayi bai koh mata Kayan daki bah
          Yan uwa suka mata ita dai koh ajikinta
     Haka a ka daura auren su ita da Muktar aka kai ta dakin shi
        Wanda yakama haya a wani gida dakin guda daya haka a kawota kowa ya wuce
        Haka rayuwa yaci gaba da tafiya tun Muktar dai da komai take zaune da shi har yaxo yasiya wani karamin mashin ledis suke rayuwan su cikin fari ciki da son junna
         Bayan auren su da shekara daya Allah ya bata ciki ta haifi diyarta mace kyakyawa fara tas harta fi babanta haske ga hanci da kyau tubarka mashaa Allah kawai zamuce don fadan Kaywunta sai ya cika mana feji daya
       Rana sunna yariya tace sunna ta Shamsiyyarh
        Haka suka cigaba da raino Shamsiyyarh cikin so da kauna
         Watara kwansam tana zaune shikuma baya nan sai gashi ya dawo ya zo mata da magana zai kara aure
        Tace toh Allah ya sa alkhaire haka kuwa akayi ya kara auren shi
       Ya auro matan shi mai suna Hauwa kulu
   Hauwa kulu tana da kirki sosai saboda ita da aikinta ya aurota batada mtsala ita nurse ce baruwanta
       A cikin gida daya suke karku manta nace maku gidan haya neh kuma daki daya ya kama wata tashi a gidan ya kuma kama dakin kafin ya auro hauwa kulu
       Hadiza da hauwa kulu suna zan Lfy abin su gwani ban sha'awa amma a gaskiya Hauwa kulu tafi Hadiza hakuri nisa ba kusa
       Hadiza bata da hakuri koh kadan ana haka Allah ya bama hauwa kulu ciki har Allah ya sauke ta lfy ta samu danta namiji kyakyawa gaske kuwa
         Rana sunna yaci sunna shi Shamsudeen
    Haka rayuwan su ya cigaba  da tafiya Hadiza ta kuma samun ciki ta haifi dan ta namiji Mai sunna Ahmad yaro dan gata mai lakani biyu Mujaheed da Babangida yana da shekara 24 Allah ya karbi abinsa Allah yasa samari gidan aljana neh (ALLAH YA JIKAN KA DA RAHMA YA KAI HASKE KABARKI AMEEN YA RABBI🙏🏼) dan Allah duk wanda ya karta novel dina yama wanna bawan adu'a ya jikan shi kuma ya kai haske kabarin shi💔😭🙏🏼 Nagode
           Hadiza ta kuma samun ciki ta haifi yarta mace mai suna Batool itace my Batool da kukaji anakira mai gudu lol😂
           Sai kuma Allah ya kuma bawa Hauwa kulu ciki ta haife da namiji wanda yaro yaci suna shi Ibrahim ana kiranshi da Modibo saboda sunna kakanshi yaci wanda ya haifi babansa,,
           Hadiza ta sake haihuwan yarta mace mai sunna Maryam tana da shekara daya Allah ya karbi abinsa (Allah ya jikanki Allah yasa yan matan gidan aljana neh🙏🏼💔😭)
            Hauwa kula takuma haihuwan danta mesuna Huzaifa bin yaman sai kuma Hadiza takuma haihuwan danta mesuna Ubaiyyu bin akab
           Hadiza ta kuma yin auta wato Khalifa iyayan rashin Allah dai ya shirya shi ya ku raaya shi Ameen ya rabbi
              Ataikace dai Hadiza nada yara 6 amma 4 neh kawai Allah ya raya mata su
           Hauwa kulu kuma ita tana da uku3 duku maza
           Haka suka cigaba da zaman lfy haka ma yaransu suka tazo kai a hade
         Sai dai kunsa dole ba'a rasa abin bacin rai ba shaidan na ko ina Allah ya kare mu daga shari shi Ameen
          Allah yafara budawa Muktar daga wanna gidan hayan har yazo ya kama gida su kadai kawai cikin gidan
        Shine gidan da muka fara dashi idan baku manta ba Mai dakuna 4
             Suna cikin zamansu cikin farin ciki har Allah yayi yasamu chanjin wurin kai har ya kai su makkah,, Hadiza da Hauwa da shi kanshi suka sauke farali
           Wata rana suna sune kwasam yazo masu da magana kara aure💔
            Koh kunsan waya auro????
            Koh kusan itace sila tarwasa  faricikin gidan su
           Koh kusan ita tasaka rayuwan kowa cikin kunci
           Koh kunsan ita tajefa RAYUWAR SHAMSIYYARH cikin bala'i da masifah yariya mai hakuri, juriya, Kawaici da biyaya

      Very emotional story💔😭

                                  Ku biyo ni dan jin karshe labarin RAYUWAR SHAMSIYYARH (TRUE LIFE STORY)
                          Don't forget to VOTE ⭐️and COMMENT ❣️

                   Wattpad Salsabeelarrrh💋❤️

Karku manta nace maku TRUE LIFE STORY💔😭 yanxu muka fara

                              Dan Allah kuyi hakuri kusan this is my first novel kuma nasan dole zaku samu kurakure sosai wurin spellings

Nagode Allah yasa mudace🙏🏼🙏🏼

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 02, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RAYUWAR SHAMSIYYARH Where stories live. Discover now