MATAR LAMEER

1.7K 51 0
                                    

_____________________________

*MATAR LAMEER*
_30% TRUE LIFE FICTIONAL STORY 30%_ _AND COMEDIANS STORY 40%_

*_LATEST HAUSA NOVEL FOR 2020_*
_____________________________
*Fauziyya Tasi'u Umar*
_____________________________
Pay before read 300 single section VIP 500  recharge card MTN ta  WhatssApp  a wannan number 09013718241 ko wannan 09031307566, ko ta account number:  0255526235: Fauziyya Tasi'u Umar
GTBank.

_____________________________
*14*
_____________________________

_________📝Tabe baki tayi ta dauki qwaryarta tace “nikam Baffana da yan gdanmu ba yar iska bane basuda bindira ni kadama ka qara cewa kasanni banasonka kuma......"
Rufe mata baki yayi yace “ni kuma inasonki zan aureki idanma bakiso bazanyi miki ba kawai kallonki zantayi kiyita sani nishadi ko?" Daqa masa kai tayi tace “amma ka yarda zaka nunamin din ko?" Murmushi yayi yace “har wasa zakiyi da ita ma"

Dariya tayi ta fara juye masa nonon saida ta gama dure masa a jarka sannan ta qulle masa furar a leda tasa masa a but sannan ta dawo ta tsaya kusa dashi tace.
“Kayyy wannan mutum oye kwai shirgege kalla fah a saitin qugunka nike" matsawa yayi yace “aa kalla sosai a saitin qirjina dai ko? Murmushi tayi tace “yawwa Ina abuna da kace zaka siyamin?"

Jan hanunta yayi ya zagaya ya sanyata a mota shima ya shiga ya zauna yace “na siyo miki amma ban gaji da ganinki ba so nake nayi miki wata tambaya inaso cikin satinnan zan turo iyayena su nemamin auranki, a yau nakeso idan na koma gda na sanar da mahaifina inason qara aure amma idan munyi aure Lagos zaa kaimin ke fah"
Wata uwar harara ta galla masa tace “tabdi kaje ka saidani kwarankwatsa dubu bazanje ko inaba"

Kallonta yakeyi da mamaki shikam tunda yake bai taba ganin sakaryar yarinya irin Jiddoh ba bude mata qofa yayi yace “naji jeki" wata leda ya dauko ya miqo mata yace.
“Ga alqawarin da nayi miki jiya ki kula da kanki zanje Lagos May be zanyi sati daya kafin na dawo kome ke akwai zanji gurin Alhajinmu.


Hannu ya sa a aljihunsa ya zaro yan dari biyar bayar da baisan adadinsu ba ya kama hannunta yasa mata tare da kissing dinta yace “ki bawa Gwaggo Koda yake muje kawai inganta da kaina banson tallan nan naki"
A fari taso qin yarda suje wuronsu dashi amma yanda yayi kicin² yasata dole ta yarda sujedin bisa sharadin saidai su tafi a qafa haka kuwa akayi suna tafe yana janta da hira yana dauke da qorain nonon nata har suka iso bayan gdan cikin saa kuwa sukaci karo da Gwaggo ta debo ruwa a rafi ta tsaya tana kallonsu cike da tsoro hadi da kunya irin tasu ta fulani ta saki bokitin ta juya da sauri.

Binta yayi shima yana fadin “Gwaggo ki tsaya bafa wani abu bane don Allah ki tsaya ki saurareni"a wata kwana suka hadu da Inna Jumme ta tsaya itama ta tsaya tasan halin abokiyar zaman nata duk da Jiddoh ba ita kadai bace amma itace mace ta fari to a al'adarsu ta fulani bazata taba tsayawa tayi mgn da duk wanda yace yanason Jiddoh ba balle Lameer da dama ba qaunarsa sukeyi ba.


Inna Jumme ce ta tareshi tace “oye miye yake hwaruwa kaiko bazaka samawa kanka lfy ka fita harkar diyarnan ba tunda sunce bazasu baka ba"
Shafa sumarsa yayi ya durqushe yace “Wlh nima nayi qoqarin hakan amma na kasa Inna nabawa Hauwah kudi ta kula da kanta sannan na bata ta kawo muku a daina dora mata tallan nono saboda bata gari Inna Hauwah tanada garin jiki kuma halittarta tana daukan hankalin maza komai zai iya faruwa ta fadamin komai da dalilin da yasa batason aurenta da Mahadi don Allah kada kuyi Mata dole kada kuja da ikon Allah wlh zan aureta kuma zan riqe muku ita amana fiye da abinda kuke tsammani"

Kallonshi Inna Jumme takeyi cikin tausayawa tanaji a ranta dama Ladingon ta ce ta samu wannan dan gayun da kota tsiya² sai anyi auren tace.
“amma ta yaya zaayi kace ta daina tallan nono bayan dashi muka saba?"
Qasa ya sakeyi da kansa yace “eh nasani amma nasan kunayi ne domin ku samu kudin cefane to ga dubu hamsin nan ku rinqa cefane har na dawo sannan a fadawa Baffa yayi hqr yau talata to rana i ta yau magabatana zasuzo don Allah ya taimakeni ya amsheni a matsayin zabin ubangiji"………………….


*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*

MATAR LAMEERWhere stories live. Discover now