Rayuwata ceh

14 1 0
                                    

[3/18, 9:42 PM] Lashminzy: 🤷🏾‍♀🤷🏾‍♀ *RAYUWATA CE*!🤷🏾‍♀🤷🏾‍♀
               ( _It is my life_)
   
       _A fictional love story_

                    *Story*
                     *And*
                 *Written by*
                *Lashminzy*

          *MARUBUCIYAR..........*

*Rayuwar ummiey*
*Rud'ani*
*Muneerah Muneer*
*Hukunci*  AND NOW
*RAYUWATA CE*

              *PAGE 66~70*

   "A rude na dago kaina na dubeshi cikin wani yanayi mai wuyar fassara, gabadaya ya fita hayyacinsa zufa ce ke karyo mashi ga fuskarshi dake zubar hawaye...

   Cikin muryar kuka nace Yaya sadiq kayi hakuri a halin yanzu banida amsar da zan baka saidai wani lokaci! Ina fadar haka na tashi da sauri na fice a part dinshi.

Bayan gidan mu naje ina mai zubda hawayen tausayin kaina ni kwakwata bana kaunar ya sadeeq banajin zan iya rayuwar aure dashi!

   Kamar wacce ta tuna da wani abu haka na tashi da sauri na shiga cikin gida cikin sa'a kuwa banyi karo da kowa ba harna shiga dakina.

  "Wani irin numfashi yake fitarwa dakyar yake fadin mommy Dan Allah kizo yanzu mutuwa zanyi!

  Mommy dake daki tana hada kayan da zata aika gidansu ramlat a firgice ta tashi da sauri ko dankwalinta daya fadi bata tsaya dauka ba ta fito da sauri ta nupi part dinshi.

A bakin madubin dakinshi ta ganshi rike da kwalban turare harya fasa yana neman burmawa a cikinshi,, Da sauri ta dakatar dashi ta hanyar daka mashi tsawa sannan ta kwace kwalbar a hannunshi ta aje kan mirror.

   "Cikin matukar tausayin shi tace haba son meyasa zaka dauki wannan mummunar matakin? Ka kuwa san laifin da kake shirin aikatawa? Haba sadeeq ban sanka da haka ba Dan Allah kayi hakuri komai da kake gani sai anyi hakuri ake samu.

   "Tun ba yau ba nasha fadamaka ka rage sa Abu a ranka gashi yanzu kana neman illata kanka,,, Daman nasan za'a rina shiyasa tun farko nake fadamaka ka daina matsawa yarinyar nan ka bita a hankali amma ina sam bakajina sai yanzu da aski yazo gaban goshi kake komai ido rufe.

    Cije labbanshi na kasa yayi yanajin zafi a zuciyar shi yama kasa magana mummy CE kawai ke surutunta dan kwatakwata ba dauka yake ba.

Sai dayaji tace ka kwantar da hankalinka insha Allah Sareenah zata zama taka da yaddar Allah....

  Sannan da sauri ya kalleta harda sakin murmushi yace da gaske mummy?

Cikin karfafa masa gwiwa tace insha Allah amma da sharadi?

 
    Jikinshi har rawa yake yace babu komai koma mene zanyi....

  "Banason ka dinga takura mata sannan banason tasan nasan kana sonta saboda zata iya tauye kanta ko bata sonka saboda ta faranta mun rai ta amince kaga mun tauye ta kenan.

  "Kabi komai a hankali sannan a cigaba da addu'a insha Allah za'a dace!

  "Yauwa mummy nagode da kulawarki gaskiya nayi dacen mahaifiya ta gari! Murmushi mummy tayi gami da sakar mashi rankwashi a kai kafin tabar dakin, shi kuwa yar kara ya saki kamar wanda cinnaka ya ciza...

    "Cike da kwarin gwiwa ya tashi ya shiga toilet ya dade yana watsa ruwa sannan ya fito kananan kaya ya sanya wanda suka amshi jikinshi amma daka kare mashi kallo zakasan yana cikin wani yanayi.

   Bayan ya gama shiryawa ne ya dauki makullin motar shi da wayoyin shi ya fita.

  "Nikam ina daki har nayi wanka zazzabi naji yana neman rufeni nasha paracetamol ba laifi na danji sauki sedai zuciyata cike take da damuwa, ina cikin hakane ramlat ta shigo sedai fuskarta ba walwala kamar yadda na saba gani.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 16, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RAYUWATA CEHWhere stories live. Discover now